Ibrahim Masari Solidarity Organisation IMSO

Ibrahim Masari Solidarity Organisation IMSO Advancing the Renewed Hope Agenda through the office of H.E. Ibrahim Masari, S.A Political Matters

P-BAT Presidential Campaign Schedule 2026-2027.
15/10/2026

P-BAT Presidential Campaign Schedule 2026-2027.

Speech by His Excellency, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Special Adviser to the President on Political and Other Matters, ...
14/10/2026

Speech by His Excellency, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Special Adviser to the President on Political and Other Matters, at Today’s Inauguration of the Presidential Campaign Council (PCC) at the Presidential Villa, Abuja.

IBRAHIM MASARI YAKAI ZIYARAR TA’AZIYYA GA SARKIN MASKAN KATSINA HAKIMIN FUNTUA​Mai Girma Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Ma...
07/10/2026

IBRAHIM MASARI YAKAI ZIYARAR TA’AZIYYA GA SARKIN MASKAN KATSINA HAKIMIN FUNTUA

​Mai Girma Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mai baiwa Shugaban Kasa shawara kan harkokin siyasa da sauran al'amura, ya kai ziyarar ta'aziyya ga Sarkin Maska kuma Hakimin Funtua, Alhaji Sambo Idris Sambo, biyo bayan rasuwar kanensa, Alhaji Yusuf Idris Sambo.

​Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya kai ziyarar ne tare da Karamin Ministan Gidaje da Bunkasa Birane, Dr. Muttaka Rabe Darma; Darakta Janar na NEPAD, Jabiru Salisu Stauri; Hon. Amiru Tukur Bakori; da sauran muhimman mutane.
​A yayin ziyarar, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya mika sakon ta'aziyyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga iyalan da rasuwar ta shafa, tare da nuna alhininsa.
​Sheikh Ibrahim Lawal Usama, Sheikh Abu Ammar, da Mallam Mai Wada Daudawa sun gudanar da addu'o'i ga mamacin, inda s**a roki Allah Madaukakin Sarki ya yafe masa kuskurensa, ya kyautata makwancibsa, Allah ya baiwa iyalansa hakurin jure wannan rasi.

Shima a nasa jawabi, ​Sarkin Maskan Katsina Hakimin na Funtua ya mika godiyarsa ga Alhaji Ibrahim Kabir Masari, tawagarsa, da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa sakon ta'aziyya, addu'o'i, da kuma nuna halin karamci ga iyalan. Daga karshe yayi fatan Alkhairi da addu’ar zaman lafiya ga jihar katsina, dama kasa baki daya.

​Ofishin Yada Labarai
Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)

Ibrahim Masari Ya Karbi Bakuncin Hadaddiyar Kungiyar Agajin Musulmi Ta Abuja FCT, Yayin Da Kungiyar Ta nuna Goyon Bayan ...
06/10/2026

Ibrahim Masari Ya Karbi Bakuncin Hadaddiyar Kungiyar Agajin Musulmi Ta Abuja FCT, Yayin Da Kungiyar Ta nuna Goyon Bayan Tazarcen Tunubu A 2027

​Mai Girma Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mai baiwa Shugaban Kasa shawara kan harkokin siyasa da sauran al'amura, ya karbi bakuncin jagororin Hadaddiyar Kungiyar Agajin Musulmi ta Tarayya (Joint Islamic First Aid Organization, FCT), karkashin jagorancin Shugaban kungiyar, Alhaji Ahmad Adamu Jingi, a ofishinsa da ke Abuja.

​Ziyarar ta maida hankali ne kan ayyukan agaji da tallafawa al'umma, ci gaban kasa, fafutukar wayar da kan jama'a a matakin karkara, da kuma gudanar da tsare-tsaren Manufar (Renewed Hope Agenda) na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
​Yayin da yake jawabi a wurin taron, Alhaji Ahmad Jingi Adamu, a madadin kungiyar, ya bayyana cikakken goyon bayansu ga sake zabar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekara ta 2027. Ya kuma nuna kwarin gwiwa kan turba da manufofin gwamnatin wajen ciyar da tattalin arziki da zamantakewar kasa gaba daya.
​Haka zalika, kungiyar ta bayyana ra'ayinta na son dorewa da ci gaba da tsarin takarar Shugaban Kasa na Musulmi da Musulmi (Muslim-Muslim ticket) a zabe mai zuwa na 2027.

​A sa'ilin da yake maida jawabi, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya kwadaitar da tawagar kan su jajirce wajen riko da wannan tafiya, inda ya roke su da su yi fafutukar kare tsarin Musulmi da Musulmin "saboda Allah," tare da kara jaddada cewa "Allah Madaukakin Sarki ne kadai zai bayar da sakamakon wannan kokari."

​Shi ma a nasa jawabin a gun taron, Sheikh Ibrahim Lawal Usama, wanda yana daya daga cikin mambobin tawagar, ya yi kira ga mambobin kungiyar da su kasance masu karsashi da jajircewa kan tsarin na Musulmi da Musulmi, sannan su tafiyar da wannan lamari da kyakkyawar niyya da gaskiya.
​Bugu da kari, ya yi kira ga mambobin da su kiyaye hadin kai, mu'amala ta zaman lafiya, da kuma sa hannu cikin tsarin dimokradiyya cikin tsantseni da rikon amana yayin da ake fuskantar zaben shekara ta 2027.

​Mai baiwa Shugaban Kasa shawaran ya yabawa kungiyar bisa ayyukanta na agaji da sauran tsare-tsare masu amfani ga al'umma, inda ya bayyana muhimmiyar gudunmawar da kungiyoyin karkara ke bayarwa wajen dankon zumuncin kasa, bunkasa dimokradiyya, da kyautata rayuwar mazauna gari.
​Tawagar ta mika godiyarta ga Mai Girma Ibrahim Masari bisa karramawa da samun kyakkyawan tarbiya da ya yi musu, inda s**a dauki alkawarin bayar da gudunmawa ta kwarai wajen wayar da kan mutanen karkara da gudanar da harkokin dimokradiyya cikin sahihiyar hanya gabanin zaben 2027.

​Ofishin Yada Labarai:
Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)

ALH IBRAHIM MASARI ARRIVED IN KANO KNOWHis Excellency Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Special Adviser to the President on P...
03/10/2026

ALH IBRAHIM MASARI ARRIVED IN KANO KNOW

His Excellency Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Special Adviser to the President on Political and Other Matters, has arrived in Kano State to represent His Excellency President Bola Ahmed Tinubu, GCFR, at the 76th Maukibul Qadiriyyah.

HAPPY INDEPENDENCE DAY! NIGERIA’S  ANNIVERSARY!!​October 1, 2026​On behalf of the leadership, executives, and entire mem...
01/10/2026

HAPPY INDEPENDENCE DAY! NIGERIA’S ANNIVERSARY!!
​October 1, 2026

​On behalf of the leadership, executives, and entire membership of the Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO), we extend our warmest felicitations and heartfelt goodwill to Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Special Adviser to the President on Political and Other Matters, as Nigeria celebrates its 66th Independence Anniversary.

​Today, as our great nation marks another significant milestone in its journey of sovereignty, unity, and democratic growth, we honor your unwavering dedication to the service of the Federal Republic of Nigeria. Your strategic leadership, political sagacity, and commitment to supporting the vision of the President have continued to foster harmony, political stability, and national progress.

​As an organization dedicated to upholding your values and driving grassroots solidarity, IMSO remains deeply inspired by your open-door policy, dedication to community empowerment, and tireless efforts toward political inclusivity across Katsina State and the nation at large.

​On this historic 1st of October, we celebrate not only the resilience and spirit of the Nigerian people but also visionary leaders like you who work diligently behind the scenes to build a stronger, more united, and prosperous nation.
​May Almighty Allah (SWT) continue to grant you wisdom, sound health, divine guidance, and protection as you discharge your vital responsibilities to the President and the nation.

​Happy Independence Day, Nigeria!

​Signed,
Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)

29/09/2026

Da yammacin yau Talata 29th Sept, 2026. Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Taimakama Shugaban Kasa a Fannin Siyasa da Sauran Al'amura, ya tarbi Mai Girma Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Lagos bayan dawowarsa daga dogon hutu.

28/09/2026

By the grace of Almighty Allah, Atiku Abubakar will never occupy the Office of the President of the Federal Republic of Nigeria.
​Alh. Ibrahim Kabir Masari
Special Adviser to the President on Political and Other Matters

Ibrahim Kabir Masari Ya Wakilci Shugaba Tinubu A Taron Siyasa Da Dandalin Malaman Jami’o’i Na Jihar Jigawa yau Asabar 26...
26/09/2026

Ibrahim Kabir Masari Ya Wakilci Shugaba Tinubu A Taron Siyasa Da Dandalin Malaman Jami’o’i Na Jihar Jigawa yau Asabar 26th, Sept.2026.

​

​Mai Girma, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Maitaimakama Shugaban Kasa kan harkokin Siyasa da Sauran Al'amuran yau da kullum ya wakilci Mai Girma Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a wani muhimmin taron siyasa tsakanin Gwamnan Jihar Jigawa, Mai Girma Malam Umar A. Namadi, FCA, da Dandalin Malaman Jami'o'i da Makarantun Gaba da Sekandari na Jihar Jigawa (Jigawa State Academic Forum).

​Taron, wanda aka gudanar a Babban Dakin Taron Baki na Gidan Gwamnati da ke Dutse, ya samu halartar malamai da masu bincike fiye da mutum dubu daya 1,000 daga cibiyoyin ilimi na gaba da sekandari Arba'in da Takwas 48 dake a fadin Jihar Jigawa da sauran jihohin Arewacin Nigeria.

​Yayin da yake wakiltar Shugaban Kasa a wurin taron, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya halarci zaman tattaunawar tare da mika saƙo na musamman daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, zuwa ga Gwamna Umar A. Namadi, FCA, wanda Shugaban Kasa ya bayyana shi a matsayin "Dan Amanar Gwamna."
​Haka zalika, Dandalin Malaman ya bayyana goyon bayansa na sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a zaben shekara ta 2027, da Gwamna Umar A. Namadi, FCA, kan karagar mulkin Jihar Jigawa a shekara ta 2027.

​Taron ya tattauna kan batutuwan da s**a shafi kyakkyawan shugabanci, ilimi, bincike, ci gaban siyasa da sauran muhimman al’amura na cigaban Jihar Jigawa dama Kasa baki daya.

​Sauran wadanda s**a halarci taron sun hada da Dr. Muttaka Rabe Darma, Ministan Gidaje da Bunkasa Birane; Prof. Suwaiba Sa’id Ahmed, Ministar Cikin Gida a Fannin Ilimi (Minister of State for Education); Prof. Shuaibu Shehu Aliyu, Sakataren Gudanarwa na Asusun Bunkasa Fasahar Fetur (PTDF); Hon. Jabiru Salisu tsauri, Mai Tsara Ayyukan NEPAD; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa; da sauran manyan jami’an gwamnati, malamai, da sauran masu ruwa da tsaki.

​Sa hannu:
Ofishin Yada Labarai
Ibrahim Masari Solidarity Organisation (IMSO)

Address

No:2&3 Nanaco Plaza, 001 Gidan Dawa, Commercial Layout
Katsina
820101

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ibrahim Masari Solidarity Organisation IMSO posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share