18/09/2026
Kasuwancinka ba sai ya zama na kowa da kowa ba. Abin da ake buƙata shi ne ya zama na musamman ga ainihin mutanen da suke buƙatarsa. Waɗannan su ne abubuwa 5 da ba za ka taɓa wasa da su ba idan kana gina sana'a. Kuma kada ka kuskura ka tsallake na ƙarshen, domin shi ne babban dalilin da yake binne kasuwanci da ransa.
1. Sanin Ainihin Kwastoman Da Kake Nema: Ka Daina ƙoƙarin burge kowa da kowa. Ka Gano ainihin mutanen da ka buɗe kasuwancin dominsu, sannan ka fahimci abin da suke buƙata a zahiri. Baka sayar da komai ga kowa.
2. Ka Zama Gwani A Abu Ɗaya: ka Bawa mutane gamsasshen dalilin da zai sa su riƙa tunawa da kai. Idan wata buƙata ta taso musu, ka tabbatar sunanka ko shagonka ne zai fara zuwa ransu kafin na kowa.
3. Ka Daina Kwaikwayon Kowa: Ba dole sai ka bi hanyar da abokan takararka suke bi ba. Ka Nemo naka tsarin wanda ya dace da kai kuma ya bambanta ka da sauran 'yan kasuwa.
4. ka Kasance Mai Sadaukarwa: Ba za ka iya yin komai a lokaci ɗaya ba. Wani lokacin dole ne ka haƙura da sayar da wasu kayan ko shiga wasu kasuwannin, domin ka fi ƙarfi a asalin ɓangaren da ka zaɓa ka kware a ciki.
5. Ka Gina Kasuwanci Mai Dogon Zango:
Ka Daina yin tsalle-tsalle kana bin duk wani sabon yayi ko canza sana'a don kawai kaga wani yana samun kuɗi a ciki. Tsaya ka gina naka tsarin, kuma ka bawa mutane lokaci su san ka da shi.
Ka riƙe wannan: Kasuwancin da yake ƙoƙarin sayar da komai ga kowa, a ƙarshe zai tashi a tutar babu, Amma kasuwancin da ya tsaya a kan tsarinsa a waje ɗaya, zai zama gagarabadau wanda ba a mantawa da shi.
Allah yasa mudace..................
MYBC ✍️