25/09/2026
KOTUN ƘOLULU YA TABBATAR DA ƘARA’AR INEC, YA MAYAR DA SASHE-SASHEN DOKAR ZAƁE DA AKA SOKE
Kotun Ƙoli a ranar Alhamis ta amince da ƙarar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta shigar kan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, wanda ya soke wasu sassa na Dokar Zaɓe ta 2026 da s**a shafi zaɓen ƴan takarar jam’iyyun siyasa da kuma rajistar mambobin jam’iyyu.
Kwamitin alkalai bakwai na Kotun Ƙoli, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Adamu Jauro, ya amince da ƙarar INEC baki ɗaya, tare da mayar da waɗannan tanade-tanade na dokar.
Kotun Ƙolin ta musamman tabbatar da Sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2) na Dokar Zaɓe ta 2026. Waɗannan sashe-sashe sun shafi rajistar mambobin jam’iyyu da kuma hanyoyin da jam’iyyu za su bi wajen zaɓen ƴan takararsu.
Sashe na 77(5), 77(6) da 77(7) sun tanadi yadda jam’iyyu za su gabatar da rajistar mambobinsu ga INEC da kuma yadda za a yi amfani da ita. Bisa waɗannan tanade-tanade, mambobin da sunayensu ke cikin rajistar da aka gabatar wa INEC cikin lokacin da doka ta kayyade ne kawai za su iya shiga zaɓen fidda ƴan takara, tarukan jam’iyya da manyan tarukan jam’iyya.
Sashe na 84(2) kuwa ya tanadi cewa jam’iyyun siyasa za su zaɓi ƴan takararsu na mukaman zaɓe ta hanyar zaɓen fidda gwani kai tsaye (direct primaries) ko kuma yarjejeniya (consensus).
Shari’ar ta samo asali ne daga ƙarar da Zenith Labour Party (ZLP) ta shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. Jam’iyyar ta ƙalubalanci sahihancin waɗannan tanade-tanade, tana mai cewa sun tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa tare da cin karo da wasu tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.
A ranar 5 ga Mayu, 2026, Babbar Kotun Tarayya ta yi watsi da ƙarar. Daga nan ZLP ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja.
A ranar 16 ga Yuli, 2026, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta amince da wani ɓangare na ƙarar, sannan ta soke Sashe na 77(5), 77(6), 77(7) da 84(2) na Dokar Zaɓe.
INEC, ba ta gamsu da wannan hukunci ba, ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli, tana neman kotun ta mayar da waɗannan tanade-tanade na dokar.
Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin biyu a ranar 16 ga Satumba, Kotun Ƙoli ta ajiye hukuncinta domin yanke shi daga baya.
A hukuncin da ta yanke a ranar Alhamis, Kotun Ƙoli ta bayyana cewa waɗannan tanade-tanade da ake ƙalubalanta ba sa cin karo da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, sannan ta mayar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke tun farko.
Haka kuma, Kotun Ƙoli ta umurci Zenith Labour Party ta biya kuɗin diyya/kudin shari’a na ₦2 miliyan.
Wannan hukunci ya kawo ƙarshen takaddamar shari’a kan waɗannan sassa na Dokar Zaɓe, musamman yayin da Najeriya ke shirin tunkarar babban zaɓen 2027.