13/10/2026
SAMAR DA RUWAN SHA: SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR SOBA NA CI GABA DA KAI AYYUKAN MORE RAYUWA GA AL’UMMA
Duk dai a cikin kudirin Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Soba Hon. Muhammad Shehu Molash, na ganin an samar da muhimman abubuwan more rayuwa ga al’ummar karamar hukumar, gwamnatinsa ta samar da burtsatsun ruwa masu amfani da hasken rana (Solar Boreholes) a wasu garuruwa da wuraren da ake da bukatar ruwan sha.
Daga cikin wuraren da s**a amfana akwai:
1. Kurmin Alhaji Saleh
2. Masallacin Izala na Jumu’a, Unguwar Rimi Soba
3. Rigar Tashi
4. Kwalliya
5. Masallacin Jumu’a na Rahama
6. Bakin Kotun Soba
Wannan na daga cikin kokarin gwamnatin karamar hukumar na saukaka wa al’umma wahalar samun tsaftataccen ruwan sha tare da inganta walwala da rayuwar jama’a.
Baya ga samar da wadannan sabbin burtsatsun ruwa masu amfani da hasken rana, Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Soba ya kuma dauki nauyin gyara da farfado da tsofaffin burtsatsun ruwa sama da guda dari (100) da s**a samu matsala a sassa daban-daban na karamar hukumar.
Wannan mataki ya nuna kokarin shugaban na ganin cewa ba a bar kadarori da kayan gwamnati su lalace ko su zama marasa amfani ba, domin dukiyar gwamnati dukiyar al’umma ce. Maimakon a yi watsi da tsofaffin burtsatsun, an mayar da hankali wajen gyara su domin su ci gaba da amfani ga jama’a.
A hankali, ayyukan samar da ruwan sha da sauran abubuwan more rayuwa na ci gaba da isa ga al’ummomin Karamar Hukumar Soba, domin tabbatar da cewa ribar gwamnati ta kai ga jama’a a matakin karkara da birane.
October 13, 2026