29/08/2026
SANARWAR FARA DAUKAR SABABBIN DALIBAI MASU KOYON DARUSSAN LAFIYA TA (ONLINE) RUKUNI NA (12)
Hilal Primacare Health Services tana sanar da jama'a cewa ta buɗe shirin daukar sababbin ɗalibai masu sha'awar ƙara ilimi, zurfafa bincike, da samun ƙwarewa ta musamman a fannin ilimin Lafiyar Al'umma. Wannan shiri na musamman an tsara shi ne bisa ingantattun tsare-tsare domin cike gurbin ƙarancin ƙwararrun masu ilimin lafiyar Al'umma da fannin rigakafi da bayar da agajin gaggawa a cikin Al'umma.
Wannan dama ce ta musamman gare ki/ka domin koyon muhimman darussan lafiya cikin sauƙi, ba ta re da barin gida ba.
📚 DARUSSAN DA ZA A KOYA:
1.🌸 Lafiyar Mata da Haihuwa (Maternal and Reproductive Health.
2.🎀 Fadakarwa da Kariyar Ciwon Nono (Breast Cancer Awareness and Prevention)
3.🌺 Fadakarwa da Kariyar Ciwon Dajin Mahaifa (Cervical Cancer Awareness and Prevention)
4.🦠 Cututtuka Masu Yaɗuwa ta hanyar Saduwa (Infectious and Sexual Transmitted Disease)
5.👨👩👧👦 Ilimin Tsarin Iyali (Family Planning Education)
6.🚑 Agajin Gaggawa da Taimakon Farko (Emergency and First Aid Education)
Mace mai ilimi kan lafiya tana da damar kare kanta, kula da iyalinta da kuma taimakawa wajen ceton rayuka, saboda haka kada ki bari wannan damar ta wuce ki.
Early Registration: ₦500
Regular Registration: ₦1,000
Bayan kammalawa zaka samu ƙwarewa da gogewar da za su ƙara wa (Certificate of Completion) din ka tasiri da daraja sosai a fagen aikin wayar da kan Al'umma akan Lafiyar su ko gina sana'a.
Domin cikakken bayani ko tura kuɗin rijista , a tuntuɓe mu ta WhatsApp: (08146236510)
Sanarwa
Hilal Primacare Health Services
Tushen Lafiyar Al'umma