03/05/2026
Wannan itace masifar da Al'ummah suke ciki musamman Matasa Maza da Mata. Wannan Allurar suananta Pentazocine injection, ana yin ta ne ga marasa lafiya wanda jikin su yayi tsanani har ta ga magani kamar irinsu Paracetamol da Diclofenac basa yiwa mara lafiya aiki sai ayi masa Pentazocine injection domin yaji dadi
Sannan ana yin Allurar Pentazocine ga mara lafiya a lokacin da za'a yi masa Surgery domin ta taimakawa Allurar Anesthesia wajen bacci da cire zafin da radadin Surgery
A wasu lokuta kuma ana yiwa Mata masu ciki a lokacin da suke nakuda domin ta taimaka musu wajen rage radadi da zafin Nakuda, a wasu lokaci kuma ana yiwa masu cutar sikila ( Sickle Cell ) a lokacin da suke cikin mawuyacin hali na crisis
Abinda yasa nace yanzu wanan Allurar ta zama masifa shine, Matasa Maza da Mata, Matan Aure da Mazajen Aure sun fara yinta a matsayin shaye-shaye
Kunsan meye take saka su idan sunyi, tana saka su suji dadi suta yin farin ciki, wasu kuma suna yi ne don su manta da matsalolin rayuwa ko damuwa wanda yake fitar dasu daka emotional distress
Wannan hoton dana saka hannun daya daka cikin masu yin Allurar Pentazocine ne yanda karfin Allurar ya dawo da hannun shi, wallahi duk wanda yake yin Pentazocine daka karshe haka hannun shi zai dawo sannan tana kashe jijiyoyin jiki idan yazo da karar kwana idan mutum bashida lafiya a nema jijiya a jikin shi a rasa har ya mutu
Wannan Allurar tana da illa sosai, wasu tunda aka musu sau daya a lokacin Surgery shikenan s**a fara yiwa kansu, wasu kuma abokai ne, wasu kuma labari aka basu shikenan. Wannan Allurar masifa ce, yanzu itace sabuwar kayan mayen matasa duk da cewa wasu sun dade suna yi. Allah ya raba mu da ita