29/09/2023
áđâsd
GAWUNA /GARO ADAVANCEMENT FORUM
29/09/2023
áđâsd
Astaghfirullaha wa'atubu ilaih!
Astaghfirullaha wa'atubu ilaih!!
Astaghfirullaha wa'atubu ilaih!!!
Astaghfirullaha wa'atubu ilaih!!!!
Astaghfirullaha wa'atubu ilaih!!!!!
Ya Allah ka yafe mana Laifukanmu🙏
Zamu Koyar Da Yadda Akeyin MTN SUBSCRIPTION Wato Betatalk Sub
Duk Wanda yake so yamin mgn ta WhatsApp
08089808889
Na fi gamsuwa da alkalancin Dr. Marzuq Ungogo
Muhawarar ‘Yan Takarar Gwamnan Kano: Fashin Ba’ki
Marzuq Ungogo, PhD
Muhawarar ‘yan Takarar Gwamnan Kano da BBC Hausa ta shirya kuma ta gabatar a yau ta mutu’kar ‘kayatar. Kwalliya ta biya ku’din sabulu domin muhawarar ta haska mana kowanne ‘dan takara, kaifin basirarsa, shirye-shirye da iya magana. Ga nawa fashin baqin.
1. Sha’aban Shara’da ya nuna bajintar fahimtar matsalolin al’umma da kuma kaifin basirar fito da hanyar gyara. Tabbas zaman Sha’aban a Abuja, gwagwarmayar da ya yi a Kano, da kuma ‘kasashen kewaye da ya zagaya ba su zube a banza ba.
2. Salihu Tanko Yakasai: shi ma ya nuna karsashi irin na Sha’aban, wajen fitar da al’kalumma da zayyana hanyoyin gyara na zamani. Sai dai kuma kash.…. Sha’aban ya yi masa fintinkau.
3. Muhammad Abacha: Biyun ‘daya, ko dai Abacha bai kai sauran ‘yan takara shiri ba ko kuma bai kai su hikimar zance ba. Abacha bai nuna wata bajinta ba wajen fahimtar matsalar talakan Kano ba, bai nuna sanin makamar aiki ba, sannan bai nuna karsashi ba.
4. Abba Kabir Yusuf: Abba ya nuna sanin makamar aiki sai dai duk aikin da ya bayyana zai yi to ba sabon abu ba ne. Abba maganarsa yawanci a kan ci gaba da ‘ko’karin Kwankwaso ne. Abba ya ci alwashin da’kile rashawa. Abba ya tafka kuskuren barin muhawara ana cikin yi. Tabbas uzurinsa a Kaduna bai kai muhawarar nan muhimmanci ba.
5. Nasir Gawuna: Ya fi kowa nuna sanin gwamnati, matsaloli da hanyoyin da an gwada su ba su ‘bulle ba. Abun mamaki sauran ‘yan takara idan s**a ce za su yi abu, Gawuna sai ya ce ai sun gwada hakan tuntuni. Gawuna dai ya nuna zai ci gaba da aiyuka ma su kyau gwamnonin Kano guda uku da s**a gabata musamman ma Ganduje. Ya kuma jaddada zai gyara kura-kuren gwamnatocin baya tun da ya sansu.
‘Dauraya
1. A ‘kwarewa da cancanta, Gawuna ya fi Abba. Sai dai ba wani abun birgewa ba ne ya yi ta maimaita zai ci gaba da aiki ko salon Ganduje.
2. Matsalar Abba dogaro da yawa a kan Kwankwaso. Tambayar shine idan s**ai fa’da, ya za a yi?
3. Sha’aban na da duk abin da Salihu Tanko ke da shi. Amman Salihu shi kuma ya gaza Sha’aban.
4. Muhammad Abacha bai shirya ba.
Daga ‘karshe:
Mutane za su yi iya shahada su zabi Gawuna ko Abba. Ba dole su cika alqawarin ci gaba da aikin Kwankwaso ko Ganduje ba kamar yadda s**ai alqawari. Sai dai duk su biyun su na da nagarta da kishin Kano. Akwai alamun za su yiwa al’umma aiki.
Duk wanda ya ci za’be ya kirawo Sha’aban da ‘Dawisu su taimake su wajen aiki. Abacha ya je ya ci gaba da kasuwancinsa da taimakon al’umma.
07/01/2023
Alhamdulillah kamar yadda kuke gani JABIR MUHAMMAD (SARAKI).Ne jagoran kungiyar GAWUNA/GARO ADVANCEMENT FORUM .
A YAYIN KARBAR certificate NA WANNAN KUNGIYA MAI ALBARKA TARE DA S.A NA NASIRU YUSUF GAWUNA.DA FATAN ALLAH YA BAMU NASARA
05/01/2023
ALLAH YA BAMU NASARA AMEEN
05/01/2023
Masha Allah yayi karbar tutar takara da dan takarar gwamnan jahar Dr. NASIRU YUSUF GAWUNA DA MATAIMAKINSA GARO SUKAYI A FILUN WASA NA SANI ABACHA DAKE KANO SUKAYI A JIYA DA FATAN ALLAH YA BAMU NASARA AMEEN. DAGA JAGORAN KUNGIYAR.... GAWUNA/GARO ADAVANCEMENT FORUM...... JABIR MUHAMMAD (SARAKI)
19/08/2022
Barcelona da sansanin Pierre Aubameyang za su kara a daren yau. Tattaunawa kai tsaye don tattaunawa kan yarjejeniyar Chelsea da yadda za a ci gaba bayan yarjejeniyar sirri da aka amince jiya da dare. 🚨🔵
Barça ta nemi kuɗi maimakon Marcos Alonso a cikin wannan yarjejeniya saboda dole ne su yi rajistar Koundé.
12/06/2022
🔴 TA TABBATA: Núñez ya koma Liverpool!
Anan MUKA DAKATA A JIYA… kuma yanzu an tabbatar da shi: Darwin Núñez zuwa Liverpool, an kammala yarjejeniyar ⭐️🇺🇾
▫️ Cikakkun yarjejeniya da aka cimma da safiyar Asabar a taron karshe a Portugal tsakanin Liverpool da Benfica da wakilan 'yan wasa.
▫️ Yuro miliyan 80 da aka ba da tabbacin biyan Yuro miliyan 20 ga Benfica, yayin da tsohon kulob dinsa Almería zasu samu nasu kason akan cinikayyar.
▫️ Núñez zai rattaba hannu kan kwantiragin har zuwa 2028, kwantiragin shekaru shida ne kuma ba shekara biyar ba kamar yadda Liverpool ta yanke shawara da wakilinsa a daren jiya.
▫️ Darwin bai buga wasa da Uruguay da Panama ba saboda kungiyarsa ba ta son yin kasada.
▫️ Núñez yana kasar Sipaniya tare da wakilansa a yanzu kuma zai isa kasar Ingila ranar litinin.
▫️ An riga an shirya gwaje-gwajen lafiyarsa a ranar Litinin, kamar yadda aka bayyana jiya:amma lokaci ne kawai zai tabbatar.
▫️ Kwangiloli sun rattaba hannu a yau tsakanin Liverpool da Benfica, an shirya takardun aiki - sanarwa a hukumance kawai muke dakon jira.
Yaya kuke kimanta wannan sa hannun Liverpool? ❤️🔥🇺🇾
Ku bayyana mana raayinku