15/10/2026
SANARWA GA AL'UMMA! 🇳🇬🗳️
Assalamu alaikum!
Duk wanda ya yi rajistar zaɓe, muna kira gare shi da ya hanzarta zuwa karɓar katin zaɓensa idan ya kammala rajista.
Katin zaɓenka shi ne mabuɗin sauyi! Da shi ne za mu iya zaɓar sabuwar gwamnati mai kishin al'umma, wadda za ta kula da ci gaban matasa, samar da ayyukan yi, inganta rayuwar jama'a da kawo ci gaba a jiharmu.
Kada mu yi sakaci da haƙƙinmu na zaɓe. Mu tashi tsaye, mu karɓi katunanmu, domin makomar jiharmu da matasanmu tana hannunmu.
Sabuwar gwamnati, sabon fata, sabon ci gaba!
Allah Ya ba mu shugabanci na gari, amin. 🤲🗳️