*GIDA DUBU YOUTH FORUM DUTSE*
_21-05-2022_
Assalamu Alaikum,
*GA WATA MUHIMMIYAR SANARWA*
Gobe insha Allah, ana sanar da fara aikin tsaftace kwatoci da magudanan ruwa a unguwar gida dubu da kewaye.
Wannan tasa ake gayyatar kowa da kowa musamman matasa, yara, iyaye da duk wanda yasan ze bada gudumawar sa a yayin gudanar da wannan aiki. Sannan ga wanda suke da kayan aiki suma ana roqo da su fito dashi idan an gama aiki su tafi da kayan su.
Allah ya bada ikon fitowa. Sannan aikin ze fara neh da misalin qarfe 7:00 am (Na safe.)
Gida Dubu Yadi Security, Patrol and Guard
Gida Dubu Yadi Security, Patrol and Guard is a voluntary security organisation.
This organisation was formed by the Gida Dubu Elders Forum in collabration with Gida Dubu Youth Forum Dutse.
10/01/2022
*GIDA DUBU SECURITY, PATROL & GUARD*
_Assalamu Alaikum,_
```Kamar ydda nayi dan jawabi kwanaki game da matasa dake gudanar da aikin sintiri a unguwar gida dubu cewa" Suna suna buqatar agaji na kayan aiki irin su toch light da gora,irin su rigar sanyi etc. An samu gudumawa da ta samar da toch light guda biyar (5) daga irin matasan da muke dasu masu kishi a wannan unguwa.
Muna godia sosai, allah ya saka da alkhairi. Kuma haryanxu qofa a bude take ana buqatar abin daya sawwaqa na abin da aka lissafa a sama na kayan aiki```
22/10/2021
*GIDA DUBU YOUTH FORUM DUTSE*
21-10-2024
_GIDA DUBU YADI SECURITY PATROL AND GUARD_
*Assalamu Alaikum*
```Yau kusan sati uku (3) kenan da kafah qungiyar sintiri a unguwar gida dubu,maqasudin kafa wannan qungiya shine don a dinga saka idanu da kuma kawo qarshe aikata wasu dabi'u da basu kamata su dinga faruwa ba a wannan unguwa ta gida dubu. Kwamitin dattawa na wannan unguwa da kuma qungiyar matasa ta wannan unguwa sunyi iya bakin iyawar su don ganin wannan abu ya tabbata,kuma alhamdulillahi aka samu hadin kai daga dukkan mazauna unguwar gida dubu dama wanda su rabarta.
Alhamdulillah bayan fara wannan aiki na sintiri wanda da daddare yafi qarfi inda ake farawa daga 12:00am (Na dare) zuwa 5:000am (Na asuba) shige da fice yana tsayawa cak a cikin wannan unguwa a tsakankanin wannan lokaci idan ba tare da wani dalili karbabbe ba. Al'ummar wannan unguwa sheda ne tunda aka fara gudanar da wannan aiki an samu canji sosae wajen tabbatuwar tsaro a cikin wannan unguwa wanda kuma ba qaramar nasara ba ce da endai aka dore da hakan sai unguwar gida dubu ta zama ta daban, sai mun zama abin kwatance da koyi ga sauran unguwanni insha Allahu
Babu abin daya kamata a yanzu illah mu taya masu gudanar da wannan aiki da addu'a,sannan aci gaba da basu hadin kai yadda ya kamata da kuma gudumawa ta kowane fanni. Domin sun sadaukar da kansu,lokacin su, da duk wata wal walar su suna qoqarin kare mana unguwa,dukiyoyi harma da rayuka a yayin da da kowa yake shan baccin sa. Allah ya saka musu da mafificin alkhairi, Allah ya kare mu ya kuma tsare mu daga dukkan wani sharri ameen.
A qarshe zanyi amfani da wannan dama kamar yadda ake ta sanarwa a masallatan mu cewa yan sintirin nan namu suna amfani da kayayyakin aiki kamar su UNIFORM, TOCH LIGHT, GORA, WHISTLE, DORINA, Etc. Wanda wadannan kaya ana da qarancin su qwarai da gaske..Wannan tasa ake ta sake neman taimako dai daga al'umma duk wanda yake da halin taimakawa da daya daga cikin wadannn
Alhamdulillah
Alhamdulillah
*GIDA DUBU YADI SECURITY, PATROL AND GUARD*
_04-10-2021_
_Assalamu Alaikum,_
Alhamdulillah Alhamdulillah
Bayan fara aiki da tabbatacciyar qungiyar sintiri ta gida dubu, wanda cikin nasara TEAM A sun fara aiki rana JUMA'A zuwa LAHADI. Aiki ya tafi yadda ya kamata sakamakon hadin kai da al'umma s**a bayar musamman mazauna unguwar gida dubu...
Allah ya sakawa kowa da alkhairi.
Yau LITININ Insha Allahu TEAM B zasu fara aiki zuwa ranar LARABA. Ana sanar da officers din mu da suke team B da kuma wanda basu taba fitowa aiki ba cewa yau ana so su fito OFFICE dawuri 11:00pm sharp.
Sannan ga duk wanda ke da sha'awar shiga wannan aikin lada na taemakon kai da kai, tou suma qofa a bude take muna so mu gansu don a tan tance su. Muna qara godia sosae da hadin kai da aka bayar kuma muna fata za'a ci gaba da bada wanga hadin kai duk dai mu samu a gudu tare a kuma tsira tare.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Hakimi Street, Dutse
Abuja
70092
