PBAT Media Centre Hausa

PBAT Media Centre Hausa

Share

Muna muku maraba da zuwa shafinmu na PBAT MEDIA CENTER HAUSA

03/06/2026

Mu tattauna abubuwan da s**a faru a watan Mayu 2026 a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba :

Takaitaccen Rahoton na watan Mayu:

Tattalin Arziki: Ya haɓaka zuwa kashi 3.89%

Fasaha/Bincike: An zuba dala miliyan 500 ($500M)

Tallafin Dalibai: An biya bashin naira biliyan 4 (₦4bn)

Sufurin Jiragen Sama: An amince da Kamfanin Hayar Jiragen Sama na Najeriya (Nigeria Aircraft Leasing Company)

Muna son jin ra'ayoyinku game da waɗannan nasarorin da s**a shafi rayuwar al'umma kai tsaye. Ku bayyana ra'ayinku a komen sakshan.

03/06/2026

Laraba, 3 ga Yuni, 2026 |

📌 Gwamnatin Tarayya tare da IITA sun ƙaddamar da babban shirin kasuwancin noma domin horas da matasa miliyan 6 tare da samar da sabbin kasuwanci 500,000

📌 Shugaba Bola Tinubu ya yaba da MREIF yayin da asusun ya samar da jinginar gidaje ta naira biliyan 128 ga iyalai 1,859 a Najeriya

📌 Najeriya ta zama ƙasa ta farko a Afirka da ta rungumi tsarin daidaita hada-hadar kasuwar hannayen jari na T+1

📌 Alamar Samun Bashi ta Najeriya (Credit Access Index) ta koma matsayi mai kyau bayan sama da shekara guda

Nishaɗin Masu Karatu.

02/06/2026

| Talata, 2 ga Yuni, 2026

Duba manyan labaran yau:

Daga ƙarfafa tsaron ƙasa zuwa inganta cibiyoyin kiwon lafiya da bunƙasa tattalin arziki, Najeriya na ci gaba da ɗaukar manyan matakai na ci gaba.

📌 An ceto fasinjoji 23 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kogi

📌 An ƙaddamar da katafaren ginin zamani na Bola Tinubu a Asibitin FMC Abuja

📌 Kuɗin da ake kashewa wajen shigo da abinci daga ƙasashen waje ya ragu da kashi 7.37%

📌 An buɗe (June Savings Bond)

Nishaɗin Mai Karatu!

01/06/2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa Eko Atlantic, Jihar Legas, domin halartar bikin cika shekaru 70 da kafuwar Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya. 🇳🇬⚓️

01/06/2026

📌 Dangane da Daliban da Aka Sace a Jihar Oyo:

Tinubu ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da dukkan hanyoyin da take da su domin ceto waɗannan malamai da ɗaliban da aka sace.

01/06/2026

📌 Game da Ɗaliban da Aka Sace a Jihar Oyo:

Tinubu ya ba da umarnin kafa sansanonin Sojoji a cikin garuruwan da abin ya shafa, kamar yadda s**a roƙi Gwamnati.

01/06/2026

📌 Dangane da Daliban da Aka Sace a Jihar Oyo:

Tinubu ya tura rundunar ceto ta musamman domin tabbatar da kubutar da daliban da aka sace tare da malamansu cikin gaggawa.

01/06/2026

Bisa umarnina, bayan ziyarar wata babbar tawagar Gwamnatin Tarayya da na aike zuwa al’ummomin Esiele da Yawota da ke Karamar Hukumar Oriire a Jihar Oyo, na amince da ɗaukar ma’aikatan tsaron dazuka (Forest Guards) 1,000 aiki tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Oyo.

01/06/2026

| Litinin, 1 ga Yuni, 2026

Bayan sace ɗalibai da malamai da aka yi a makarantar jihar Oyo, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaukar Masu Tsaron Daji 1,000 tare da tura tawagar musamman ta ceto domin tabbatar da tsaron dazuzzuka da kare ɗalibanmu.
Babu sassauci ko kaɗan kan batun tsaro.

Sauran labarai masu jan hankali:

📌 Jimillar darajar kasuwar hannayen jari na NGX ya kai Naira tiriliyan 160.5.

📌 Mata da matasa 37,000 za su amfana da manyan damar tattalin arziki a sashen samar da madara da sarrafa ta.

📌 Ana rarraba buhunan taki miliyan 1.9 domin ƙarfafa samar da abinci da tabbatar da wadatar abinci a ƙasa.

Barka da shiga sabon wata! 🎉

01/06/2026

PBATVersary 3.0: Shekaru Uku na Gyara, Ci Gaba da Sabuwar Fata.

Shekaru uku kenan da fara aiwatar da Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda), kuma Najeriya na ci gaba da ganin manyan gyare-gyare, zuba jari masu muhimmanci, da manufofi masu sauyi da ke da nufin gina ƙasa mai ƙarfi da wadata.

Daga ilimi, kiwon lafiya, da ƙirƙire-ƙirƙiren fasahar zamani zuwa gyaran tattalin arziki, bunƙasa noma, da ƙarfafa al’ummomi a matakin ƙasa, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da shimfiɗa tubalin ci gaba mai ɗorewa da farfaɗowar ƙasa.

A wannan fitowar na wasiƙarlabarai, mun haskaka muhimman nasarori, shirye-shirye masu tasiri, da ci gaban da aka samu a manyan fannoni daban-daban cikin shekaru uku da s**a gabata.

Ku karanta, ku shiga tattaunawa, kuma ku kasance masu samun sahihan bayanai yayin da muke bibiyar tafiyar gyare-gyare, ci gaba, da sabuwar fata ga dukkan ‘yan Najeriya.

Want your business to be the top-listed Government Service in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Address


Abuja