24/02/2026
MAHAIFINMU YA MUTU, ZA MU IYA YIN ZAMAN MAKOKI ?
Tambaya :
Malam mahaifina ya rasu, sai wani malamin islamiyyarmu ya ce min ba kyau zaman makoki, to gaskiya kaina ya daure, saboda na taso na ga ana yi, kuma idan ban yi ba za'a ce ban damu da mahifinmu ba, malam yanzu yaya zan yi ? Allah ya datar da kai zuwa dukkan alkairai .
Amsa :
To dan'uwa Allah ya ba mu dacewa gaba daya, tabbas malamai sun tattauna akan hukuncin zaman makoki, saidai sun kasu kashi uku :
1. Akwai wadanda s**a tafi akan makaruhi ne, saboda hadisin Jarir RA wanda Imamu Ahmad ya rawaito cewa: "Mun kasance muna kirga taruwa yayin mutuwa da kuma yin abinci ga gidan da aka yi mutuwa daga cikin rurin da Allah da ya haramta" , Musnad : 6905, don haka suna cewa, saidai a hadu da wadanda aka yiwa rasuwa akan hanya ko a kasuwa, ko masallaci ayi musu ta'aziyya, wannan ita ce maganar Shafi'i a cikin Umm 1\318, haka Nawawy a Majmu'u 3\306 .
2. Akwai wadanda s**a ta tafi akan cewa bidi'a ne, kamar Ibnul-kayyim a zadul ma'ad 1\527
3. Akwai malaman da s**a tafi akan halaccin zaman makoki, saboda hadisin da nana A'isha ta rawaito cewa, lokacin da aka kashe Zaid dan Haritha da Ja'afar dan Abu-dalib Annabi s.a.w. ya zauna a wani wuri, duk wanda ya gan shi zai ga alamun bakin cikin tare da shi, sai wani mutum ya zo ya ce masa : ga matan Ja'afar can suna ta kuka, sai Annabi s.a.w ya umarce shi da ya je ya hana su, su kuma yi hakuri" Bukhari hadisi mai lamba ta : 1299. Wadannan malaman suna cewa : Za'a iya fahimtar hallacin zaman makoki a wannan hadisin a wurare guda biyu :
A. Fadin nana A'isha cewa : ya zauna ana ganin alamun bakin ciki tare da shi da kuma zuwan wancan mutumin, dalili ne da yake nuna cewa : yana zaune ne a wurin da mutane s**a sani kuma suke zuwa su same shi.
B. Kasancewar bai hana matan Ja'afar taruwar da s**a yi ba, kawai kukan ya yi umarni da a hana su.
Wannan magaanar ta hallaci an rawaitota daga Imamu Ahmad kamar yadda ya zo a Insaf 5\565 da kuma Ibnu-Abdulbarr na Malakiyya,, kamar yadda ya zo a littafinsa na Alkafy 1\283, sannan wasu daga cikin Hanafiyya sun tafi akan haka kamar yadda ya zo a Binaya 3\303
Prof. Khalid Al-mushaIkih (daya daga cikin manyan daliban Sheik Bn Uthaimin) ya rinjayar da zance na uku, saidai za'a guji abubuwa kamar haka a lokacin wannan zaman :
1. Yawaita yin abinci, da masu karbar gaisuwa, zai yi kyau ya zama makusantansa ne kawai za su amshi gaisuwa.
2. Nisantar yin laccoci a wurin, domin hakan na daga cikin bidi'o'in da ba su da hujja.
3. Nisantar tsawaita zaman, a yi shi gwarwadon bukata.
Duba maganarsa a : Fiqhunnawazil shafi na : 75
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
23/02/2026
MATA GOMA SHA DAYA (HADISIN UMMU-ZAR'IN) //04
4● MACE TA HUDU !!!
العربية: ﻗَﺎﻟَﺖْ ﺍﻟﺮَّﺍﺑِﻌَﺔُ ﺯَﻭْﺟِﻲ ﻛَﻠَﻴْﻞِ ﺗِﻬَﺎﻣَﺔَ ﻟَﺎ ﺣَﺮَّ ﻭَﻟَﺎ ﻗُﺮَّ ﻭَﻟَﺎ ﻣَﺨَﺎﻓَﺔَ ﻭَﻟَﺎ ﺳَﺂﻣَﺔ.
Hausa: Mace ta hudu tace: Mijina kamar dare irin na yankin Makka yake babu zafi babu sanyi, kuma babu wani tsoro da zaka ji, kuma bayi da wani hali da zaka kosa dashi.
→Abunda take nufi mijinta kamar dare na yankin Makka, idan kasan Makka da garuruwan da ke makwabtaka da ita zaka san yanki ne mai matukar zafi amma idan dare yayi yanayin wajen sai ya zamanto daidai babu sanyi kuma babu zafi, kuma babu tsoro tana nufin a bangaren mu'amala ta aure babu abunda zata nema ta rasa daga gare shi, a takaice dai tana nufin mijinta mutum ne mai kyakykyawar dabi'a bayi da wani halin da za'a kosa dashi ta kowace fuska.
English: The Fourth One said: My husband is like the night of Tihama (the night of Hijaz and mecca), neither too cold nor hot, neither there is any fear of him nor grief.
Mu hadu a rubutu na gaba inshaa ALLAH..
Muslim UMMAH ☪️
21/02/2026
MATA GOMA SHA DAYA (HADISIN UMMU-ZAR'IN) //03
3● MACE TA UKU !!!
العربية: ﻗَﺎﻟَﺖْ ﺍﻟﺜَّﺎﻟِﺜَﺔُ ﺯَﻭْﺟِﻲ ﺍﻟْﻌَﺸَﻨَّﻖُ ﺇِﻥْ ﺃَﻧْﻄِﻖْ ﺃُﻃَﻠَّﻖْ ﻭَﺇِﻥْ ﺃَﺳْﻜُﺖْ ﺃُﻋَﻠَّﻖ.
Hausa: Mace ta uku tace: Mijina mai tsawo ne (Mutum wanda yake da tsayi kuma siriri yana da mummunan hali) idan nayi magana sai ya sake ni, idan nayi shiru kuma sai a mayar dani gefe (a daina mu'amala da ni).
→ Abunda take nufi mijinta mai tsawo ne a tsarin halitta, (ana iya siffanta shi da bayi da hankali, hankalinsa yayi sama) a takaice a fuskar halitta bai kayatar da ita ba hakanan a fuskar halayya nan ma bai kayatar da ita ba, idan yayi mata laifi ba daman tayi magana, idan kuma tayi magana Toh zai sake ta, idan kuma tayi shiru za'a mayar da ita mu'allaka wato ta zamto tamkar bata da miji ta zama saniyar wararre, a takaice babu abunda take mora da mijin irin wanda sauran mata suke mora daga mazajen su.
English: The Third one said: My husband statured fellow (I.e he lacks about him, he would devorce me, and if I keep quiet I would be made to live in a state of suspense (neither completely abandoned by him nor entertained as wife.)
Mu hadu a rubutu na gaba inshaa ALLAH.
https://chat.whatsapp.com/6nQfgB3w0V6CnQYJ7fNlZ0
19/02/2026
MATA GOMA SHA DAYA (HADISIN UMMU-ZAR'IN) //02
2● MACE TA BIYU !!!
العربية: ﻗَﺎﻟَﺖْ ﺍﻟﺜَّﺎﻧِﻴَﺔُ ﺯَﻭْﺟِﻲ ﻟَﺎ ﺃَﺑُﺚُّ ﺧَﺒَﺮَﻩُ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﺧَﺎﻑُ ﺃَﻥْ ﻟَﺎ ﺃَﺫَﺭَﻩُ ﺇِﻥْ ﺃَﺫْﻛُﺮْﻩُ ﺃَﺫْﻛُﺮْ ﻋُﺠَﺮَﻩُ ﻭَﺑُﺠَﺮَﻩ.
Hausa: Mace ta biyu tace: Mijina Bazan iya bada labarinsa ba, ina jin tsoro idan har zan bada labarinsa na ambacesa zan ambaci komai nasa gaba daya bazan rage masa ba.
→ Abunda take nufi mijinta yana da halaye munana wanda sun kai matuka ta fuskar yawa wanda kawai sai dai idan za'a kamanta amma baki bazai iya fadan su gaba daya ba, idan kuma har zata iya ambaton labarinsaToh lallai zata ambaci halayyarsa ciki da waje ba tare da ta rage masa komai ba wato bazata yi masa karya ba.
English: The second one said: My husband (Is so bad) that I am afraid I would not to be able to describe his faults both visible and invisible completely.
Mu hadu a rubutu na gaba inshaa ALLAH.
http://www.muslimummah.com/
18/02/2026
MATA GOMA SHA DAYA (HADISIN UMMU-ZAR’IN) //01
1● MACE TA FARKO !!!
العربية: ﻗَﺎﻟَﺖْ ﺍﻟْﺄُﻭﻟَﻰ ﺯَﻭْﺟِﻲ ﻟَﺤْﻢُ ﺟَﻤَﻞٍ ﻏَﺚٍّ ﻋَﻠَﻰ ﺭَﺃْﺱِ ﺟَﺒَﻞٍ ﻭَﻋْﺮٍ ﻟَﺎ ﺳَﻬْﻞٌ ﻓَﻴُﺮْﺗَﻘَﻰ ﻭَﻟَﺎ ﺳَﻤِﻴﻦٌ ﻓَﻴُﻨْﺘَﻘَﻞ.
Hausa: Mace ta farko tace: Mijina naman rakumi ne kwamusashshe wanda babu tsoka acikinsa, wanda aka daura akan kololuwar dutse mai wuyar hawa (Dutsen) bayi da Saki (gashi da sarkakiya da dumi acikinsa) ballantana a hau a dauko, shi kuma naman bayi da tsoka ajikinsa mai yawa b***e wannan tsokar ta kwadaitar da mutum bazai sha wahalar hawa ya dauko ba.
→Abunda take nufi mijinta ba mai kyakykyawar hali bane shiyasa ta siffanta shi da namar rakumi, saboda naman rakumi bayi da daraja kamar naman tsuntsaye da kaji awancan lokacin domin ko a Aljannah naman tsuntsaye akayi alkawari. Naman rakumi shine karshe wajen daraja saboda taurinsa yana da wahalar dahuwa Toh duk lokacin da aka siffanta mutum da naman rakumi to ana nufin taura-tauran mutum ne bayi da kyawawan hali. Shine ta siffanta shi da naman rakumi saboda taurinsa ya zamo kyamatacce wanda bayi da kiba sannan kuma aka dauki naman aka daura saman wani dutse mai wuyar hawa da sarkakiya da kuma duhu, ma’ana dai mijinta mutum ne mai mummunar dabi’a wanda zama dashi babu dadi. (wannan shine abunda nace ta farko tace)
English: The First One said: My husband is a sort of the meat of lean camel placed at the top of a hill, which it is difficult to climb up nor (the meat) is good enough that one finds in oneself the urge to take it away (From the top of that mountain).
Mu hadu a rubutu na gaba inshaa ALLAH.
https://chat.whatsapp.com/6nQfgB3w0V6CnQYJ7fNlZ0
*Muslim UMMAH ☪️*
26/03/2025
She has reached the age of puberty but she is not strong enough to fast
Question :
A girl has reached puberty at the age of eleven and she is weak. Does she have to fast? If she is unable to fast then what should she do?.
Answer
If the situation is as described, then she has to fast because menstruation is one of the signs of puberty for women, if it comes when she is nine years old or more. If she is able to fast then she must do it at the proper time, and if she is unable to do it or she faces extreme hardship in doing so, then she may not fast but she must make up the days that she did not fast when she is able to do so. End quote.
Muslim UMMAH ☪️
24/03/2025
DAGA YAUSHE GOMAN KARSHE TAKE FARAWA ?
Tambaya;
Mutane da yawa sun aiko da tambaya, da neman karin haske game da lokacin da goman karshe a Ramadhana take shiga, Yaya bayanin da wasu s**a yi na cewa goman karshe tana farawa ne daga daren ashirin, idan aka kai AZUMI na (19) ?
Amsa
Goman karshe tana shiga ne in an kammala AZUMI na (20) an shiga daren (21).
Daren ashirin yana cikin goma ta biyu, ba ya cikin darare masu girman daraja, wadanda Allah ya yi rantsuwa da su a farkon suratul Fajr.
Duka hadisan da s**a zo akan falalar goman karshe, sun kunshi daren 21- zuwa daren 30 ga watan Ramadhan .
Idan har aka lissafa da daren (20) a cikin goman karshe, dararen za su zama guda (11), hakan kuma ya sabawa dalilan Sharia da s**a kayyade su da guda (10).
Duk Wanda zai yi sallar tahajjudi saboda fatan riskar goman karshe to ya fara daga gobe.
Allah Ne Mafi Sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
19/9/1445
29/3/2024
Muslim UMMAH ☪️