Gwagware Online Vanguards

Gwagware Online Vanguards

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gwagware Online Vanguards, Katsina.

Gwagware Online Vanguards kafar yaɗa labarai mai mayar da hankali kan harkokin siyasa, wadda ta ƙunshi ƙwararrun masanan sadarwa masu jajircewa wajen yaɗa sahihan bayanai da inganta tasiri ta hanyar dijital.

21/04/2026

SAKON TAYA MURNA

Muna miƙa sakon taya murna ga
Engr. Muttaka Rabe Darma

Bisa (nomination) da aka yi masa a matsayin
"Ministan Tarayyar Najeriya"

Muna masa fatan alheri da nasara a wannan muƙami, tare da addu’ar Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa cikin adalci da gaskiya,

Allah Ya taya riko.

Gwagware Online Vanguards
April 21st, 2026

14/04/2026

Gwamnan jahar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya rattaba hannu akan dokar ta baci, kan kauraye a jihar Katsina, tare da bada umarnin hukunta su nan take

13/04/2026

Bazamu daina tallata Ayyukan Maigirma Adalin Gwamnan Jahar Katsina ba, Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON

Inji Hon. Jamilu Kayauki, Dan takarar Majalissar Dokoki ta jahar Katsina, ƙaramar Hukumar Batagarawa

Photos from Gwagware Online Vanguards's post 12/04/2026

DR. SIRAJO YAKUBU BATAGARAWA YA AYYANA ANIYARSA NA TAKARAR KUJERAR ƊAN MAJALISSAR TARAYYA BATAGARAWA/RIMI/CHARANCHI A ZAƁEN 2027 A ƘARƘASHIN JAM’IYYAR APC

Bayan tuntuba da neman shawarwari da kuma kiraye-kirayen da aka yi masa a dukkan ƙananan hukumomi uku, Dr. Sirajo Yakubu ya bayyana aniyarsa a gaban shugabannin jam’iyya, kansiloli, masu ba da shawara da magoya baya a sakatariyar APC ta Batagarawa.

Gabanin babban zaɓen 2027, Dr. Sirajo Yakubu Batagarawa, yau 12 ga Afrilu, 2026, ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar Batagarawa/Rimi/Charanchi a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Wannan sanarwa ta gudana a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Batagarawa.

Da yake jawabi a wajen taron, Dr. Sirajo ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka ya samo asali ne daga irin gagarumar goyon baya da karɓuwa da ya samu daga shugabannin al’umma, matasa, da ’ya’yan jam’iyya a faɗin ƙananan hukumomin uku (3). Ya jaddada aniyarsa ta samar da wakilci nagari mai tasiri, wanda zai mayar da hankali kan haɗin kai, kusanci da al’umma, da kuma kawo ci gaba mai ɗorewa da zai amfanar da matasa da kuma al’umma baki ɗaya.

Taron ayyana takarar ya samu halartar shugabannin jam’iyyar APC, kansilolin ƙaramar hukumar Batagarawa masu ci, masu ba da shawara (S.A.s), tare da dimbin magoya baya da masu fatan alheri. Shugabannin jam’iyyar sun yaba da yadda ya bi matakan shawarwari kafin ayyana takararsa, tare da jaddada aniyar jam’iyyar na tabbatar da adalci a dukkan matakai, yayin da masu sa ido kan harkokin siyasa ke ganin shigowarsa zai ƙara sauya fasalin siyasar Batagarawa/Rimi/Charanchi.

Gwagware Online Vanguards
12 ga Afrilu, 2026

06/04/2026
22/03/2026

Wakilin mu a Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Nura Haske a lokacin da yayi ma Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Ummaru Raɗɗa barka da Sallah...

14/03/2026

Muna JAJE tare da ALHINI ga yan uwan mu, yan Jam'iyyar ADC yadda TARO ya tashi, wasu sun dage se sun nuna Jam'iyyar FUSATATTU ce.

13/03/2026

𝐒𝐚𝐤𝐨𝐧 𝐠𝐨𝐝𝐢𝐲𝐚 𝐝𝐚 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐬𝐚𝐧𝐚𝐫𝐰𝐚 𝐭𝐚 𝐄𝐦𝐩𝐨𝐰𝐞𝐫𝐦𝐞𝐧𝐭 𝐧𝐚 ₦𝟑,𝟖𝟓𝟎,𝟎𝟎𝟎 𝐝𝐚 𝐅𝐨𝐮𝐧𝐝𝐚𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐧𝐚 𝐋𝐚𝐭𝐞 𝐀𝐦𝐢𝐧𝐮 𝐌𝐨𝐝𝐢𝐛𝐛𝐨 𝐳𝐚'𝐚 𝐠𝐚𝐛𝐚𝐭𝐚𝐫 𝐛𝐢𝐬𝐚 𝐣𝐚𝐠𝐨𝐫𝐚𝐧𝐜𝐢𝐧 𝐇𝐨𝐧. 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥 𝐊𝐚𝐫𝐢𝐦 𝐀𝐥'𝐀𝐦𝐞𝐞𝐧 𝐌𝐨𝐝𝐢𝐛𝐛𝐨 ( 𝐒𝐞𝐜𝐫𝐞𝐭𝐚𝐫𝐲 𝐊𝐚𝐭𝐬𝐢𝐧𝐚 𝐋𝐆, 𝐒𝐚𝐫𝐤𝐢𝐧 𝐌𝐚𝐥𝐚𝐦𝐚𝐢 𝐧𝐚 𝐌𝐚𝐠𝐚𝐣𝐢𝐧 𝐆𝐚𝐫𝐢𝐧 𝐊𝐚𝐭𝐬𝐢𝐧𝐚, 𝐏𝐫𝐨𝐩𝐫𝐢𝐞𝐭𝐨𝐫 𝐌𝐨𝐝𝐢𝐛𝐛𝐨 𝐀𝐜𝐚𝐝𝐞𝐦𝐲 𝐊𝐚𝐭𝐬𝐢𝐧𝐚 & 𝐂𝐄𝐎 𝐒𝐌 𝐌𝐞𝐝𝐢𝐚 𝐓𝐞𝐚𝐦 𝐊𝐚𝐭𝐬𝐢𝐧𝐚 𝐒𝐭𝐚𝐭𝐞

11/03/2026

Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda yana karatun Al-ƙur'ani a Masallacin Annabi Muhammadu da ke Madina, bayan ya ziyarci kasar Saudiyya domin Ibadar Umrah.

Vanguard

02/03/2026

Taƙaitattun Rahotannin Mako, na ayyukan Maigirma Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Rada PhD, CON.

22/11/2025

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN.

Allah yayima Diyata SAFARA'U ABDULKARIM AL'AMEEN MODIBBO ( HAJIYAR RADDA) Rasuwa a yanzu.

Za'ai janaza a nan gidan MODIBBO dake nan GRA. Kusa da Police Children School Katsina. Bisa titin tsohuwar Government House Katsina. Da misalin karfe 10:00am.

Muna rokon Allah yasa mai ceto ce. Bayan haka muna barar addu'o'in ku akan jinyar da mahaifi na yake yi a nan Kano. Muna rokon Allah ya bashi lafiya.

Abdulkarim Al'Ameen Modibbo ( Secretary na karamar Hukumar Katsina,
Sarkin Malamai na Magajin Garin Katsina & Proprietary Modibbo Academy Katsina 07061505055)

Want your business to be the top-listed Government Service in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Katsina