01/04/2026
Labari da Dumi-Dumi
Hukumar INEC ta sanar da cewa za ta dakatar da mu’amala da dukkan bangarorin da ke takaddama akan shugabanci jam’iyyar ADC gaba daya, (Bangaren Sen. David Mark da bangaren Hon. Nafiu Bala).
Haka kuma, ba za ta sake sa ido ko halartar tarukan jam’iyyar ba, har sai kotu ta yanke hukunci na karshe.
Bugu da kari, INEC za ta cire sunayen su Sen. David Mark a matsayin shugabannin jam’iyyar na yanzu daga shafinta na yanar gizo (portal), domin tabbatar da bin umarnin kotu da kuma daukan matsayi na tsaka-tsaki.
16/03/2026
Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Ya Amince Da Ɗaukar Malaman Makaranta Dubu Ɗaya Da Ɗari Bakwai A Lungu Da Saƙon Jihar Domin Bunƙasa Koyo Da Koyarwa A Faɗin Jihar
Sahara Reporters Hausa ✍️
16/03/2026
DAGA MAIDUGURI
Rundinar 'yan sandan Nigeria reshen jihar Borno ta tabbatar da harin kunar bakin wake da ya faru dazu a cikin birnin Maiduguri a gurare uku
(1) B0m na farko ya tashi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri
(2) B0m na biyu ya tashi a kasuwar Monday Market dake Maiduguri
(3) B0m na uku ya tashi a Post Office fly over dake Maiduguri
Bayan aukuwar hare-haren kunar bakin waken guda uku zuwa yanzu 'yan sanda masu binciken ababen fashewa (EOD) suna ci gaba da aikin bincike da tsabtace wuraren
An dawo da zaman lafiya a wuraren, kuma ana shawartar mazauna Maiduguri da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da kasancewa cikin shiri da lura
Rundinar 'yan sandan Borno sunce a kira wadannan layukan waya domin daukin gaggawa 08068075581, 08023473293
Muna rokon Allah Ya yaye mana wannan masifa
Sahara Reporters Hausa
15/03/2026
Hukumar NDLEA ta k**a wani dattijo da hodar ibl!s da aka ɓoye cikin barkono a filin jirgin sama na Abuja.
Hukumar kula da safarar miyagun ƙwayoyi ta k**a wani dattijo mai shekaru 74 bisa zargin ƙoƙarin safarar kilogram 11 na hodar iblis a filin jirgin sama na Abuja.
An ruwaito cewa jami’an hukumar sun gano miyagun ƙwayoyin ne da aka ɓoye cikin barkono yayin binciken kaya a Nnamdi Azikiwe International Airport da ke Abuja.
Daga Abba Sani Pantami
15/03/2026
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed na shirin komawa APC
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, Bala Mohammed, na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a cikin makon nan, idan har tattaunawar da ake yi ta yi nasara inji rahotan Arise News.
Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan ya gana da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugabannin APC, inda ya nuna sha’awarsa ta shiga jam’iyyar mai mulki.
Ana kuma tattaunawa kan sharuddan sauya shekar tasa.
Rahotanni sun ce daga cikin abubuwan da ake tattaunawa akwai ba shi tikitin takarar Sanata, amma ba za a ba shi cikakken iko da tsarin jam’iyyar APC a jihar Bauchi ba, kuma ba zai iya zabar wanda zai gaje shi a matsayin gwamna ba.
An kuma ce an bukaci gwamnan ya ba da hakuri ga Seyi Tinubu, bayan wani rikici da ya faru a bara lokacin da dansa ya soki rabon tallafin Ramadan da Seyi ya yi a Bauchi.
A bangaren Seyi Makinde da wasu jiga-jigan PDP kuwa, an bayyana takaici kan wannan shiri, suna mai cewa sauya shekar shugaban gwamnonin PDP zai iya kara raunana jam’iyyar adawa a kasar.
Sahara Reporters Hausa
13/03/2026
DA DUMI-DUMI: Za a gurfanar da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, tare da ƴaƴansa biyu a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja domin fuskantar sabuwar shari’ar zargin badakalar kudi Naira biliyan 1.35.
13/03/2026
Gidauniyar Professor Pantami Ta Kaiwa Jam'iyyar APC Ta Jihar Gombe Kyautar Naira Miliyan 10,000,000, Da Macaroni Katon Dubu 1,000, Na Azumin Ramadan Da Kuma Azumin Lenten Wadanda Dukkansu Biyu Ake Yi A Yanzu
Idan baku manta ba a kwanakin baya gidauniyar Professor Isa Ali Pantami ta raba kayayyakin abinci fiye da buhu 12,500 da kuma kuɗi Naira miliyan 33,750,000 ga malaman Addini a jihar Gombe, a cikin wannan watan na Ramadan.
A jiya Alhamis tawagar wakilan Professor Isa Ali Pantami, karkashin jagorancin Alhaji Ahmad Abubakar Walama, tsohon Kwamishina mai kula da harkokin kananan hukumomi da Masarautu kuma tsohon shugaban Ƙaramar hukumar Dukku (sau biyu) ya jagoranta, da sauran manyan tawaga ta Dattawa, malamai da matasa.
Tawagar ta ziyarci ofis din jam'iyyar, inda s**a kai kyautar Naira miliyan 10,000,000, da Macaroni Katon dubu 1,000, domin azumin Ramadan da kuma Azumin Lenten wadanda dukkansu biyu ake yi a yanzu.
Tawagar ta samu tarba mai kyau a hedkwatar APC ta jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Shugaban jam'iyyar ta jiha Mohammed Dantata Ndus, wanda ya samu wakilcin mataimakinshi Abdullahi Baba Abuja da Sakataren jam'iyya da mambobin Kwamitin zartarwar Jam'iyya na jiha.
Farfesa Isa Ali Ibrahim (Pantami) ya shafe shekaru da dama yana tallafawa jama’a a lokacin watan Ramadan, inda adadin tallafin yake sauyawa shekara bayan shekara.
13/03/2026
Breaking News: Sanatoci 9 Sun Sauya Sheƙa Zuwa Jam’iyyar ADC
Sanatoci guda tara daga jam’iyyun PDP, LP da APGA sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Majalisar Dattawa.
Sanatocin sun haɗa da:
Daga LP:
• Victor Umeh
• Tony Nwoye
• Ireti Kingibe
Daga PDP:
• Aminu Waziri Tambuwal
• Binos Yaroe
• Lawal Adamu Usman
• Mohammed Ogoshi Onawo
• Augustine Akobundu
Sai kuma:
• Enyinnaya Abaribe daga All Progressives Grand Alliance (APGA) wanda shi ma ya sauya sheƙa zuwa ADC.
Sai dai Majalisar Dattawa ta bai wa Sanata Abaribe wa’adin mako guda ya sake nazarin sauya sheƙarsa, domin hujjar da ya bayar cewa an kore shi daga jam’iyyar APGA ba ta dace da kundin tsarin mulki ba
12/03/2026
Yanzu ne lokaci mafi daɗi ka zama gwamna a Najeriya domin Tinubu na basu Bilyoyi kuɗi don rabawa — Akpabio ya yabawa Tinubu
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce a halin yanzu gwamnoni a Najeriya suna cikin wani lokaci mai matuƙar anfani idan aka kwatanta da shekarun baya.
Akpabio ya bayyana cewa a zamanin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuɗin da jihohi ke rabawa daga gwamnatin tarayya ya ƙaru sosai.
A cewarsa, a yanzu gwamnoni na rabon kusan Naira tiriliyan 1.9 zuwa tiriliyan 2.7, wanda ya fi abin da ake samu a gwamnatocin baya nesa ba kusa ba.
Ya ce da a ce shi ma gwamna ne a wannan lokaci, da ya fi jin daɗin mulki saboda yadda kudaden shiga na jihohi s**a ƙaru sak**akon sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta yi.
Akpabio ya ƙara da cewa yawancin gwamnoni ma na cewa abin da suke karɓa yanzu ya kai kusan sau huɗu na abin da ake samu a baya.
Tambaya yanzu ita ce: Shin karin kuɗin da jihohi ke samu zai haifar da sauƙin rayuwa ga talakawa kuwa?
11/03/2026
Babu maganar sulhu tsakanin mu da Amurka da Isra'ila, Inji Kwamandan sojin Iran, k**ar yadda jaridar Iran Times ta Rawaito.