Hon Isa Ali Pantami Fans

Hon Isa Ali Pantami Fans

Share

United Nigeria is our goal.

21/11/2025

KHUƊUBAR JUMA'A DAGA MASALLACIN JIBWIS TUDUN-WADA DANKADAI KANO STATE

TARE DA SHEIKH ABUBAKAR MUHAMMAD TUDUN-WADA

MAI TAKEN
"KAIDIN KAFIRAI DA MAKIRCIN SU BA SABON ABU BANE GURIN MASU IMANI"

Photos from Hon Isa Ali Pantami Fans's post 03/09/2025

DA DUMI-DUMI: Professor Isa Ali Pantami Ya Bai wa Kungiyar Musulunci Ta "Joint Aid Group" Kyautar Mota Domin Tallafawa Ayyukan Addini

Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami CON, ta hannun gidauniyarsa ta Al-Waalidayn Charitable Foundation da ke Gombe, ya bayar da kyautar mota ga kungiyar musulunci ta Joint Aid Group domin tallafa wa ayyukansu na hidima ga al’umma.

An gudanar da bikin mika kyautar ne a harabar cibiyar Al-Waalidayn, karkashin jagorancin Alhaji Ahmadu Abubakar Walama (Sarkin Malaman Gombe), tare da halartar manyan wakilai irin su Arch. Dahiru Saidu da Dr. Umar Dokaji da wasu jiga-jigan malaman addini da shugabanni.

A jawabinsa yayin karɓar motar, Shugaban Joint Aid Group, Malam Umar Ya’u, ya bayyana matuƙar farin ciki da godiya ga Farfesa Pantami bisa wannan taimako da kuma gudummawar da ya dade yana bayarwa wajen ci gaban kungiyar da al’umma baki ɗaya. Ya ce wannan kyauta tana ƙara nuna yadda Farfesa ke ƙaunar ci gaban Musulunci da al’ummarsa.

Ya kuma ce motar za ta sauƙaƙa musu aiki, musamman wajen gudanar da ayyukan jinƙai da gaggawa ga mabuƙata a sassa daban-daban na jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Wannan aiki yana ɗaya daga cikin abubuwan da ke nuna dagewar Farfesa Pantami wajen tallafawa ayyukan addini da na ci gaban al’umma, wanda ke zama sadaka mai dorewa (Sadaqah Jariyah) gareshi da iyayensa.

30/08/2025

Shin Idan Professor Isa Ali Pantami A Minta Zai Tsaya Takarar Gomnan A Jihar Gombe Zaka Zabe Shi ?

29/08/2025

DA DUMI-DUMI: Professor Isa Ali Pantami Ya Biyawa Ɗaliban Jami'ar BUK Ƴan Asalin Jihar Gombe Kuɗin Rajista

Daga Muhammad Kwairi Waziri

A makon da ya gabata, Farfesa Isa Ali Pantami, CON (Majidadin Daular Usmaniyya), ya nuna halin jin ƙai da jajircewarsa wajen tallafa wa harkar ilimi, inda ya biya kuɗin rajista na ɗaliban Jihar Gombe dake karatu a Jami’ar Bayero Kano (BUK).

Bayan da ya ga wani matashi ya wallafa matsalolin da ɗaliban ke fuskanta dangane da biyan kuɗin rajista a dandalin X (Twitter), Pantami ya gaggauta amsa kiran tare da ɗaukar nauyin kuɗin rajistar gaba ɗaya.

Wannan mataki ya zo ne a matsayin ci gaba daga irin tallafin da Farfesa Pantami ya saba bayarwa, kasancewar a baya ma ya biya kuɗin rajista ga ɗaliban Jami’ar Gombe (GSU).

Shugaban ƙungiyar ɗaliban Gombe a BUK (BUK-GOSSA), Muhammad Al Amin Abdulkadir, ya tabbatar da biyan kuɗaɗen a shafinsa na Facebook, yana mai yabawa wannan gagarumin taimako da ya sauƙaƙa wa iyaye da ɗalibai.



11/08/2025

Professor Isa Ali Pantami Yayi Abinda Babu Wanda Yayi Kalan Sa Lokacin Yana Minista, Kuma Ya Kare Malamai Da Addinin Musulunci

Muhammad Buhari Dalhatu Allah ya mana jagora

Photos from Hon Isa Ali Pantami Fans's post 08/08/2025

Yadda Pantami Ya Sauya Noma a Gombe Ta Hanyar Fasaha

Lokacin da Professor Isa Ali Pantami ya kawo shirin National Adopted Village for Smart Agriculture (NAVSA) zuwa Gombe, ya canja yadda mutane da dama suke kallon noma.

Maimaikon yin noma da tsohuwar hanya kaɗai, ya kawo tsarin da fasaha ke taimaka wa manoma su yi aiki cikin sauri, su samu riba mai yawa kuma su rage asara. An bai wa manoma wayoyin salula masu ƙwaƙwalwa, damar amfani da intanet, kuɗin fara aiki, da kuma horo kan yadda za su sayar da amfanin gona da kuma yadda za su kula da gonakinsu yadda ya dace.

Haka kuma, an yi musu rajista a wani kundin bayanan “Know Your Farmer” wato KYF a taƙaice, domin gwamnati da masu saye su iya tuntuɓarsu kai tsaye. Wasu daga cikin manoman sun koyi sababbin dabarun kasuwanci da s**a ba su damar ci gaba da saka jari da faɗaɗa harkokinsu a kowace shekara.

Pantami ya bayyana cewa ƙananan ƙasashe kamar Netherlands suna samun kuɗi mai yawan gaske daga noma ne saboda suna amfani da dabaru na zamani da fasaha. Ya yi imanin cewa Gombe ma za ta iya yin haka—kuma ya fara nuna hakan tun yana Minista a Abuja.

Baya ga noma, ya kuma kawo horon fasahar sadarwa, cibiyoyin fasaha, da shirye-shiryen tallafa wa matasa da mata a sassa daban-daban na jihar Gombe, ta yadda hakan ya ba su ƙarin hanyoyin samun abin dogaro da kai.

Yanzu da ake tattauna batun shugabancin Gombe a shekarar 2027, tambayar da mutane da dama ke yi ita ce: Wanda ya iya kawo waɗannan ayyukan cigaba daga Abuja, me zai hana ya yi fiye da haka idan ya zama Gwamna anan gida Gombe?

Ga waɗanda s**a shaida aikinsa, amsar mai sauƙi ce—Gombe za ta ga manyan canje-canje da sauye-sauye a fannonin noma, ilimi, lafiya, da ma yadda ake gudanar da mulki gaba ɗayansa.

Photos from Hon Isa Ali Pantami Fans's post 22/07/2025

Jagororin Hukumin Gwamnatin Tarayya Sun Kaiwa Professor Isa Ali Pantami Ta’aziyyar Rasuwar Shugaba Buhari

Wasu daga cikin manyan shugabannin hukumomin Gwamnatin Tarayya da Professor Isa Ali Ibrahim Pantami ya tallafawa samun mukamai, sun jagoranci ziyarar ta’aziyya zuwa gare shi, biyo bayan rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a asibiti da ke London a ranar 13 ga Yuli, 2025.

Ziyarar ta gudana ne ƙarƙashin jagorancin Alhaji Ishaq Ali Kalshingi, inda wakilai daga hukumomi da dama s**a halarta, ciki har da: NCC, GBB, NIMC, NITDA, NFIU, POLICE, NEDC, CBN, da wasu.

A yayin karɓar ta’aziyyar, Prof. Pantami ya bayyana wasu daga cikin kyawawan halayen Marigayi Baba Buhari, ciki har da rikon gaskiya, amana, karamci da girmama na gaba – halaye da ya ce sun cancanci a yi koyi da su.

Ya kuma yi kira da a ci gaba da yi wa Marigayi Shugaba Buhari addu’a, tare da rokon Allah ya gafarta masa, ya sanya shi cikin rahama da Aljanna Firdausi. Ya kuma roki gafara da rahama ga dukkan iyaye da malamai da s**a rigamu.

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Photos from Hon Isa Ali Pantami Fans's post 21/07/2025

Professor Isa Ali Pantami Ya Ziyarci Garin Nguru Dake Jihar Yobe Domin Gaisuwar Ta'aziyyar Rasuwar Mahaifin Abokin Sa

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Tsohon Ministan Sadarwa kuma malamin addini na duniya, Farfesa Isa Ali Pantami, ya kai ziyarar ban girma da ta’aziyya a garin Nguru, jihar Yobe, a wata ziyara da ke cike da alheri da girmamawa.

Daya daga cikin muhimman abubuwan ziyarar shi ne dubiya da gaisuwa da ya kai wa sirikinsa, Alhaji Abubakar Salihu Bakabe. Farfesa Pantami ya yi masa addu’ar samun ƙarin lafiya.

Haka kuma, Farfesan ya kai ziyarar ta’aziyya ga likita kuma abokin sa, Dr. Ukasha Ibrahim, shugaban Asibitin Tarayya Nguru (FMC Nguru), bisa rasuwar mahaifinsa.

A yayin ziyarar, Farfesa Pantami ya yi wa iyalan mamacin nasiha tare da addu’ar Allah ya jikansa da rahama, ya ba iyalai haƙuri da juriya.

Ziyarar ta jawo ɗumbin al’umma da ’yan uwa s**a taru, inda s**a bayyana farin cikinsu da godiya bisa wannan ziyara ta girmamawa da goyon baya daga Farfesan. Ana kallon wannan ziyarar a matsayin abin koyi da kara karfafa haɗin kai a tsakanin shugabanni da al’umma.

Photos from Hon Isa Ali Pantami Fans's post 20/07/2025

Allah Ne Kaɗai Ya San Irin Alherin Da Shiekh Pantami Ya Yiwa Ƴan Nigeria, Inji Farfesa Yusuf Usman

Daga Muhammad Kwairi Waziri

A wata hira da aka yi da shi, tsohon shugaban Hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf, ya bayyana godiyarsa da yabonsa ga Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, bisa irin kyakkyawan taimako da goyon bayan da ya bai wa al’umma da kasa baki ɗaya.

A cewarsa, tun lokacin da Farfesa Pantami yake shugaban Hukumar NITDA, yana da halin kaiwa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wa’azi da shawarwari na gari, inda yake isar da bukatun al’umma da abubuwan da zai amfani jama’a ba tare da wata manufa ta kai kanka ba.

Ya ƙara da cewa akwai wani lokaci da aka hana shi ganawa da shugaban ƙasa, amma Farfesa Pantami ne ya shiga tsakani har shugaban ƙasa ya kira shi da kansa, abinda ya nuna irin matsayinsa wajen kare mutuncin mutane da taimakonsu a boye.

Farfesa Usman Yusuf ya ƙare da cewa, “Allah ne kaɗai yasan yawan alherin da Farfesa Pantami ya yi wa ‘yan Najeriya. Irin jajircewarsa da gaskiyarsa abin yabo ne. Allah ya saka masa da alheri.”

19/07/2025

MAGANA ZARAR BUNU!

Mun sha jin kalaman yabo da rantsuwa daga bakin Nafi’u Scorpion, yana cewa: “Duk ƴan takarar gwamna a jihar Gombe babu wanda ya kai Professor Isa Ali Pantami ".

Mun sha ganin bidiyo da rubuce-rubucensa yana tsayawa tsayin daka kan cewa shi kaɗai Malam ne ya cancanta. Yana rantsuwa yana cewa Farfesa ya fi kowa gaskiya, ilimi, tsoron Allah da cancanta.

Amma yau, saboda an siya masa waya, ya dawo yana yi wa mutane rashin kunya, yana cin mutunci da wulakanta waɗanda s**a fi shi ilimi, mutunci da daraja. A yau, mutum Nafi’u ya sauya kalamansa, yana zagin wanda a jiya ya ya taimake shi.

A baya ya kira mai gidan sa Eng Aliyu Muhammad Combat, da "Dan takarar Facebook" wanda ba dan Gombe ba ne, kai ya kai ga ya kalubalanci mutane Gombe su fadi unguwarsu domin ya tabbatar ba su da tushe a jihar Gombe ko goyon baya.

Ya manta da Muhammad Buhari Dalhatu wanda ya masa riga, kuma ɗaya daga cikin makusantan Malam, wanda ya ci masa mutunci a fili. Shin me wannan yake nufi?

Me yasa mutum zai iya rufe idon sa ya ci mutuncin wadanda s**a kyautata masa?

Muna nan muna da shedu da maganganu da bidiyo da rubuce-rubuce akan Nafi’u Scorpion. Idan bai gyara ba, zamu nitsar da shi da gaskiya, mu bayyana wa duniya hakikanin waye shi.

Malam baya taɓa yarda da mutane masu ƙarya, butulci, cin amana, da sauran su, duk waɗanda kuka ga suna tare da Farfesa Isa Ali Pantami a baya yanzu basa tare to ku bincika akwai cin amana ko rashin gaskiya tattare da shi.

Amma muna nan a matsayin mu na masu kare mutum mai mutunci da ilimin addinin musulinci wato Farfesa Isa Ali.

Kuma ga wata magana da Nafi’u ya furta da bakinsa da kan shi:
“Farfesa Isa Ali Pantami ne ya ɗauki nauyin mai gidan sa Aliyu Combat tun daga admission har ya kammala karatu, kuma Farfesa ne ya sama wa matar sa aikin gomnati"

Ina jiran raddin Nafi’u Scorpion, idan har yana da karfin hali da gaskiya, sai ya fito da hujja akan abin da ya fadi.

Idan ba haka ba, al’ummar Gombe su gane cewa wannan mutum ba abin dogaro ba ne, mutumin da yake wulakanta wanda ya gina rayuwarsa, don a ba shi kofi guda na ruwa.

19/07/2025

Professor Isa Ali Pantami Ne Ya Ɗauki Nauyin Karatun Eng Aliyu Muhammad Combat, Tun Daga Shiga Jami'a Har Ya Gama Inji, Nafiu Othman Scorpeey

Want your business to be the top-listed Government Service in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address


Area 3 Garki
Abuja
900243