25/05/2026
Subhaanallah 😢
'Yan Sandan jihar Katsina sun Chafke Masu Garkuwa Da Mutane Domin Neman Kudin Fansa, A Ciki Hadda Wani Nura Aliyu Garwa Wanda SSA on Community Development na Goman jihar Katsina Mln Dikko Umar Radda, Wanda Ya Ajiye Muqamin shi bada dadewa ba domin yayi takara Kamar yadda Dokar zabe ta tanadar da duk Wanda keda Muqamin Siyasa Idan zaiyi takara to zai ajiye Muqamin sa.
Wannan Nura Ance shine Jagoran kungiyar Tasu, kuma maƙwabcine ga yaron da aka sace din mai shekaru takwas (8) a cikin birnin Katsina wanda akayi ta bada cigiyar shi.
Masu garkuwar sun nemi kuÉ—in fansa har Naira miliyan 50, amma an biya Naira miliyan 17 kafin a sako yaron.
Allah Ya Cigaba da tona Muku Asiri!!!..
21/05/2026
Fallen Biyu Ta Tabbata...
12/05/2026
Katsina Ta Fara Duba Yiwuwar Samar Da Titin Jirgin Kasa Na Cikin Gari
Gwamnatin Jihar Katsina ta fara duba yiwuwar samar da titin jirgin kasa na cikin gari domin inganta harkokin sufuri da bunkasa ababen more rayuwa na zamani a fadin jihar.
A wani mataki na cimma wannan buri, gwamnatin ta kafa kwamitin fasaha da zai nazarci kudirin samar da tsarin jirgin kasa na cikin gari (Light Rail), tare da tantance yadda za a aiwatar da aikin.
Kwamitin wanda Kwamishinan Ayyuka na Jihar ke jagoranta, ya hada wakilai daga muhimman ma’aikatu da hukumomin gwamnati da s**a hada da Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsare, Ofishin Sakataren Gwamnati (SGS), Hukumar Tsara Birane, KTDMB, KSTA, da kuma ma’aikatun Filaye, Muhalli, Ayyuka da Gidaje.
Bayanai daga gwamnatin jihar sun nuna cewa an dorawa kwamitin alhakin nazarin yiwuwar aikin ta fuskar fasaha da kudi, tare da duba yadda shirin ya dace da Kundin Tsare-tsaren Cigaban Jihar Katsina na shekarar 2025 zuwa 2040.
Haka kuma, kwamitin zai gabatar wa gwamnati shawarwari kan anfani da muhimmancin aikin wajen habaka tattalin arziki da kuma rage matsalolin sufuri a jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa wannan yunkuri na daga cikin manufofin Gwamna Dikko Umaru Radda na samar da ingantaccen tsarin sufuri, hada yankuna da kuma kara bunkasa ci gaban jihar ta hanyar samar da manyan ababen more rayuwa na zamani.
11/05/2026
A cikin 'yan sa'o'i masu zuwa, fagen siyasar Jihar Katsina zai cika da abubuwan al'ajabi.
05/05/2026
Dikko Radda Gwamna Radda... 💞
05/05/2026
kuyita Yan tsine tsinenku Dikko Ta aikinsa yake.
Nanfa Makarantar Secondary CE a Radda Ba Kasar turai bace ko Abuja
kauyen nanne Radda ta jahar katsina domin Amfanin 'Ya'yan Talakawa
26/11/2025
Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Auwal Haruna Dashe Dengi, Umar Idrs
26/11/2025
Big shout out to my newest top fans! 💎 Comrd Imrana Buhari Usman
Drop a comment to welcome them to our community,