Tarihin Magabata

Tarihin Magabata

Share

An ƙirkiri wannan shafi na Arewa Tarihi domin kawo maku tarihin magabata na ciki da wajen Nijeriya, domin ilmantarwa, nishaɗantarwa, dakuma faɗakarwa.

11/04/2026

Zaman sulhun da akeyi a Pakistan alamu suna nuna cewa sabuwar yaudara ce Amurka ta sake shiryawa, domin dakarun juyin juya hali na Iran sun hango jiragen ruwan yaki na Amurka sun taso daga tashar ruwan Fujairah dake Daular Larabawa sun nufi mashigar ruwan Hormuz.

Nan take dakarun Iran s**a sanar da wakilan Iran dake tattaunawa akan su sanar da Pakistan domin zasu tarwatsa su idan s**a matso kusa da mashigar ruwan.

13/02/2026

Yadda Babangida Su Kayi Da Dimka

Sunan Janar Ibrahim Babangida ya fara fitowa a duniya, tun a ranar 13 Ga Fabrairu, 1976, ranar da abokin sa Kanar Bukar S**a Dimka ya kashe Shugaban Kasa na mulkin soja a lokacin, Janar Murtala Ramat Muhammad wajen karfe 8:30 na safiyar ranar.

Bayan da Dimka ya kashe Murtala, sai ya zarce gidan rediyon tarayya da ke Lagos, in da ya fara yin sanarwa. Sai dai kuma ya na cikin yi wa ‘yan Najeriya jawabin ne, sai Janar dan Danjuma ya umarci Babangida yaje gidan Radiyo ya kamo Dimka ko ta halin ka'ka. Babangida ya darkaki gidan radiyon ya na mai jagorantar rundunar sojoji da motocin sulke da aka tura don ta murkushe Dimka.

IBB ya shiga gidan Rediyon ne domin ya shawo kan Dimka da ya yi watsi da yunkurinsa na kwace mulki. Maimakon IBB ya yi amfani da Karfi sojoji k**ar yadda aka bashi umarni sai ya zabi hanyar lallashi.

Juyin mulkin ya ci tura," k**ar yadda ya shaida wa Dimka. "Dole ka mika wuya." Sai Dimka ya yi barazanar zai harbe shi, sai IBB yayi murmushi ya shaida wa Dimka kashe ni, in ka kashe ni nasan matata da ‘ya’yana ba za su sha wahala a karkashin kulawar ka ba. Sai Dimka zuciyarsa ta karaya kuma ya nemi a yi masa afuwa idan an kafa sabuwar gwamnati, in da yake cewa Babangida, zai taka muhimmiyar rawa.

IBB ya fita da nufin zuwa neman izinin tattauna batun neman Sulhu daga Dimka. IBB ya koma wurin Danjuma wanda ya fusata da wannan bukata da ya kawo. Danjuma Ya dakawa IBB tsawa da cewa, “Ban nemi kaje don sulhu ba! a lokacin da IBB ya dawo gidan rediyon Najeriya cikin Sauri Kafin ya Karasa Dimka ya tsere.

Daga baya an k**a Dimka da Taimakon wata karuwa a gabashin Najeriya a lokacin da yake kokarin tserewa zuwa Kamaru. A ranar 15 ga watan Mayu 1976, aka Harbe shi a bainar jama'a saboda laifin cin amanar kasa.

✍️ Muhammad Cisse

20/01/2026
20/01/2026

Wannan bidiyon yana tona asirin yadda Patrice Emery Lumumba, Firayim Ministan Congo na farko, ya zama barazana ga ƙasashen waje, da kuma yadda ƙasarsa kanta ta juya masa baya.
Ballewar yankuna, juyin mulki, cin amana, tsoma bakin ƙasashen waje duk sun haɗu s**a mayar da filin samun yanci ya koma filin yaƙi da Mubarak da jini.

15/01/2026

Yau shekaru 60 da rasuwar Tafawa Ɓalewa da Ahmadu Bello Sardauna

A rana irin ta yau a 1966 ne aka kashe Firaiministan Najeriya na farko, Tafawa Ɓalewa da Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello da wasu jiga-jigan ƴansiyasa da sojoji a yunƙurin sojoji na juyin mulki.

Tarihin Magabata

15/01/2026

Inyamuri Chukwuma Nzeugwu shine wanda ya halaka Ahmadu Sardauna a rana irin ta yau 15 ga watan Janairu 1966...

Sardauna ya amince da Chukwuma ya bashi amana, amma hakan bai hanashi cin amana ya halaka Sardauna ba...

Tarihin Magabata

04/01/2026

Yau Shekaru 42 Da Kashe Birgediya Muhammad Bako. An Aikeshi Ya Kamo Shugaban Kasa Shehu Aliyu Usman Shagari A Yunkurin Ya Rasa Ransa.

Brigadier Ibrahim Bako Ya Mutu A Juyin Mulki Na Disamba 1983.

Soja Daya Tak Daya Rasa Ransa A Rana Mai Kamar Ta Yau 31 Disamba 1983 A Lokacin Juyin Mulkin Soja A Najeriya.

Birgediya Ibrahim Bako ya kasance babban jami'i a cikin sojojin Najeriya da s**a taka babbar rawa a juyin Mulkin sojoji guda 2 da akayi a Najeriya, da juyin mulkin da akayi a ranar 29 ga watan Yuli 1966 (counter), da kuma juyin mulkin ranar 31 ga watan Disamba 1983, juyin mulkin 1983 ya hambarar da gwamnatin dimokaradiyya ta Shehu Shagari.

An kashe Bako ne a lokacin da yake yunkurin k**a shugaban kasa Shehu Shagari a juyin mulkin.

Birgediya Ibrahim Bako (A lokacin daraktan tsangayar soji a kwamanda na rundunar soji da kwalejin ma’aikata, Jaji) kuma mukaddashin GOC 1 Mechanized Division, Kaduna.

Sojojin da s**a shirya juyin mulkin sun tura Birgediya Ibrahim yaje ya kamo shugaban kasa Shehu Shagari salin-alin ba tare da zubar da jini ba, domin kasancewar mahaifin Ibrahim Bako amini ne ga Shugaban Kasa Alhaji Shehu Aliyu Usman Shagari, ana fatan wannan alaƙar za ta tabbatar da mika mulki cikin lumana.

Bako dai bai san cewa an fallasa shirin juyin mulkin ga shugaba Shagari ba! wanda yasa masu gadin sa na cikin shirin kota kwana.

Bayan ya isa gidan shugaban kasa (a cikin kayan da ba na soja ba), kuma ba tare da tawagarsa na dauke da wasu isassun mak**ai domin k**a shugaban ba. An harbe Bako ne a lokacin da yake zaune a gefen fasinja na wata babbar mota kirar Unimog a wata arangama da aka yi tsakanin sojojin da ke tare da Bako da kuma sojojin Brigade of Guards a karkashin jagorancin Captain Augustine Anyogo.

Motar Unimog da aka kashe Bako a ciki ta na gidan baje kolin kayan tarihi na sojojin Najeriya da ke Zariya Najeriya.

Bako ne kawai wanda ya mutu a juyin mulkin 1983. Majalisar Koli ta Soja (SMC) ta yi shiru na minti ɗaya a lokacin taronta na farko a ranar 3 ga Janairu, 1984.

03/01/2026

DAREN 22 GA AFRILU, 1990 DAREN BAN TSORO: Lokacin da Aminci Ya Ƙone a Cikin Wuta
Bayanin hoto. Hoto ya nuna Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida, a tsakiya, tare da Janar Sani Abacha a dama da Janar Abba Abdulkadir a hagu.

Daren 22 ga Afrilu, 1990 ya kasance ɗaya daga cikin mafi ban tsoro da tayar da hankali a tarihin sojan Najeriya bayan samun ƴancin kai. A cikin tsakar dare, wata ƙungiyar masu shirya juyin mulki ta ƙaddamar da mummunan yunƙuri, mai tsari sosai, domin kifar da gwamnatin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Harbin bindiga ya karaɗe wurare masu muhimmanci a Lagos, sanarwar rediyo ta bayyana wai an sauya gwamnati, yayin da ruɗani ya k**a ƙasa gaba ɗaya, ƴan Najeriya s**a farka da sautin rikici da tashin hankali. A tsakiyar rikicin kuwa, lafiyar Shugaban Ƙasa na mulkin Soja da kansa ce ta zama babban abin damuwa. Yunƙurin juyin mulkin ya kasance mai ƙarfin hali da rashin tausayi, inda ya kai hari ba kawai kan muhimman sansanonin soja ba, har ma da cibiyar ikon siyasa.

A cikin rikice-rikicen artabu, Janar Babangida ya fuskanci babban rashi na ƙashin kai, sak**akon mutuwar Aide-de-Camp ɗinsa, Laftanar Kanal UK Bello, wanda aka kashe yayin da yake cikin aikinsa yayin wutar yaƙi. Mutuwarsa ta nuna tsananin halin da ake ciki da kuma ainihin barazanar da ke fuskantar gwamnatin.

A cikin waɗannan sa’o’i masu matuƙar muhimmanci ne Janar Sani Abacha ya fito a matsayin ginshiƙin kare gwamnati. Cikin natsuwa, ƙuduri da rashin ja da baya, Abacha ya karɓi ragamar jagorantar sojojin da s**a kasance masu biyayya, tare da daƙile ci-gaban masu shirya juyin mulkin.

Ayyukansa sun taimaka wajen kare kujerar mulki da tabbatar da tsaron Babban Kwamandan Runduna a wani lokaci da daidaiton al’amura zai iya karkata zuwa wani ɓangare. Da asubahin gari, an murƙushe yunƙurin juyin mulkin gaba ɗaya, kuma ikon gwamnatin Babangida ya dawo yadda yake.

Bayan ceton gwamnati, abubuwan da s**a faru a wannan daren sun ƙulla ƙaƙƙarfan alaƙa tsakanin Babangida da Abacha. Amincin da Abacha ya nuna a ƙarƙashin wuta ya bar gagarumar alama a zuciyar Shugaban Mulki. A matsayin girmamawa ga rawar da ya taka, jarumtaka da jajircewarsa, daga baya Babangida ya ɗaga Sani Abacha zuwa cikakken mukamin Janar mai taurari huɗu. Wannan ɗaukaka ta kasance tarihi kuma ba ta taɓa faruwa ba a al’adar sojan Najeriya.

A karo na farko a tarihin ƙasar, wani jami’i mai aiki ya riƙe cikakken muƙamin Janar alhali kuma wani jami’i ke ci-gaba da zama Shugaban Mulki. Wannan shawara ba wai nuna godiya ta ƙashin kai kaɗai ba ce, har ila yau alamar babban amana, inda ta ɗaga Abacha zuwa matsayi na musamman mai matuƙar tasiri a tsarin rundunar soji.

Saboda haka, daren 22 ga Afrilu, 1990 ya mallaki wuri na musamman a tarihin Najeriya. Dare ne da aka zubar da jini da yawan asara, wanda ya haɗa da sadaukarwar jami’ai irin su Laftanar Kanal UK Bello.

Haka kuma dare ne da ya sake fasalta dangantakar iko a cikin rundunar soji, ya ƙarfafa ƙawance a matakin koli, tare da shimfiɗa turbar abubuwan da s**a biyo baya waɗanda s**a shafi ƙasar ƙwarai. An gwada aminci a cikin wuta, kuma bayan haka, tarihi ya ɗauki sabon salo mai muhimmanci.

02/01/2026

Lt. Col. Muhammad Abu Ali Rahimahullah

Dan sarki dan gwamna mahaifinsa ya zabi ya Dora shi Akan hanyar bautawa kasa da kishin kasa

Idan Alfarma Ake magana ta canjin wurin Aiki babu wani soja daya darashi ita

Yayi rayuwa mai wahala kwana a cikin rami gaba da gaba da makiya kasa har numfashinsa na karshe

Wallahi zai wahala ace Muhammad Abu Ali ya malakki milyan 100 a asusunshi a yayin da wadanda Ake tsare rayukansu suke gina diyan su da kudin Al’umma

Irin wadannan dalilai ne yake kashe karsahin kishi a aikin soja

Allah ya gafartawa Muhammad Abu Ali Da mahaifinsa da magabatan mu Ameen.

galant Army.

02/01/2026

Muhammad Abu Ali Rahimahullah

Dan sarki dan gwamna mahaifinsa ya zabi ya Dora shi Akan hanyar bautawa kasa da kishin kasa

Idan Alfarma Ake magana ta canjin wurin Aiki babu wani soja daya darashi ita

Yayi rayuwa mai wahala kwana a cikin rami gaba da gaba da makiya kasa har numfashinsa na karshe

Wallahi zai wahala ace Muhammad Abu Ali ya malakki milyan 100 a asusunshi a yayin da wadanda Ake tsare rayukansu suke gina diyan su da kudin Al’umma

Irin wadannan dalilai ne yake kashe karsahin kishi a aikin soja

Allah ya gafartawa Muhammad Abu Ali Da mahaifinsa da magabatan mu Ameen🙏

galant Army.

31/12/2025

Na san zaku gane General buhari a hoton nan amma na gefen shi kam sai gwarzo
🔻🔻

Daga Salmanul Paris

19/04/2025

TAƘAITACCEN TARIHIN SIR AHMADU BELLO SARDAUNA

An haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, a ranar 12 ga watan Yuni na 1910 a garin Rabbar na jihar Sokoto dake Arewacin Najeriya.

Kakansa shi ne sarkin Musulmi Bello, wanda na daya daga cikin wadanda s**a kafa daular Sokoto, kuma dane ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo.

Ahmadu Bello ya fara makaranta a garin Sokoto, sannan ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina.

Kafin daga bisani Sultan ya nada shi malami a makarantar Middle School ta Sokoto.

A shekarar 1938 aka nada shi Sardaunan Sokoto bayan da ya gaza a yunkurin da yayi na zamowa Sultan, wato Sarkin Musulmi.

Ya kuma halarci kasar Ingila domin yin karantu kan harkokin mulki a shekarar 1948.

Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda har aka zabe shi ya zamo mamba a majalisar dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama ministan ayyuka da raya kasa.

Ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa daga shekarar 1954 zuwa 1966.

Sannan ya jagoranci jam'iyyar NPC ta lashe kujeru da dama a zaben da aka gudanar bayan samun 'yancin kai.

Bayan kammala zabe, ya zabi ya ci gaba da kasancewa Firimiya, inda ya nada Abubakar Tafawa Balewa ya zamo Fira Minista.

Ya taka rawa sosai wajen hada kan yankin Arewacin kasar wanda keda kabilu mabiya addini daban-daban, da kuma aiwatar da ayyuka na ci gaban kasa.

An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji 'yan kabilar Ibo s**a jagoranta.

ALLAHU YAJIƘAN MAZAN JIYA.

✍️ Tarihin Magabata

Want your business to be the top-listed Government Service in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Address


Abuja