13/06/2026
13 JUNE 2026.
ƘARYA KA KE YI, KANA DA MAI GIDA KUMA AKWAI WANDA YA GIRME KA A FAGEN SIYASAR JIHAR ZAMFARA.
1994 bayan Mai girma tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja marigayi Genaral Sani Abacha ya karɓe mulki a hannun Ernest Shonekan ya rusa Jam'iyyun siyasar da Mai girma tsohon shugaban ƙasa General Ibrahim Badamasi Babangida ya kafa na NRC da SDP, Abacha ya kafa na sa Jam'iyyun daga baya, inda ya kafa sabbin Jam'iyyu dukkaninsu mallakar Gwamnatin Tarayya ta wannan lokacin.
* UNCP.
* DPN.
* GDM.
A wannan ƙarnin a jihar Zamfara Jagororin waɗannan sabbin Jam'iyyu su ne k**ar haka:
* UNCP - Dattijo Sanata Sa'idu Idris Samaho
* DPN - H.E Malam Yahaya Abdulkareem.
* GDM. Baba Isan mayana da Baba Ummaru Ɗangaladima Birnin Magaji.
Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin Marigayi Abacha ta fi baiwa Jam'iyyar UNCP ƙarfi da muhimmanci a matakin ƙasa, wato a sama, amma a Zamfara Jam'iyyar DPN ta fi ƙarfi, dikkanin Jam'iyyun mallakar Gwamnatin Tarayya ne, a wannan lokacin, fatan Gwamnatin mulkin soja a wannan lokacin shi ne, idan an zo zaɓe al'ummar ƙasa a matakin jihohi, kowa ya shiga Jam'iyyar da ta yi masa, idan an zo matakin zaɓen ɗan takarar kujerar Shugaban Ƙasa, kowa ya marawa Marigayi General Sani Abacha baya a matsayin ɗan takarar kujerar Shugaban Ƙasa na maslaha guda ɗaya tilo.
A wannan lokacin 1994-1996 Mai girma tsohon Shugaban Ƙasa General Abacha baya da ɗan takarar kujerar Gwamna a jihar Zamfara a ƙarƙashin tutar Jam'iyyar DPN face Mai girma Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura a dai-dai lokacin da ka ke maganar ka yi takarar kujerar Majalisa wakilai, da Allah (SWT) bai ƙaddari mutuwar General Abacha ba, da tin wannan lokacin Mai girma Sanata Ahmad Sani Yarima shi ne Gwamnan jihar Zamfara.
* GA MAI GIDANKA A FAGEN SIYASAR JIHAR ZAMFARA.
Dattijo Mai girma Sanata Sa'idu Idris Samaho Talata Mafara, Jagoran Jam'iyyar UNCP a Zamfara a wanchan lokacin shi ne ya tsayar da kai takara a ƙarƙashin tutar Jam'iyyarsa ta UNCP 1996 kuma shi ne Mai gidanka kuma yana nan raya a cikin Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara a wannan lokacin kai waye a Zamfara?
A dai-dai wannan lokacin da ka ke takarar kujerar Majalisar wakilai a ƙarƙashin tutar Jam'iyyar UNCP, Mai girma Sanata Abdul'aziz Yari Abubakar (Marafan Sokoto) yana takarar kujerar ɗan majalisar dokoki a ƙarƙashin tutar Jam'iyyar DPN ta H.E Malam Yahaya Abdulkareem.
Akasin da aka samu Jam'iyyarsa ta DPN ba ta samu damar tsayar da shi a matsayin ɗan takarar ba, shi ne, a lokacin da aka buɗe rijistar ƴan Jam'iyya yana Legos gurin kasuwanci, da yake a wanchan lokacin Doka ta bayar da damar ana iya yi wa wanda baya kusa rijista, saboda haka Malamin rijistar Jam'iyyar DPN Marigayi Abdullahi A.Malik tsohon ma'aikacin First Bank shi ne ya yi wa (Marafan Sokoto) rijista, a gurin yi masa rijistar madadin ya saka masa ainihin shekarunsa na haihuwa, sai ya rage masa shekarunsa.
Amma a wannan lokacin babu ɗan takara mai ƙarfinsa, gudun kada Gwamnatin Tarayya ta ji kunya a ce ɗan takararta a UNCP ya faɗi zaɓe, Sai Gwamnatin mulkin soja a ƙarƙashin Jagorancin Marigayi Abacha daga sama, aka ce shekarun da Mai girma (Marafan Sokoto) ya saka a yayin rijistarsa a Jam'iyyar DPN, sunyi ƙaranci, ba zai iya tsayawa takara ba.
* GA WAƊANDA S**A GIRMEKA A FAGEN SIYASAR JIHAR ZAMFARA.
1. Hon.Sani Galadi: - 1983 ɗan majalisa ne a cikin Gwamnatin Marigayi Shehu Aliyu Shagari, yana nan raye a cikin Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara yanzu haka, ya girme ka a fagen siyasar jihar Zamfara, a lokacin kana ina ne kuma me ka ke yi?
2. Mai girma Sanata Ikira Aliyu Bilbi: - 1993 ya shiga zaɓe kuma ya lashe zaɓen Ɗan Majalisar wakilai ya girme ka a fagen siyasar jihar Zamfara, a wannan lokacin kana ina ne kuma aikin me ka ke yi?
3. Mai girma Sanata Tijjani Yahaya Ƙaura: 1993 yana Chairman na Local Government, a dai-dai wannan lokacin kana ina kuma me ka ke yi ?
4. Hon.Aliyu Lugga.
5. Hon.Aliyu Tukur ES.
6. Hon.Sule Adamu Gummi.
Dikkanin waɗannan Dattawan babu wanda bai gimeka a fagen siyasar jihar Zamfara ba, amma sun yarda da Allah ( SWT),kowannensu yana mutunta Mai girma Sanata Abdul'aziz Yari Abubakar (Marafan Sokoto) ba dan ya girme su a fagen siyasar jihar Zamfara ba, sai dan sun yarda Allah (SWT) shi ne mai ɗaukaka wanda ya so, a lokacin da ya so ba tare da ya yi shawara da kowa ba.
GA TAMBAYA......?
Ka ce ka girmi kowa a fagen siyasar jihar Zamfara, har da Mai girma Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, bari mu tina maka idan ka manta, Sanata Yarima shi ne ya tsayar da kai takara a Jam'iyyar APP a matsayin Chairman na ƙaramar hukumarka ta Maradun, Hon.Muhammad Chado Gora ya kayar da kai zaɓe, Mai girma Sanata Yarima ya baka kujerar Kwamishina, amma ka ce ba mai gidanka ba ne, to shin Kwamishina ne Mai gidan Gwamna, ko kuma Gwamna ne Mai gidan Kwamishina?
Kalamanka na cike da hasada, rashin sanin waye Allah (SWT) da tauhidi, haka zalika kalamanka na k**anceceniya da kalaman nasara, yahudawa da kafiran Makkah a lokcin da suke adawa da Shugabanmu Annabi Muhammad (SAW).
"NARFA'U-DARAJATI-MAN'NA'SHA'U" INJI ALLAH (SWT).
1. Allah (SWT) yana fitar da mai kyau a marar kyau.
2. Allah (SWT) yana fitar da marar kyau a cikin mai kyau.
3. Allah (SWT) ya na arzitta wanda ya so, a lokacin da ya so, ba tare da kallon nasaba ko ilmin ɗan Adam ba.
4. Allah (SWT) sai ya ƙaddari mutum yana yawon kiwon shanu a daji, amma ya haifi Shugaban ƙasa.
5. Allah (SWT) ya sa ka haifi ɗa ya fi ka arziki.
Waɗannan kalamai na ka, na cike da rashin sanin Allah (SWT), rashin Dattako da tsabar hasada, irin wannan harshen da ka yi anfani da shi, irinsa ne shaiɗan ya yi anfani da shi gurin yi wa Annabi Adam (ASW) ya hasada, kuma daga wannan lokacin ne, Allah (SWT) ya yi alƙawarin rusa dik wanda ya yi hali irin na shaiɗan. (Alhasadu-adalu).
Kuma ba mu yi mamakin jin hakan daga gurinka ba, dama bama zaton jin kowane irin magana mai ɗanɗanon ilmi, hikima da basira a tare da kai, ma'aikatar ilmi ta ƙasa ita ce ta tabbatar da hakan.
Muna roƙon Allah (SWT) ya cigaba da tsare kima da mutuncin (Marafan Sokoto), Allah (SWT) ya zaunar da jihar Zamfara da Arewacin Nijeriya baki ɗaya lafiya alfarmar Annabi Muhammad (SAW).