27/05/2026
BARKA DA SALLAH DAGA HUKUMAR KWANA KWANA TA JIHAR BAUCHI.
A madadin dukkanin jami'an hukumar kwana-kwana ta jihar Bauchi, shugaban hukumar, Bldr Dauda B Pali MNIOB, Kachallan Pali, yana taya al'ummar musulmin jihar Bauchi murnar bikin sallar layyah wacce ake yi a yanzu haka.
Bldr Pali, yana kira ga al'ummar jiha akan kada su manta ta ɗaukar matakan kariya daga iftila'in gobara a lokacin da suke gudanar da hidimar bikin sallah, musamman kasancewar ita sallar layyah akan yi mu'amala da wuta wajen sarafa nama.
Iyaye mata su tabbatar da sun kashe wuta a duk lokacin da s**a gama amfani da ita, su kuma hana ƙananan yara mu'amala da wuta da sunan gasa nama ko kuma yin tsire.
Masu babbakan kai da ƙafa da kuma fata, su tabbatar da sun kashe wutar sosai a duk lokacin da s**a gama amfani da ita, kasancewar yanzu muna lokacin da ake yawan samun iska mai ƙarfi tana kaɗawa, sakamakon yanayin damuna da muke ciki.
A duk lokacin da ake buƙatar samun hukumar kwana kwana ta jiha, sai a kira ɗaya daga cikin wannan lambobin wayar, 07086463943 ko 09038352982.
Daga ƙarshe, shugaban hukumar yana roƙon Allah da Ya ci gaba da zaunar da jihar Bauchi lafiya da kuma kawo mata arziki mai albarka.
Allah Ya ja zamanin Mai Girma Gomnan Jihar Bauchi, Sen. Bala Abdkulƙadir Mohammed, Ƙauran Daular Uthmaniyya.
Allah Ya ja zamanin Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dr Rilwanu Sulaiman Adamu .
Allah Ya ja zamanin Al'ummar Jihar Bauchi.
26/05/2026
A SPEEDY RECOVERY.
The wife of our Director had undergone a successful caesarean section(CS) yesterday.
Through The Almighty Allah's infinite mercy, both the mother and baby boy were in good healthy condition.
We pray to The Almighty Allah to grant her and all those suffering from any types of illnesses a speedy recovery.
ALLAH YA ƘARA SAUƘI.
A jiya ne iyalin Daraktan mu aka mata aiki inda aka cire jariri.
Allah cikin Ikon Shi, mahaifiyar da jaririn duk suna cikin ƙoshin lafiya.
Muna roƙon Allah da Ya ƙara mata lafiya kuma Ya kawo sauƙi wa dukkan wanda suke fama da rashin lafiya.
25/05/2026
GENERAL FALL-IN.
A general fall-in of all the personnel of The Bauchi State Fire Service was held today at The Headquarters of The BSFS.
The Director of The BSFS, Bldr Dauda B. Pali, MNIOB, addressed the gathering of the gallant firefighters on various issues concerning the BSFS.
Also those that gave their contributions, included The Deputy Director Engineer Jesse M. Zamba, The Operation Officer Abubakar L. Mohammed, The BSFS PRO Mohammed T Bature, The Head of Prevention unit Abdullahi Saleh and The Fire Service Training School Commandant Abubakar B. Bala.
Questions and answers were held, where questions asked by the firefighters, were answered by the appropriate officers.
***********
A yau Litinin, aka gudanar da taron dukkanin jami'an hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi a helkwatarta hukumar.
Shugaban hukumar, Bldr Dauda B. Pali MNIOB ne ya gabatar da jawabi wa taron zaratan jami'an hukumar akan al'amuran da s**a shafi hukumar.
Sauran manyan jami'an hukumar da s**a bada tasu gudunmawar, sun haɗa da mataimakin shugaban hukumar Eng. Jesse M. Zamba, babban jami'in gudanarwa na hukumar Abubakar L. Mohammed, jami'an hulɗa da jama'a na hukumar Mohammed T. Bature, jami'in sashin wayar da kai na hukumar Abdullahi Saleh da kuma kwamandan makarantar horarwa ta hukumar Abubakar B. Bala.
An gudanar da tambayoyi da kuma amsoshi, inda manyan jami'an hukumar s**a amsa tambayoyin da jami'an hukumar s**a yi.
14/05/2026
Shirin "INA MUKA DOSA" wanda gidan rediyon Globe FM Bauchi ta ke gabatar, shirin na yau Alhamis, an gudanar da shi ne da Shugaban Hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi, Bldr Dauda B. Pali.
Shirin an tattauna da shugaban ne akan irin ƙalubalen da jami'an hukumar suke fuskanta a lokacin da suke gudanar da aikin su, musamman da yadda a wasu lokutan s**an fuakanci cin zarafi ko kuma farmaki daga wajen wasu ɓata garin matasa.
Bldr Pali, ƙarin bayani akan irin matakan da hukumar ta fara ɗauka domin maganin masu irin wannan ɗanyen aikin, inda ya bada misali akan hukuncin da kotu ta yi akan matasan da s**a kai wa jami'an hukumar farmaki a Mararraban Liman Katagum, inda aka yanke musu ɗaurin wata ashirin da ɗaya a gidan gyaran hali ko kuma biyan tarar Naira Dubu Ɗari Biyu da Hamsin.
Shugaban hukumar, ya bada shawara wa al'umma jiha akan hanyoyin da s**a kamata su dinga ɗauka wajen yin riga kafin afkuwar gobara.
Masu sauraron shirin da s**a kira waya domin bada tasu gudunmawar, sun yi kira wa jama'a da su dinga bada haɗin kai wa jami'an hukumar a duk lokacin da suke gudanar da aikin su.
12/05/2026
ZIYARAR GODIYA DA NEMAN AGAJI.
A daren ranar Juma'an data wuce ne aka samu iftila'in gobara a kasuwar waya, wacce ta ke cikin kasuwar Muda Lawal.
Duk da kasancewar jami'an hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi sun yi ƙoƙari wajen hana yaɗuwar wutar, an sami asarar dukiya mai yawa da kuma ƙonewar shaguna masu yawa.
Domin nuna farin cikin da irin ƙoƙarin da jami'an hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi s**a yi a lokacin faruwar gobarar, yasa shugabannin ƙungiyar 'yan kasuwar wayar s**a kawo ziyara hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi a yau Talata.
Da yake bayani akan dalilin ziyarar ta su, shugaban ƙungiyar, Mal. Adamu Yahaya mai kifi, ya ce sun ziyarci hukumar ne domin su miƙa godiyar su akan irin rawar ganin da jami'an hukumar s**a taka a lokacin gobarar, Mal. Mai kifi, ya jinjinawa SDFO Muddassir Mohammed wanda shi ne ya jagoranci tawagar jami'an hukumar, akan irin ƙwarancewar da ya nuna a lokacin gobarar.
Shugaban ƙungiyar, ya miƙa roƙon shi akan a tallafawa wanda iftila'in ya shafa.
Da yake maida martani, Shugaban Hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi, Bldr Dauda B. Pali, ya jajentawa 'yan kasuwar akan jarabawar da s**a samu, ya kuma yi alƙawarin hukumar zata isar da roƙon su wajen hukumomin da s**a da ce.
11/05/2026
FAMILIARIZATION VISIT.
Brigadier General SS Shehu, Brigade Commander Of The 33 Artillery Bridge Bauchi alongside some of his principal officers, today Monday, paid a familiarization visit to The Headquarters of The Bauchi State Fire Service.
He was received on arrival by The Director of The Bauchi State Fire Service, Bldr Dauda B. Pali alongside some of the officers of the BSFS.
The aim of the visit according to The Commander, is to familiarize himself with The BSFS being one of the long time partners in progress with The Army and also to strengthen the already established synergy and the good cordial working relationships that existed for a long time between The BSFS and The Nigerian Army.
The Director of The BSFS, Bldr Dauda B. Pali, thanked the August visitor for the visit. A closed door meeting was held between the heads.
ZIYARAR AIKI.
Brigadier General SS Shehu, komandan sojoji masu aiki da manyan makamai dake barikin Shadawanka, a yau Litinin, ya kawo ziyarar aiki hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi.
Shugaban hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi, Bldr Dauda B. Pali, shi ne ya tarbe shi a lokacin da ya iso hedkwatar hukumar.
Dalilin ziyarar, in ji Komandan, shi ne , domin ya ƙara danƙon dangantakar aiki da ta ke tsakanin hukumomin biyu kasancewar akwai kyakkyawar daɗaɗdiyar alaƙar aiki a tsakanin rundunar sojoji da kuma hukumar kwana kwana ta jihar Bauchi.
An gudanar da tattaunawar sirri tsakanin shugabannin biyu.