02/10/2026
DR. YAKUBU ADAMU YA BAYAR DA TALLAFIN ₦200M DA MOTOCIN COASTER 10 GA DALIBAN ATBU
Dr. Yakubu Adamu, Wazirin Giade, ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM), ya bayyana wani tallafi na ₦200 miliyan tare da samar da motocin Coaster guda 10 domin tallafa wa ɗaliban Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), Bauchi.
tallafin yabiyo baya ne a yayin wani taro da ya samu halartar ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara mayar da hankali kan tallafawa ɗalibai da inganta harkokin ilimi a Jihar Bauchi.
Bauchi Social Network.