01/01/2023
MAI GIRMA RECTOR ATAP YA SAMU HALARTAN WAJEN NADIN SARAUTAR MAI GIRMA ALIYU AMINU GARU
************************************
A yau Lahadi 01/01/2023 ne Mai girma rector Atap Dr. Adamu Sa'idu ya samu halartan wajan nadin sarautar mai girma Alh. Aliyu Aminu Garu (Dan takarar dan majalisan tarayya a karkashin tutar jam'iyar PDP). Wanda Mai girma sarkin Bauchi Dr. Rilwanu Sulaiman Adamu ya nada shi a matsayin sarkin alhazan Bauchi.
Muna taya Mai girma Alh Aliyu Aminu Garu murnar samun wannan daukaka. Kuma muna yima Mai girma rector Atap gaisuwan ban gajiya. Allah yasa anyi a sa'a.
