23/11/2025
ABU YA ZO KARSHE: SANATA SHEHU BUBA UMAR YA KAI DAUKI GA MAKARANTAR ISLAMIYYAR DA TA SHAFE SHEKARA 26 BA TA KAMMALA BA.
__________
Mai girma Sanata na Bauchi ta Kudu, Sanata Shehu Buba Umar, ya ɗauki nauyin kammala ginin makarantar Islamiyya da ke Unguwar Yalwan Makaranta, cikin Karamar Hukumar Bauchi, wacce ta shafe shekaru 26 tun daga 1999 ana aiki ba tare da kammalawa ba.
Sanatan ya shiga aikin ne bayan korafe-korafen da al’ummar yankin s**a kai masa, inda s**a bayyana irin dogon jinyar da dalibai da malamai ke yi saboda rashin kammala ginin makarantar.
A halin yanzu, aikin na ci gaba da tafiya cikin sauri, domin tabbatar da cewa yara da matasa za su samu ingantaccen wurin karatun addini cikin girmamawa da kwanciyar hankali.
11/11/2025
YANZU-YANZU: SANATA SHEHU BUBA YA CIKA BURIN WANI MATASHI DA YA DAD'E YANA NEMA
Wani matashi mai suna Mr. Emmanuel Yusuf ɗan asalin ƙauyen Marti da ke cikin Karamar Hukumar Tafawa Balewa ta Jihar Bauchi, ya cika burinsa na samun aikin gwamnati bayan dogon lokaci yana fafutukar neman aiki.
Rahotanni daga ofishin Sanata Shehu Buba Umar sun tabbatar da cewa matashin ya samu aikin sa ne a Federal College of Education (Technical), Yauri – Jihar Kebbi.
Mr. Emmanuel, cikin murna da godiya, ya bayyana cewa ya shafe shekaru da dama yana nema, amma yau Allah Ya cika masa burinsa ta hannun Sanata Shehu Buba Umar, wanda ya tabbatar da cewa ba zai bar matasa da ƙwararru a Bauchi su zauna babu aiki ba.
A cewarsa:
“Na gode wa Allah da kuma Sanata Shehu Buba Umar bisa wannan damar da ya bani. Wannan aiki ya zama sabuwar rayuwa a gare ni da iyalina.”
Al’umma da dama daga yankin Tafawa Balewa sun bayyana farin cikinsu da wannan cigaba, suna cewa hakan ya nuna yadda Sanata Shehu Buba ke taimakawa matasa wajen samun hanyar dogaro da kai.
Our Governor 2027
Sanata SHEHU BUBA UMAR