Press, Deputy Gov. Office

Directions

Press, Deputy Gov. Office Official page of the Deputy Governor's Office Welcome to Muhammad Auwal Jatau page

BAUCHI TA ƘADDAMAR DA DOKAR STARTUP, JATAU YA JADDADA ƘUDURIN GWAMNATI NA ƘARFAFA MATASA TA FUSKAR FASAHA:Mataimakin Gwa...
20/10/2026

BAUCHI TA ƘADDAMAR DA DOKAR STARTUP, JATAU YA JADDADA ƘUDURIN GWAMNATI NA ƘARFAFA MATASA TA FUSKAR FASAHA:

Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Mai Girma Rt. Hon. Auwal Mohammed Jatau, ya wakilci Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed a bikin yaye ɗaliban shirin Cyber Nations da ƙaddamar da Dokar Startup ta Jihar Bauchi.

Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital ta Jihar Bauchi ce ta shirya taron, wanda ke nuna ƙudirin gwamnatin jihar na bunƙasa fasahar dijital da ƙarfafa matasa ta hanyar koyar da su dabaru da ƙwarewar amfani da fasaha.

Haka kuma, ƙaddamar da dokar na da nufin samar da yanayi mai kyau domin sabbin kamfanoni masu tasowa da sauran harkokin kasuwanci da s**a dogara da fasaha su samu damar bunƙasa a Jihar Bauchi.

Rahoto: Muslim Lawal
Mai Bai wa Mataimakin Gwamnan Bauchi Shawara na Musamman kan YaÉ—a Labarai.

May Allah distance you from shame and failure, destroy every evil plan against you and your loved ones, protect you from...
09/10/2026

May Allah distance you from shame and failure, destroy every evil plan against you and your loved ones, protect you from known & unknown enemies.
May Allah (SWT) support you and your family with His Love, Kindness, Mercy, Blessings and Forgiveness...
May you continue to enjoy Allah's Rahma, Ni'ima and protection till Yaumul Kiyama.
JUM@T MUBARAKA!!!

BAUCHI ZATA TA SAMAR DA GWAJIN ULTRASOUND KYAUTA GA MATAGwamnatin Jihar Bauchi za ta samar da na’urorin Ultrasound na za...
06/10/2026

BAUCHI ZATA TA SAMAR DA GWAJIN ULTRASOUND KYAUTA GA MATA

Gwamnatin Jihar Bauchi za ta samar da na’urorin Ultrasound na zamani guda 20 a asibitocin gwamnati 20 da ke fadin jihar, domin inganta kula da lafiyar mata masu juna biyu da rage mace-macen mata da jarirai.

An samar da na’urorin ne tare da tallafin Bankin Duniya (World Bank) ta hanyar shirin IMPACT, inda ake sa ran dubban mata masu juna biyu za su amfana da gwajin Ultrasound kyauta.

Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Muhammad Awwal Jatau, ya bayyana cewa wannan shiri zai taimaka wajen gano matsalolin ciki tun da wuri, tare da inganta samun ingantaccen kiwon lafiya ga mata a fadin jihar.

Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Muhammad Auwal Jatau ya jagoranci tawagar ministoci guda biyu minista...
05/10/2026

Maigirma Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Muhammad Auwal Jatau ya jagoranci tawagar ministoci guda biyu ministan lafiya da ministan kudi daga gidan gwamnatin jihar bayan ganawar su da Maigirma Gwamna zuwa fadar mai martaba sarkin Bauchi daga bisani s**a babban asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya domin bude sabon wajen jinya da wasu kayyayiki na aikin jinya

Happy 68th Birthday Sir🎂
05/10/2026

Happy 68th Birthday Sir🎂

GWAMNONIN AREWA MASO GABAS SUN TARA ₦15.8BN DOMIN KAFA KAMFANIN JIRGIN SAMA NA YANKINKungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas...
03/10/2026

GWAMNONIN AREWA MASO GABAS SUN TARA ₦15.8BN DOMIN KAFA KAMFANIN JIRGIN SAMA NA YANKIN

Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas ta bayyana cewa ta samu gudummawar Naira biliyan 15.8 a matsayin kudin haÉ—in gwiwa domin kafa wani kamfanin jirgin sama na yankin, da nufin inganta zirga-zirgar tattalin arziki tsakanin jihohin yankin.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ne ya bayyana hakan yayin bude taron karo na 13 na Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas, wanda aka gudanar a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Gwamna Zulum ya bayyana kyakkyawan fata cewa za a samu karin kudade daga sauran jihohin yankin kafin karshen shekara, domin a samu damar fara aikin kafa kamfanin jirgin saman.

Ya yi kira ga dukkan jihohin da ke cikin kungiyar da su hada kai domin ganin an cimma nasarar kafa kamfanin jirgin saman, yana mai cewa inganta zirga-zirgar tattalin arziki na daga cikin muhimman ginshikan ci gaban Arewa maso Gabas.

Gwamna Zulum ya kuma bayyana cewa kungiyar ta cimma matsayar samar da megawatt 10 na wutar lantarki ta hasken rana a kowace jiha domin inganta samun ingantacciyar wutar lantarki a fadin yankin.

Ya kara da cewa, kwamitin kwararru na ci gaba da aikin samar da wata hadaddiyar tashar samar da wutar lantarki, wadda za ta samar da ingantaccen tsari na magance matsalolin wutar lantarki a yankin.

Gwamna Zulum ya kuma jaddada bukatar bai wa matasa ingantaccen ilimi, dabarun sana'o'i, harkokin kasuwanci, fasahar zamani da damar samun ayyukan yi.

Ya ce Arewa maso Gabas mai zaman lafiya da wadata ya kamata ya kasance yankin da matasa za su ga makoma a cikinsa, tare da samun halastattun damar gina rayuwarsu.

Taron ya samu halartar gwamnonin Borno, Adamawa da Gombe, da kuma mataimakan gwamnonin Bauchi da Yobe.

Daga Maiduguri:Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi da wasu daga cikin mukarraban gwamnatin jihar sun halarci Dinne...
03/10/2026

Daga Maiduguri:

Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi da wasu daga cikin mukarraban gwamnatin jihar sun halarci Dinner/Gala Night da aka shirya a daren jiya gabannin taron Gwamnonin Arewa maso gabas da zai gudana a yau asabar.

Jatau Ya Wakilci Gwamna Bala A Taron Ƙasa Na Masu Watsa Shirye-shirye A BauchiMai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi,...
28/09/2026

Jatau Ya Wakilci Gwamna Bala A Taron Ƙasa Na Masu Watsa Shirye-shirye A Bauchi

Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau (Madugun Katagum), ya wakilci Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, a wajen bikin buɗe taron shekara-shekara na ƙasa na Society for Nigerian Broadcasters (SNB).

An gudanar da taron ne a Cibiyar Taro ta Ƙasa ta Sir Ahmadu Bello (ICC), Bauchi, inda ƙwararrun masu watsa shirye-shirye da sauran masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai daga sassa daban-daban s**a halarta.

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ƙaddamar da aikin tantancewa da kuma biyan tsohon bashin alawus na ritaya da ake bin ma’aikata...
23/09/2026

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ƙaddamar da aikin tantancewa da kuma biyan tsohon bashin alawus na ritaya da ake bin ma’aikatan gwamnati na jiha da ƙananan hukumomi da s**a yi ritaya.

Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Mai Girma Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau, ne ya wakilci Gwamna Sanata (Dr.) Bala Abdulkadir Mohammed, CON, wajen ƙaddamar da shirin.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin da ya jagoranta ta gaji bashin alawus na ritaya da ya samo asali tun daga shekarar 2012, wanda ya sa dubban masu ritaya s**a shafe shekaru suna jiran a biya su hakkokinsu.

Gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 10 a matsayin kashi na farko domin fara biyan wannan tsohon bashi.

A kashi na farko, za a fara biyan masu ritaya na ƙananan hukumomi daga shekarun 2012 zuwa 2013, sannan ma’aikatan gwamnatin jiha da s**a yi ritaya daga shekarar 2013.

Gwamnatin ta ce za a ci gaba da biyan sauran waÉ—anda abin ya shafa a matakai daban-daban, bisa ga sakamakon tantance bayanai, ingancin takardu da kuma kuÉ—aÉ—en da aka amince da su.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa an ƙarfafa Hukumar Fansho ta Jihar Bauchi (Bauchi State Contributory Pension Commission) domin kula da aikin tantance bayanai da biyan kuɗaɗen.

Haka kuma, gwamnatin ta kafa wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Sabiu Baba, domin tabbatar da cewa kuɗaɗen sun isa ga waɗanda s**a cancanta cikin gaskiya da adalci.

Gwamnan ya umarci jami’an da ke kula da aikin da bankunan da aka ɗora wa alhakin biyan kuɗaɗen da su tabbatar da saurin aiki, gaskiya da kuma adalci, tare da gargadin kada a samu cikas na ofisoshi, nuna bambanci ko karɓar kuɗin haram daga masu ritaya.

Ya kuma bayar da umarnin a ba tsofaffi masu rauni ko nakasa kulawa ta musamman domin kada su fuskanci wahala yayin tantancewa da karɓar hakkokinsu.

Gwamna Bala Mohammed ya ce biyan kuÉ—in na Naira biliyan 10 da aka fara a yau kashi na farko ne kawai, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da biyan sauran bashin ritaya a hankali bisa sahihan bayanai da tanadin kuÉ—aÉ—e.

Ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na maido da martaba da kuma inganta rayuwar ma’aikatan da s**a sadaukar da shekarunsu wajen yi wa Jihar Bauchi hidima.

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya nemi samar da ingantattun dabaru domin jawo masu É—aukar nauyi,...
15/09/2026

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya nemi samar da ingantattun dabaru domin jawo masu ɗaukar nauyi, masu zuba jari da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa kasuwanci da ɗorewar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Wikki Tourists.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da masu tallata ƙwallon ƙafa daga Barcelona da Abuja, inda ya ce gwamnati na sa ran samun sakamako mai ma’ana wajen tallafawa ƙungiyar, zuba jari, inganta suna, sayar da kayayyaki masu alamar ƙungiyar da sauran damar kasuwanci.

Gwamna Bala Mohammed, wanda mataimakinsa Auwal Mohammed Jatau ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar na tallafa wa samar da shafin intanet da kafar sadarwa ta zamani ta Wikki Tourists domin inganta martabar ƙungiyar, rajistar magoya baya, tallace-tallace, tikiti da sadarwa.

Ya bukaci masu tallata ƙwallon, hukumar gudanarwa da shugabannin ƙungiyar su tabbatar da ƙwarewa, gaskiya da rikon amana, tare da tabbatar da cewa haɗin gwiwar da ake shirin kulla wa zai ƙara samar da kuɗaɗen shiga da rage dogaro da tallafin gwamnati.

A nasa jawabin, wani mai tallata ƙwallon ƙafa daga Spain, Gene Joseph, ya ce ziyararsa Bauchi ta biyo bayan tattaunawa da Jacob Onu, mai ba da shawara ga Tarayyar Afirka kan harkokin wasanni, wanda ya gabatar masa da damar da Wikki Tourists ke da ita.

Gene Joseph ya ce ya burge shi da wuraren wasanni, ’yan wasa, masu horaswa da magoya bayan ƙungiyar da ya ziyarta, yana mai bayyana aniyarsa ta taimakawa wajen samar da haɗin gwiwa tsakanin Wikki Tourists da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Turai.

Shi ma Jacob Onu ya nuna damuwa kan yadda Wikki Tourists ke fama da rashin kyakkyawan sakamako a baya-bayan nan, yana mai cewa ƙungiyar na buƙatar rashin son kai wajen gudanarwa, ingantattun tsare-tsare da kyakkyawan shugabanci domin komawa gasar Premier League da samun ɗorewar ci gaba.

Ya ce masu tallata ƙwallon za su taimaka wajen samar da shirye-shiryen

Address

Government House
Bauchi
740001

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Press, Deputy Gov. Office posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share