18/01/2024
MUNIR DANKWAMBO FOUNDATION
FREE JAMB REGISTRATION 2024
Thu, Jan 19, 2024
Amadadin Jagoran Gidauniyar Munir Dankwambo Foundation, Wato Alh Munir Dankwambo (Jagaban Tula)
Ina farin cikin sanar da al'umman Jahar Gombe da cewa kamar yanda muka Saba yi a baya,Duk Shekara wannan shekaran ma baza abarmu abaya Chiroman Talban Gombe Alh Munir Dankwambo Ya Amince Da Biyan Kudin Rubuta Jarrabawa na Shiga Makaranta Gaba Da Sakandari wato Jarrabawar Jamb Kyauta Ga Masu Kananan Karfi
Gidauniya ta Saba bada Jamb kyauta ga ma bukata, Idan bamu manta ba a shekaran da ya gabata na 2023 Gidauniyar Munir Dankwambo Foundation Tabiyawa mutum 670 Registration na JAMB kyauta a Fadin Jahar Mu Ta Gombe Dama Kananan Hukumomi .
Wannan Shine Link Din Da Mutum Zaibi Domin Samun wannan tallafi Gashi Nan A Kasa
https://bit.ly/3vIVH4U
Sannan Form Da Komai Da Komai Kyauta Gidauniyar Mu Bata Amince Ga Wani Ko Wata Yabiya sisin kobold domin cike form din mu komai da komai kyauta ne .
REQUIREMENTS
1. Dole me cikawa ya kasance Dan Jahar Gombe ne (Any of the 11 local Governments Indigine).
2. Ya kasance Mai karamin karfi (less privilege).
3. Ya kasance yanada (7 credits including Maths and English).
Mun samar da wayannan gyare-gyaren ne saboda yanda wasu suke wasa da damar idan an basu. Insha Allah wannan karon za'ayi dubi ga asalin mabukata kuma wanda suke da son cigaba da karatun bayan sunyi jarabawan ta JAMB.
Bayan Gama cikawa (Online Registration), Gidauniyan zata saka rananda za'a tantance kowa( Physical Screening) kafun biyawa wanda yaci tantancewan rajistan.
A kula, Gidauniya kowani dan cikinta bazasu bada dama ga kowa ba se wanda yaci screening da za'ayi.
Da wannan muke sanarda Al'umman gari cewa yau zamu bude kofa domin fara cikawa.
Allah ya bada sa'a ya kuma biyawa Jagaban Tula bukatunsa na alkhairi, Ameen.
Signed
Zakariya Abubakar Kumo (chairman munir Dankwambo Foundation)
19/01/2024
05/10/2023
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
Cikin Alhini Tare Da Kaduwa Muke Sanar Da Wannan rashi Na Alh Sani Abdullahi .
Alh Sani Abdullahi Yakasan Ce Mijine Ga Kanwar Hajiya Adama Dankwambo wato Hajiya Inna Inuwa Gombe
Wanda Allah Yakarbi Rayuwar sa yau A Garin Jos
Amadadin ni kaina Da Dukkan Yan uwa Members namu Na munir Dankwambo Foundation Muna Mika sakon Gaisuwan wa Dukkan Yan uwa da Abokai
Allah Ya Jikan Shi Da Rahama Yasa Aljanna makomarsa
Za Ayi masa Sallah a garin Jos kamar Yadda Addinin Musulunci Yatanadar
Signed
Zakariya Abubakar Kumo (chairman munir Dankwambo Foundation)
5/10/2023
01/10/2023
MUNIR DANKWAMBO FOUNDATION
Happy Independence Day Nigerians!
Amadadin shi kansa Alh Munir Ibrahim Dankwambo (Jagaban Tula) Muna farin cikin taya daukacin jama'ar kasarmu Nigeria na murnan zagayowar wannan Rana da muke cika shekara 63 da samun yancin Kai.
Duk da cewa Kash! Kasarmu tana cikin firgici da tashin hankula daban daban wayanda muke fuskanta a rayuwarmu na yau da Da Kullum, K**a daga demokradiyyarmu,rashin tsaro Rashin kwanciyar Hankali musamman a yankunanmu na Arewa, Garkuwa Da Mutane ,Yawan Hare Hare Da Kashe- Kashe, Yiwa Mata fyade, Fama Da Tsadar Da Abinci da Magani , da sauransu.
Tabbas munkadu da irin abubuwa da suke faruwa a yankunanmu na Arewa. Yazama wajibi ga Gwamnati suyi duba da garan bawul wa harkan tsaro,ilimi,Abinci Da Magani a irin wannan rana yanada kyau akawo Sabbin tsaruka da hanyoyi wanda yan kasa zasuci gaba da morarsu mora.
Kwanan nan akayi Garkuwa da kanne mu yam mata wanda Ke Karatu a Zamfara da sauran kashe kashe Na Malaman mu Da Yan uwa wayanda basuji ba basugani ire iren wannan abubuwan da muke fama dasu yasa hankulanmu ya kasa kwanciya tare Da Samun Nitsuwa.
Da wannan muke kira ga Gwamnati da babbar murya cewa, Aduba Arewa Kuma muga sauyi cikin gaggawa, zaman lafiya shine kashin bayan al'umma.
Kashe Rai a Arewa
Garkuwa da mutane a Arewa
Adena Wahalar Abinci Da Magani
Bata Sunan Arewa
Da harkan Ilimi A Arewa
Taimaki Matasan mu Da Ayyukanyi
da Daraja Da Kimar Kannemu Mata Adaina Musu Fyade
mana Adalci.
Daga karshe muna Kara addu'a, Allah kawo mana zaman lafiya a Arewa da kasarmu Nigeria baki daya domin mucigaba da cin riban demokradiyya.
Allah bamu zaman lafiya Mai daurewa, Ameen.
Signed
Munir Dankwambo Foundation
01/10/2023
26/09/2023
Alhamdulillah,Masha Allah
Happy Maulud
Amadadin Alhaji Munir Ibrahim Dankwambo Yana Taya Daukacin Al-umman Musulmin duniya Murna Zagayowar Wannam wata Mai Albarka na Murna da Farin ciki Na Wata da aka haifi Fiyeyyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W) musamman Al-umman Jahar gombe masu Albarka.
Wannam wata yakasance watane da dukkammu zamu hadu waje daya domin Nuna Farin cikimmu da Soyayarmu Ga Annabi Muhammad (S.A.W).
Munkasance cikin Farin ciki da Zagayowar Wannam wata Mai Cike da dumbin Albarka muna Rokon Allah yakarama na Qauna da Soyayyan Annabi a zukatammu.
Ya Allah Muna tawassali da Sunayenka Tsarkaka Alfarman wannam wata Mai Albarka Allah kawo mana karshen Matsalan da muke fama da ita a kasarmu Mai Albarka ta Nigeria.
Allah kataimaki Munir Dankwambo foundation kabasu Daman Cigaba da Aikin taimakon Al-umman Ameen.
Kowa Yace ( S .A .W ) Alfarman Wannan Rana
Signed
Munir Dankwambo foundation
27/09/2023