Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi Social Media Committee

Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi Social Media Committee

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi Social Media Committee, Political organisation, .

Photos from Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi Social Media Committee 's post 10/09/2025

Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi Social Media Committee

Alhamdullahi Yau 10-09-2025 Maigirma Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Funtua da Dandume, Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi, Ya Hana da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa Hon. Ali Bukar Dalori a Abuja.

A yau ne mai girma Dan Majalisa ya gudanar da wata muhimmiyar ganawa da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan ganawa ta gudana cikin yanayi na tattaunawa kan ci gaban jam’iyya da kuma irin rawar da ‘yan majalisa da sauran shugabanni za su taka wajen tabbatar da nasarar APC a kasa baki ɗaya.

Dan Majalisar ya samu rakiyar wasu manyan abokansa na siyasa, ciki har da Hon. Lawal Isah Kiraye, Hon. Gilima Dandume da Hon. Abdulkadir Usman Funtua, wadanda s**a nuna cikakken goyon baya da hadin kai ga duk wata manufa da za ta ƙara ɗaukaka jam’iyyar APC.

A yayin taron, an jaddada muhimmancin haɗin kai da kuma ci gaba da wayar da kai ga al’umma, domin tabbatar da nasarar jam’iyya a matakai daban-daban na mulki.

Rahoto: Barrister Media Team 4+4

Photos from Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi Social Media Committee 's post 10/09/2025

Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi Social Media Committee

Cikin Daliban Da Maigirma Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Funtua da Dandume, Hon. Barr. Abubakar Mohammad iGardi Esq. Ya Tura Karatun Midwifery And Nursing Sun Fara Aikin Jinkai Tareda Karbar Haihuwa Ga Iyayen Mu Mata.

A Kwanakin Baya Ne Maigirma Dan Majalisar Wakilai Ta Tarrayar Nigeria Mai Wakiltar Kananan Hukomomin Funtua/Dandume Constituency Hon Barrister Abubakar Mohammed Gardi Esq Ya Dauki Nauyin Karatu Wasu Mata 60 Inda 37 S**ayi Nasara Yan Asalin Wannnan Yankin Na Funtua/Dandume Constituency Domin Suje Suyi Karatun Koyon Aikin Jinya Dana Unguwar Zoma Wato Nursing And Midwifery A Makarantar School Of Midwifery Dake Garin Malumfashi.

Ya Zuwa Yanxu Haka Wasu Daga Cikin Wannnan Dalibai Sun Fara Aikin Jinkai Tareda Karbar Haihuwa A Cikin Al.ummah Su Ko A Satin Daya Gabata Daya Daga Cikin Daliban Maryam Musa Mai Alura Dake Unguwar Bagari Funtua Ta Karbi Haihuwa Wani Jariri Cikin Nasara Inda Al.ummah Wannnan Unguwar Suke Chigaba Da Yimata Godiya Da Fatan Alkhairri Tareda Maigirma Dan Majalisar Wakilai Ta Tarrayar Nigeria Mai Wakiltar Kananan Hukomomin Funtua/Dandume Constituency Hon Barrister Abubakar Mohammed Gardi Esq Abisa Irin Wannnan Aikin Jinkai Dayake Amfanar Da Al.ummah.

Tabbbas Ilimantar Da Diya Mace Tamkar Ilimantar Da Al.ummah Ne.

07/09/2025

MURNAR MAULIDIN FIYAYYEN HALITTA ANNABI MUHAMMAD S.A.W.

A Madadin Mazabar Dan Majalisar Wakilai ta Tarayyar Najeriya, Hon Barr Abubakar Mohammad Gardi Dandume Hon Barrister, da Mataimaka Na Musamman Na Dan Majalisar Wakilan Tarayya, 1 Saddam Yusuf Saleh 2 Malam Murtala Dandume Suna mika gaisuwa da jinjina ga daukacin al'ummar Musulmin mazabar Funtua Da Dandume a daidai lokacin da muke murnar zagayowar watan Maulidi Nabiyyil Kareem - maulidin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Wannan biki mai albarka yana tunatar da mu zurfin koyarwar rahama da jin kai da adalci da Manzonmu (SAW) ya zo da su ga bil’adama. Lokaci ne da ya kamata mu zurfafa imaninmu, da karfafa hadin kanmu, da sabunta kudurinmu ga kyawawan dabi'u na Musulunci wadanda suke samar da zaman lafiya a tsakanin al'ummominmu da kasa baki daya.

A yayin da muke tunawa da wannan gagarumin biki, da fatan Allah SWT ya sakawa al'ummar musulmin Funtua Da Dandume da ma Najeriya baki daya, Ya ba mu hikimar koyi da halayen Manzon Allah S.A.W a cikin rayuwarmu ta yau da kullum, da karfin shawo kan kalubale tare da hakuri da juriya.

Mu yi amfani da wannan lokaci a matsayin wata dama ta samar da soyayya, 'yan'uwantaka, fahimtar juna a tsakanin al'umma baki daya, tare da ba da gudummawa ga cigaba mazabarmu da kasarmu.

Mataimaki Na Musamman Na Kakakin Majalisar Wakilai Tarayya, ina addu’ar Allah ya karawa Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam Daraja Ameen

Photos from Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi Social Media Committee 's post 06/09/2025

Alhamdullah Daga Garin Kaduna Wurin Bikin Saukar Karatun Al Qur'ani Maigirma

Tareda Maigirma Dan Majalisar Wakilai Ta Tarrayar Nigeria Mai Wakiltar Kananan Hukomomin Funtua/Dandume Constituency.
Hon. Barrister Abubakar Mohammad Gardi Esq.

Maigirma Dan Majalisar Wakilai Ta Tarrayar Nigeria Mai Wakiltar Kananan Hukomomin Funtua/Dandume Constituency Hon Barrister Abubakar Mohammed Gardi Esq. Ya Hallarci Bikin Saukar Karatun Al Qur'ani Maigirma Wanda Abbas Abdullahi Albasu Yaron Elder A.A Albasu Yasamu Zama Daya Daga Cikin Masu Su Saukar.

Bayan Kammala Bikin Saukar Karatun Al Qur'ani Anyi Addu,o'in Neman Samun Zaman Lafiya A Wannnan Yankin Na Funtua Dandume Constituency Dama Jihar Katsina Da Tarrayar Nigeria Baki Daya.

Maigirma Dan Majalisar Wakilai Ta Tarrayar Nigeria Mai Wakiltar Kananan Hukomomin Funtua Dandume Constituency Hon Barrister Abubakar Mohammed Gardi Yayi Addu,ar Allah Swt Ya Albarkaci Abunda S**a Karanta Tareda Fatan Allah Swt Yasa Su Chigaba Da Zama Jakadu Nagari A Idon Duniya Tareda Fatan Allah Swt Ya Kauratar Da Abunda Ke Cikin Littafin Zuwa Zukatanmu Da Gabbanmu Don Aiki Dashi.

06/09/2025

Innalillahi Wa'innaillaihi Raju'un.
Innalillahi Wa'innaillaihi Raju'un.
Innalillahi Wa'innaillaihi Raju'un.

Bullar Barayin Daji Bandits A Garuruwan Magaji Wando Dandume/Jabiri Funtua

Cikin Alhini Da Jimami Hon. Barrister Abubakar Mohammad Gardi Esq. Yake Mika Sakon Alhinin Shi Da Jajantawa Ga Al.ummah Yankin Magaji Wando Dake Karamar Hukumar Dandume Wanda Barayin Daji Bandits S**a Shiga Garin Jiya Da Dare S**ayi Harbe Harbe Tareda Kisan Mutane (8) Tareda Raunata Wasu.

Inda Muka Kara Neman Daukin Gaggawa Daga Manyan Jami,an Tsaron Mu Na Soji Da Yan Sanda Da Domin Kawo Karshen Wannnan Matsala Tsaro Data Addabi Wannnan Yankin Na Funtua/Dandume Constituency Muna Kara Rokon Allah Swt Ya Kawo Mana Karshen Wannnan Matsala Tsaro Data Addabi Jihar Katsina Da Tarrayar Nigeria Baki Daya Wanda S**a Rasu Allah Swt Ya Karbi Shahadarsu Allah Swt Yasa Aljannah Firdausi Tazama Makoma Agaresu Baki Daya.

Haka Nan Ansamu Bullar Barayin Daji Bandits A Unguwar Jabiri Dake Karamar Hukumar Funtua Duk A Cikin Daren Jiya Inda S**a Shiga Unguwar Jabiri Dake Maigamji Ward Funtua S**ayi Harbe Harbe Tareda Garkuwa Da Wasu Mutane Nuna Rokon Allah Swt Ya Kubutar Dasu Cikin Aminci Allah Swt Ya Kawo Mana Karshen Wannnan Matsala Tsaro Data Addabi Wannnan Yankin Na Funtua Dandume Constituency Jihar Katsina Da Tarrayar Nigeria Baki Daya.

05/09/2025

Murnar Zagayowar Watan da Aka Haifi Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu ﷺ......

Maigirma Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Funtua da Dandume, Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi, Ya Roki Yan Uwa Musulmi Masoya Annabi Muhammadu ﷺ, Dasu Mayar da Hankali Wurin Rokon Allah Ya Kawo Mana Dawwammamen Zaman Lafiya A Wannnan Yankin Na Funtua/Dandume Constituency Da Jihar Katsina Da Tarrayar Nigeria Baki Daya.

Maigirma Dan Majalisar Wakilai Ta Tarrayar Nigeria Mai Wakiltar Kananan Hukomomin Funtua/Funtua Dandume Constituency Hon Barrister Abubakar Mohammed Gardi Yana Taya Daukacin Yan Uwa Musulmi Murna Zagayowar Ranar Haihuwa Fiyayyen Hallita Annabi Muhammadu S.A.W A Yau Jumma'at (12-Rabi'Ul Awwal) Yayi Kira Ga Daukacin Yan Uwa Musulmi Damu Chigaba Da Koyi Da Koyarma Annabin Muhammadu S.A.W Dabin Tafarkin Daya Doramu Akansu Wanda Yin Hakan Zaisa Mukara Zama Jakadu Nagari A Idon Duniya.

Hon Barrister Abubakar Mohammed Gardi Yayi Kira Ga Daukacin Al.ummah Wannnan Yankin Dasu Mayarda Hankali Wurin Rokon Allah Swt Ya Kawo Mana Dawwammamen Zaman Lafiya A Jihar Katsina Da Tarrayar Nigeria Baki Daya Duba Wannnan Hali Na Rashin Tsaro Daya Addabi Wannnan Yankin Na Funtua Dandume Da Jihar Katsina Da Tarrayar Nigeria Baki Daya.

Daga Karshe Hon Barrister Abubakar Mohammed Gardi Yana Taya Daukacin Yan Uwa Musulmi Masoya Annabin Muhammadu S.A.W Murna Zagayowar Ranar Haihuwa Fiyayyen Hallita Daftan Allah Swt Yasa Annabin Yacece Mu Baki Daya

03/09/2025

TWO YEARS OF TRANSFORMATIVE LEADERSHIP AND QUALITATIVE REPRESENTATION.

THANK YOU Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi

1. Tallafawa manoman rani 220 da injinan ban ruwa tare da gina musu rijiyoyin ban ruwa na zamani don habaka nomansu, a dukkan mazabu 22 na Funtua da Dandume.

2. Aikin gyaran dam na Farar Kasa domin bunkasa noman rani a Karamar Hukumar Dandume.

3. Daukar nauyin gyaran famfo na rijiyoyin burtsatse 120 a mazabu 22.

4. Tallafawa manoma da buhunan takin zamani guda 2,000 da injinan ban ruwa a shekarar 2023.

5. Ba da kyautar mota da sabbin wayoyin hannu ga matasa 'yan soshiyal midiya.

6. Rabon kartonin taliya 1,000 ga al’umma don rage radadin rayuwa a shekarar 2023.

7. Rabon littattafan rubutu 20,000 ga makarantun firamare da sakandare.

8. Daukar nauyin mata 38 zuwa makarantar koyon aikin jinya da unguwar zoma a Malumfashi – irinta na farko a tarihi.

9. Samar da ayyukan dindindin (na ofis) ga mutane fiye da 31 a matakin jiha da na tarayya.

10. Gyaran gadon asibiti da raba katifu a Asibitin Dandume.

11. Daukar nauyin matasa 50 da horas da su kan sana'o'in zamani tare da ba kowane tallafin naira 50,000.

12. Sanya fitilun masu amfani da hasken rana 100 a manyan tituna a garuruwan Funtua da Dandume.

13. Nasarar kawo Jami’ar Kiwon Lafiya a garin Funtua.

14. Nasarar kawo Jami’ar Open University (NOUN) a Funtua.

15. Gina makarantar firamare ta zamani a Maigamji.

16. Gina karin ajujuwa a makarantar sakandire ta Community a Dandume.

17. Karin ajujuwa a makarantar Mare Firamare, Dandume.

18. Nasarar samar da fili mai matsakaicin girma donyin filin jirgin sama a Funtua.

19. Tallafin fiye da naira miliyan 40 lokutan bukukuwan Sallah (Karama da Babba) na shekarun 2023, 2024 da 2025.

20. Daukar nauyin yin aiki ga masu fama da matsalolin ido a dukkan mazabu na Funtua da Dandume.

21. Tallafin murnar Maulidin Annabi (SAW) da ya kai naira miliyan 5 a 2023 da 2024.

22. Gina babbar makarantar Islamiyya a garin Maska.

23. Gina karin ajujuwa a makarantar Shehu Abubakar Alti (RA), Funtua.

24. Gabatar da kudirin dokar magance matsalolin tsaro a gaban majalisa.

25. Hadin gwiwa da jami’an tsaro a sirrance don magance matsalar masu ba da bayanan sirri (informants) a Dandume.

26. Raba kekunan guragu 100 ga masu buƙata a Funtua da Dandume.

27. Horas da matasa 20 kan sana’o’in zamani tare da ba kowane kwamfutar zamani kirar HP mai darajar naira 500,000.

28. Daukar nauyin koyar da matasa fasahar canza injin man fetur zuwa na iskar gas (LPG).

29. Tallafawa mabiya addinin Kirista a lokutan bukukuwansu na Kirsimeti.

30. Ba da tallafin naira 100,000 ga dalibai 200 na manyan makarantu – jimilla naira miliyan 20 – a shekarar 2025.

31. Daukar nauyin sayen kayan daki gaba ɗaya ga wata marainiya a mazabar Dantankari.

32. Ba da tallafi ga mutane 30 masu buƙata ta musamman a Karamar Hukumar Dandume.

33. Daukar nauyin tafsirin Alƙur’ani mai girma na Sheikh Ahmed Tijjani Dandume da Sheikh Mahmud Adam a Martaba FM, Funtua.

34. Daukar nauyin shirin Mimbarin Ma’aiki (SAW) na Sheikh Liman Abdurrahman a Martaba FM.

35. Mika kudirin kafa makarantar koyon kiwon dabbobi ta ƙasa a garin Dandume.

36. Ba da katunan ganin likita 3,000 ga marasa lafiya a Asibitin General dake Funtua.

37. Gina da sauya famfo 17 masu amfani da hasken rana.

38. Tallafa wa iyalan wadanda harin ta’addanci ya shafa a Funtua da Dandume.

39. Gabatar da roko ga Gwamna. dan
Neman amincewar gina hanya daga Kasuwar Mata Funtua zuwa Nasarawa Dandume

40. Raba babura kirar Boxer 10 ga matasa a Funtua da Dandume.

41. Tallafin kayan azumin Ramadan da ya haɗa da buhunan shinkafa 3,000, masara 320 da gero 530 a 2023.

42. Ba da kyautar fom na JAMB ga dalibai 70 na yankin Funtua da Dandume a shekarar 2024.

43. Raba buhun shinkafa 5,500 (25kg) a lokacin azumin shekarar 2025.

44. Taimakawa marayu a unguwar Musa, Funtua don biyan kuɗin haya da siyan kayan abinci.

45. Daukar nauyin shirin refresher ga daliban shekarar ƙarshe a makarantun sakandare.

46. Ba da tallafi ga makarantar sakandire ta Dandume da kuma wani tallafin don siyan fili makabarta a yankin Magaji Wando da Mahuta.

47. Sanya transfoma guda biyu – ɗaya a Funtua da ɗaya a Dandume.

48. Tallafi kai tsaye ga Islamiyyu, masallatai, marayu, majiyanta da mabukata a kowane lokaci.

49. Daukar nauyin matasa 6 zuwa Katsina don koyon sana’o’in dogaro da kai.

50. Hada guiwa da hukumar hanasha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta hanyar daukar nauyin shirin wayar da kan matasa illar shan miyagun kwayoyi a Funtua.

Photos from Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi Social Media Committee 's post 03/09/2025

Hon. Barr.....

Alhamdullahi Kadan Daga Bangaren Tallafawa Ga Rayuwar Matasa Maigirma Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Funtua da Dandume, Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi, An Koyawa Matasa 20 Ilimin Na'ura Mai ƙwaƙwalwa Da Kasuwancin Zamani Na Tsawon Kwana Biyu

Wanda Hon. Barrister Abubakar Muhammad (Gardi) Dan Majalisar Mai Wakiltar Funtua Da Dandume Jihar Katsina Ya Dauki Nauyi.

Photos from Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi Social Media Committee 's post 02/09/2025

The Best Record In A Two Years Of Hon. Barr. Abubakar Mohammad Gardi Esq. Hon Member Federal House Of Representative Funtua Dandume Constituency.

1. Veterinary Research institute Dandume Bill - awaiting second reading
2. ⁠Craft institute establishment bill - Submitted before the house
3. ⁠Public officers Restriction Medical Treatment Bill - Submitted before the house
4. ⁠tertiary institutions academic salary enhancement bill - Submitted before the house
5. ⁠public officers children in public schools - Submitted before the house
6. ⁠Compulsory free Child education bill - Submitted before the house.

Sannu Da Kokari Hon Barrister Abubakar Mohammed Gardi Esq. Hon Member Federal House Of Representative Funtua/Dandume Constituency Katsina State.

Want your business to be the top-listed Government Service?

Website