Halqatu Ibni Taimiyah

Halqatu Ibni Taimiyah

Share

حلقة ابن تيمية للدراسات الإسلامية و حفظ المتون العلمية

الهدف العام:
تخريج طلبة مؤصلين في عدد من الفنون الشرعية والعلوم المساعدة وفق منهج علمي متكامل يجمع بين الحفظ والقراءة والتحضير مع المتابعة في وقت وجيز فياسي.

13/03/2026

KARKASUWAR SHI'A,
AƘIDARSU DA HUKUNCINSU
(BIDI'AH KO KAFIRCI)❗

Gyaran
Sheikh Basheer Nuhu Assalafy
ga amsar
Dr. Jalo Jalingo

🔦 GYARA NA BIYU..2️⃣

Gabatarwa :
Sheikh Basheer Nuhu Assalafy
(Hafizahullah)
ـــــــــــــ❁🌼❁ــــــــــــ

16/01/2026

⏳ Saura kwana uku a fara darussa❗💪🏻💯

Koyon Harshen Larabci
da Ilimomin Addinin Musulunci
ta yanar gizo

👉 Shiga WhatsApp don rajista.

wa.me

23/06/2025

KO ..⁉️
SHIN AKWAI NA GARI A TSAKANINSU ⁉️
Sheikh Basheer Nuhu Assalafy Hafizahullah

27/04/2025

TUKUICI GA MAI KASALA ❗

26/04/2025

Saura mako ɗaya
a fara ɗaukar darasi..🚀💪💯

15/04/2025

DUK WANI MAI IJTIHADI YA DACE..❌
Sheikh Basheer Nuhu Assalafy (Hafizahullah)

Wannan zance kuskure ne a ko ina ❗

13/04/2025

AUNA AYYUKAN MALAMI TSAYAYYE AKAN AQEEDAH INGANTACCIYA ❗

Kaɗan daga majlisin rana ta farko na cikin littafin MUWAZANAH, mai suna:
QA'IDAR AWO TSAKANIN KYAWAWA DA MUNANAN AYYUKAN MALAMAI, DA YIN RADDI KO WARWARE SU, TSAKANIN WUCE IYAKA DA SAKACI.

Wallafar malamanmu Sheikh Basheer Nuhu Assalafy (Hafizahullah)

Allah Madaukakin Sarki Ya ƙarawa rayuwarsa albarka Ya kuma amfanar da al'umma daga waɗannan darussa 🤲

10/04/2025

Littafi wallafar Sheikh Basheer Nuhu Assalafy (Hafizahullah)

08/08/2024

KUN GA ILLAR ..‼️

(1)
Kunga illar zanga-zanga
Ko muce sata da banga
Malamai sune mahanga
Sun faɗa domin mu farga
Aibuka da yawa mu ƙirga

(2)
Jahilai sun toshe kunne
Wasu ma wai malamai ne
Masu bin son zuciya ne
Ko ƙiyayyar gwamnatin ne
Ke zama turba ta banga

(3)
Na gano taro da kwaɓa
An kirawo ƴan acaɓa
Ga su ɓera har da jaɓa
Ga maciji ga su kulɓa
Sun biyo ƙofa da taga

(4)
Ga kare ya ɗau agogo
Ga biri ya dafa bango
Ga su kura anyi ɗango
Ko ina sun yada zango
Ca suke sun sami sabga

(5)
Waifa ƴanci za'a ƙwato
Malami, boka da kwarto
Hadda gayu ƴan crypto
Duk a zo domin a ceto
Rayuwa kowa ya farga

(6)
Babu jagora a fili
Koko mai sassaita hali
Sai fa ƴan ƙwaya da sholi
Sun riƙo ganye da kwali
Babu mai sawa su waiga

(7)
Ƴan Kano sam basu ɓuya
Sun ma NCC ƙawanya
Sun fasa sun kwashi kaya
Babu tsoro babu kunya
Sun zamo ɓera a raga

(8)
Sun fashe taskar abinci
Don nufin kore talauci
Ko muce don kare ƴanci
Gashi yau kowa a ƙunci
Duk a ribar zanga-zanga

(9)
Sun tare mota a t**i
Sun jide kaya na kanti
Ca suke sun samu bati
Har da kayan ƙara sauti
Je masallaci ka hanga

(10)
Mu a nan birnin Kaduna
Sunyi ƙwace sunyi ɓarna
Sun fashe shago da rana
Sunci haƙƙin ƴan uwa na
Har waya sun rinƙa fizga

(11)
Gashi har sun farwa banki
Sun fasa sun ɓata aiki
Sunbi ƴan sanda da kulki
Wai suna son canza mulki
Duk da sunan zanga-zanga

(12)
Babu ƙima babu girma
Wai suna ɗibar ganima
Basu ko hangen ƙiyama
Dukiyar kowa su farma
Sun zamo ƴan banga-banga

(13)
Ga maza harma da mata
Naga sun goge a sata
Duk da sunan sun fusata
Ko a tarbiyyar ƙasa ta
Sun riga sun tuɓe riga

(14)
Shi ko addini fa dama
Yayi tambihi da dama
Malamai sun jaddada ma
Zanga-zangar ta tuna ma
Yanzu kowa sai ya farga

(15)
Sai mu koma gunSa Sarki
Malamai har masu mulki
Masu bi sai munyi aiki
Duk mu kakkaucewa raki
Gun du'a'i babu ƙirga

(16)
Rabbi mai tarin karamci
Sa tsaro harma aminci
Sauƙaƙe tsadar abinci
Yassarewa masu ƙunci
Masu sa kaya na ragga

(17)
Shugabanni ƙarfafasu
Sanya albarka garesu
Dukkanin sharri hanasu
Tausayi sanya cikinsu
Sanya alkhairi ya zaga

(18)
Rabbi al'umma Ka gyara
Duk gari manya da yara
Ayyukan maye fitsara
Masu jin kai ko gadara
Ko dabi'ar zanga-zanga

✍🏻
༻📜༺
Abul-Mustapha Al-athary
═══ ༻🕸️༺═══
4/2/1446h 🔁 8/8/2024m

11/07/2024

MATSAYIN ZANGA-ZANGA A MUSULMI..(01)

Duk wanda ya kalli zanga-zanga da bore ga mahukunta da idon basira da hangen nesa, zai iya fahimtar cewa ababe ne waɗanda suke ƙunshe da saɓawa shari'a ta fuskoki da dama.

Zan tsakura maka kaɗan daga cikin waɗannan fuskoki ga abinda ya bayyana a gare ni

1️⃣ Waɗannan abubuwa ba su da tushe a cikin Alkur’ani, ko Sunnah, ko aikin magabata, haka kuma maganganun manyan malamai kafaffu a ilimi, saidai ma sun bayar da fatawa ta haramci ga zanga-zanga da duk wani nau'i na taratsi da bore ga mahukunta.

Kada ka manta mai karatu, malamai nace gogaggu kafaffu a ilimi ❗

2️⃣ Zanga-zanga ta saɓawa nassoshi waɗanda s**a zo game da umarni wajen hakuri da zaluncin mahukunta, da addu’a da maida lamari zuwa ga Allah.

3️⃣ Zanga-zanga ta saɓawa tsarin shari’a game da nasiha ga masu mulki, kamar yadda duk masu karatu s**a sani.

4️⃣ Abune sananne cewa a mafi yawan a mafi yawan lokuta zanga-zanga tana ƙunshe da la'antar masu mulki da keta alfarmarsu, kuma wannan ba ya taɓa zama hanyar canza ɓarna, da ma kuma akwai nassoshin shari'a masu yawa cikin haramci game da hakan.

5️⃣ Zanga-zanga kafa ce dake ɓullewa zuwa ga aikata zunubai masu yawa, kamar : bayyana tsiraici, cakuɗuwar maza da mata, iface-iface, fashe-fashe, ƙone-ƙone da sauransu, waɗanda basu daga cikin tarbiyyar musulunci da al'ummar musulmi.

6️⃣ Wani lokaci zanga-zanga tana sabbaba daidaito tsakanin Musulunci da kafirci, ta fuskar cakuɗewa da tarayya a cikin aiki ɗaya tsakanin musulmai da sauran maz'habobin ƙarya masu da'awar musulunci, dama sauran addinai mabanbanta.

Irin wannan tarayya bata daga cikin tarbiyyar da musulunci ya lamuncewa musulmi ya haɗa kai da kafirai wajen samar da ita ❗

7️⃣ Zanga-zanga ta kan haifar da munanan ayyuka, kamar : zubar da jini, almubazzaranci da kuɗi, yaɗa hargitsi, da dai sauransu; ga kuma rashin cimma abubuwan da ake buƙata a mafi yawan lokuta.

8️⃣ Zanga-zanga da bore ga mahukunta su ne mafara na amfani da makami ga masu mulki, wanda nassoshi s**a yawaita cikin hani game da hakan.

Babu shakka zanga-zanga hanya ce da ke kaiwa zuwa ga khawarijanci(boko haram), domin mutane sunada mabanbantan manufofi a cikin zukatansu, sai kuma zanga-zanga ta share masu fage na bayyana manufofinsu❗

9️⃣ Idan zanga-zanga ta yamutsa lamari ta kuma tsananta, sai ta kai ga shigowar kafircin kasashen waje a kasashen musulmi.

Wannan kuma abu ne da duk mai madaidaici hankali zai iya fahimta, ballantana mai zurfin nazari ko kuma masani a fagen ilimin rayuwa da addini ❗

🔟 Abin takaici ma shine: zanga-zanga asali ne tabbatacce a cikin mulkin demokradiyya, wanda ya samar da dama ga duk wani ɗan ƙasa ya faɗi albarkacin bakinsa, kuma yayi tutsu da zanga-zanga game da abinda yake ganin bai masa ba❗

Ko shakka babu wannan dabi’a ba ta dace da Musulunci ba, kuma wannan ƙa’idar ta saɓawa ƙa’idojin Musulunci, don haka babu wani hukunci sai abinda shari'a ta yanke, kuma baya halatta ga wani ya shar'anta wanin ta, don haka duk wanda ya yi da'awar cewa zai iya saɓawa hakan, ko kuma yana ganin hukuncinta bai tabbata ba, ko kuma bai dace da zamani ba; wannan kuma babu shakka ya afka kan tafarkin halaka.

Allah Ya tsaremu Ya tsare mana imaninmu da addininmu🤲🏻

Abul-Mustapha Al-athary
08037894111
5/1/1446🔁11/7/2024

04/07/2024

RANAR ASABAR MAI ZUWA..
SILSILAH TA..9️⃣

24/06/2024



ANYI MANA ALQAWARI KUMA ZA'A CIKA DA YARDAR ALLAH 💪💯

Want your business to be the top-listed Government Service in Kaduna South?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Address


AF. 8 Birnin Kebbi By Bima Road Tudun Nufawa Kaduna
Kaduna South