27/04/2026
Hon. Hussaini Kero ya sake nuna cewa shugabanci na gaskiya hidima ne ga al’umma. Ta hanyar kokarinsa da taimakonsa, matasa 8 sun samu guraben aiki a Asibitin Tarayya na Kula da Lafiyar Ƙwaƙwalwa (Neuropsychiatric Hospital), Barnawa.
Wannan abin alheri ba kawai samar da aiki ba ne, har ila yau yana nufin taimaka wa iyalai, gina makoma mai kyau, da kuma ba matasa fata a rayuwa.
A jiya, domin nuna godiya da yaba wa irin wannan kokari, wadanda s**a ci gajiyar wannan dama sun taru tare da mika masa lambar yabo ta godiya (Award of Appreciation). Lallai wannan karramawa ta dace da shugaba mai kishin jama’a.
Muna taya shi murna tare da yi masa fatan alheri. Allah ya kara masa lafiya, basira da ikon ci gaba da yi wa al’umma hidima.

16/04/2026