Dan Iyan Dallatun Zazzau

Dan Iyan Dallatun Zazzau

Share

Alhamdulillah Ala Kulli Halin

Photos from Dan Iyan Dallatun Zazzau's post 27/03/2026

Yau muke cika kwanaki bakwai na Sallah. Muna Godiya ga Allah ﷻ da ya rayamu cikin ƙoshin lafiya.

Sallah ya wuce, Allah ya maimaita mana, Ameen.

MATASA - idan kun samu dama kuyi Aure, lallai ku sani akwai alkhairi mai ɗumbin yawa a cikin Aure.

Wato duk yadda za'ayi maka bayanin alkhairin dake cikin Aure, ba za ka fahimta ba, sai kayi Auran. Sai dai ayi don Allah, kada ayi don magance sha'awa ko dan neman tara abin duniya ga masu Auran Jari kenan, domin akwai da yawa waɗanda suke Aure ba don Allah ba, ba domin sun yarda suyi Auran don Ibada ne ba. Lallai ka sani, ki sani, idan har za kuyi Aure ba don Allah ba, to babu shakka ba za kuga alkhairin dake tattare da Auran ba, kuma daɗin da za kuji na ɗan lokaci ne, takaici zai biyo baya. Sai dai kuma ku sani, akwai jarabawa da ƙalubale a cikin Aure, amma idan akai haƙuri aka jure, tabbas za aga sakamako na alkhairi mai tarin yawa.

Ina amfani da wannan dama in sake gode wa dukkan waɗanda s**a taka rawar gani wajen ganin Auran mu ya kasance. Tun daga ɓangaren Iyaye da Ƴan'uwa da Abokai da Iyayen gida na Siyasa. Allah ta'alah ya saka ma kowa da alkhairi. Nagode!

Matata JAMILA - Allah yai miki Albarka, Allah ya ƙara mana zaman lafiya da haƙuri da fahimtar juna, Allah ya barmu tare ya bamu zuri'a masu Albarka, alfarmar Shugaba ﷺ Ameen thumma Ameen.

Photos from Dan Iyan Dallatun Zazzau's post 20/03/2026

EID MUBARAK | Alhamdulillah. First Eid with my lovely wife. Muna yiwa ɗaukacin Ƴan'uwa da Abokan arziki barka da Sallah. Allah ta'alah ya karɓa mana ibadunmu, ya maimaita mana, Ameen.

20/02/2026

Yau sati biyu da kasancewar mu tare a matsayin Miji da Mata. Allah abin Godiya. 🙏🏻

Tabbas akwai farin ciki a cikin Aure mara misaltuwa, haka zalika akwai ƙalubale, amma haƙuri da juriya shi ne jigon zamantakewar Aure.

Ni da Matata muna zaune lafiya, cikin farin ciki da ƙaunar juna. Zan iya cewa nafi kowa sa'ar Mata 😊

Ya Allah, muna ƙara Godiya gareka, ka ƙara mana zaman lafiya da haƙuri da fahimtar juna. Allah muna tawassuli da ibadan da zamuyi a wannan wata mai Albarka, Allah ka rufa mana Asiri, ka shiga lamarin mu, ka bamu zuri'a masu Albarka, dan alfarmar Shugaban mu Annabi Muhammad ﷺ Ameen.

Photos from Dan Iyan Dallatun Zazzau's post 03/02/2026

𝐒𝐎𝐅𝐓 𝐑𝐄𝐌𝐈𝐍𝐃𝐄𝐑 | In the next THREE Days, our wedding fatiha will take place, insha Allah.

📅 𝐃𝐚𝐭𝐞: Friday, 6th February 2026.
🕐 𝐓𝐢𝐦𝐞: 1:00 PM
📍 𝐕𝐞𝐧𝐮𝐞: Ni'ima Juma'at Masjid, New Jos road, Zaria City.

You are all invited, and we kindly request your prayers and blessings. 🙏🏻

23/01/2026

𝐌𝐘 𝐖𝐄𝐃𝐃𝐈𝐍𝐆 𝐈𝐍𝐕𝐈𝐓𝐀𝐓𝐈𝐎𝐍 -
Bismillahirrahmanirrahim. Alhamdulillah!!
The long-awaited moment has finally arrived.

Today makes it exactly two weeks to my wedding fatiha ceremony. I am delighted to invite you.

📅 𝐃𝐚𝐭𝐞: Friday, 6th February 2026.
🕐 𝐓𝐢𝐦𝐞: 1:00 PM
📍 𝐕𝐞𝐧𝐮𝐞: Ni'ima Juma'at Masjid, New Jos road, Zaria City.

It would be a great honor to have you attend this special occasion and celebrate with us.

If you're unable to join us, we kindly request your prayers and good wishes for the success of this occasion. Thank you for considering this invitation.

22/10/2025

SAƘON GODIYA - Alhamdulillah. Ina ƙara yiwa Allah (Swt) Godiya da ya nunamin zagayowar ranar haihuwata, wanda a wannan shekaran ya zo min da farin ciki na musamman. Kamar yadda kowa ya sani tsayar da ranar Aure, ba Aure bane, matakin farko ne dake sanya farin ciki a zukatan Masøyan da s**a aminta da juna, s**a yarda su kasance tare a matsayin Miji da Mata. Tabbas abin farin ciki ne, ban tabbatar da haka ba, sai da layi yazo kanmu.

Mun gode da Addu'o'i da fatan Alkhairin da kukayi mana a ƙasan post ɗin da nayi, na bi na karanta comment ɗin kowa, sai dai ayi haƙuri ban iya bin kowa nayi reply ba, saboda comments sunyi yawa. Nayi received calls nayi received messages ta messenger ta WhatsApp babu adadi. Naji daɗi ƙwarai da gaske, ba abinda za muce maku sai Godiya, mun gode. Jazakhallahu bi Khair. Allah ya saka ma kowa da Alkhairi, Allah ya bar zumunci 🙏🏻

A gefe guda, masu complain cewa, Aure sai next year amma na fitar da Pre-wedding pictures tun yanzu. Nagode da kulawarku, but waɗannan pictures da kuka gani, duk ba Pre-wedding pictures bane. Pictures ne da mukayi domin farin cikin an sa mana rana, kuma muka ƙi fitar dasu sai a ranar Birthday ɗina, saboda mu samu wani Special memories wanda Facebook za su riƙa tuna mana a duk ranar birthday ɗina. Pre-wedding sai nan gaba.

Masu tambayar Venue na inda za'a ɗaura Aure da time, ina sanar dasu, idan lokacin fitar da Invitation yayi duk za su gani, insha Allah. Zaria za kuje 😊

Ku fahimci girman farin cikin da nakeyi, ba mamaki shiyasa nayi abu ba akan tsari ba, ko ba dai dai ba.

Nagode maku da Addu'o'in ku, da fatan Alkhairin ku.

Photos from Dan Iyan Dallatun Zazzau's post 20/10/2025

Alhamdulillah! Godiya ta tabbata ga Allah (Swt) mai kowa mai komi. Salati da kirari su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammadu ﷺ. Tsira da aminci su tabbata gareshi da Iyalan sa baki ɗaya.

Kamar kowani shekara, rana kamar ta yau 20th October 2025 nake murnar ƙarin shekera. Sai dai wannan shekaran murnar tawa na musamman ne.

Ina farin cikin sanar da Ƴan'uwa da Abokan arziki, an sakamin ranar Aure da abar ƙauna ta Jamila.

Wato komi lokaci ne, na jima ina fama da tambayar yaushe za kayi Aure? wasu s**e kaƙi Aure Khaleel, tun ina ɗaukan abin wasa har raina ya soma ɓaci, sai da na kai matakin da na rage zuwa ɗaurin Auran Abokai, saboda gudun ɓacin rai, Ni kaɗai nasan halin da nake ciki. Na kan bayar da amsar idan lokaci yayi zanyi Aure, amma duk da haka ban tsira ba, gani akeyi banyi niyyar Auran bane, ko kuma banaso inyi ne. Duk wanda yaimini farin sani zai bada shaidar cewa shekaru 15 ko sama da haka da s**a gabata nayi yunƙurin yin Aure amma Allah bai nufa ba, da yake lokacin baiyi ba. To Alhamdulillah. Tabbas komi lokaci ne, zan iya cewa lokacin yayi.

Insha Allah, Ni da Jamila za mu kasance a matsayin Miji da Mata, A ranar Juma'a 6th February, 2026.

Jamila ta kafa tarihi wanda ba zai gogu ba a rayuwa ta. Ban taɓa samun Mace mai sona, so na gaske, mai tausayina, mai son mu rayu tare kamar Jamila ba. Na gamsu Jamila tana ƙauna ta 100 percent.

Ku shaida, ina ƙaunar Jamila with all my heart 🥰
Muna baran Addu'ar ku da fatan Alkhairi. Mun gode.

13/10/2025

Kada ka kalli girman matsalarka, ka kalli girman Allah da zai warware maka ita, ka miƙa damuwarka gareshi, tabbas zai magance maka damuwar ka.

Kamar kowani shekara, Yau saura kwanaki 8️⃣ ranar haihuwata ya zagayo, 21st October. Insha Allah.

Wannan rana zai bambanta da sauran ranaku a Tarihin rayuwata. Masøya za suyi farin ciki.

Allah ta'alah ya kaimu da rai da lafiya, Ameen.

Ya Allah, kamar yadda kake juya dare zuwa rana, Ya Allah, ka juya damuwar mu zuwa farin ciki, dan alfarmar Shugaba Annabi Muhammad ﷺ Ameen.

Photos from Dan Iyan Dallatun Zazzau's post 16/05/2025

Madugun Kwankwasiyya yana matuƙar burgeni.

Yau gashi a birnin Zazzau yaje gaisuwar ta'aziyyar Marigayi Turakin Dawakin Zazzau Alh Ramalan Yero. Allah ya jaddada Rahama gareshi, Ameen.

Want your business to be the top-listed Government Service in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Kaduna