31/03/2026
💥 wasa farin girki
Sadiq wali youth o’clock Kano central campaign for governor 2023
31/03/2026
💥 wasa farin girki
31/03/2026
💥 Here we go
30/03/2026
Menene fatan ku a wannan tafiyar
11/03/2026
12/02/2026
Wacce hulace tafi DARAJA…
Ku saka mana a comment section
06/02/2026
Da tsohuwar zuma ake magani….
06/02/2026
Kodai muje maha…?
05/02/2026
ABIN MAMAKI DA DAMUWA MAI GIRMA
Abu ne mai matuƙar mamaki da tayar da hankali ganin yadda uwar jam’iyyar PDP ta ƙasa ta sanar da naɗa caretaker committee a Jihar Kano. Wannan mataki ba wai kawai abin tambaya ba ne, har ma yana nuna alamar rashin gaskiya, rashin adalci, da yunƙurin yin zagon ƙasa ga tafiyar siyasar jihar Kano.
Abin da ya ƙara tayar da hankali shi ne, akwai zababbun shugabanni sahihai a jihar Kano, waɗanda ’yan jam’iyya s**a zaɓa bisa doka da ƙa’ida, tare da cikakken fata da amana cewa za su yi musu jagoranci na gaskiya, adalci da riƙon amana. Watsi da waɗannan shugabanni da aka zaɓa, tare da ɗaukar matakin naɗa caretakers, na nuna raina ra’ayin ‘yan jam’iyya da kuma tauye hakkinsu na dimokiraɗiyya.
Tsoma baki cikin harkokin jam’iyyar jihar ba tare da la’akari da tsarin da ke akwai ba, abu ne da ke haifar da ruɗani, rarrabuwar kai, da shakku kan ainihin manufar wannan mataki.
Wannan lamari na nuna kamar ana ƙoƙarin murƙushe muradun ‘yan jam’iyya na gaskiya, tare da ƙirƙirar rikici domin cimma wata manufa ta ɓoye. Irin wannan mataki ba ya dace da jam’iyya mai ikirarin bin tafarkin dimokiraɗiyya, adalci, da girmama zaɓin jama’a.
A ƙarshe, wajibi ne uwar jam’iyyar PDP ta ƙasa ta sake duba wannan mataki cikin gaggawa, tare da girmama zababbun shugabannin da ‘yan jam’iyya s**a zaɓa, domin siyasar Kano ba ta bukatar tsoma baki marar tushe, illa tana bukatar gaskiya, adalci, da mutunta ra’ayin ‘yan jam’iyya.