Muhd Kassim Warure Media

Muhd Kassim Warure Media

Share

MUHAMMAD KASSIM UMAR WARURE MEDIA SUPPORT

Photos from Muhd Kassim Warure Media's post 04/04/2026

HASKEN GWALE MAI JAMA'A!

Yau Asabar 4 ga watan March 2026 daga gurin daurin auren aboki kuma masoyi inda Hon. Muhammad Kassim Warure (HASKEN GWALE) yasamu damar halarta.

Photos from Muhd Kassim Warure Media's post 31/03/2026

Today at the National Assembly, Abuja.🇳🇬
A reminder that leadership is not a dream—it is a responsibility.
We are getting closer, Insha Allah.

Hasken Gwale muke fata.

Photos from Muhd Kassim Warure Media's post 27/03/2026

Magoya bayan fitaccen ɗan kasuwa a Jihar Kano, Honourable Alhaji Muhammad Kassim Warure, sun mamaye wasu sassa na filin da ake gudanar da babban taron jam’iyyar APC a Abuja, inda s**a nuna goyon bayansu ga bukatar ya tsaya takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwale.

Wannan mataki na zuwa ne bayan da wasu kungiyoyi a Gwale s**a bukaci Alhaji Muhammad Kassim Warure da ya shiga takarar, suna mai bayyana cewa yana da gogewa da kwarewa wajen jagoranci da kuma taimakon jama’a.

Magoya bayan sun jaddada cewa Warure ya yi fice wajen ayyukan jin kai da tallafawa al’umma, musamman matasa da marasa galihu, abin da s**a ce ya sa ya cancanci samun damar wakiltar su a Majalisar Tarayya.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Honourable Alhaji Muhammad Kassim Warure bai fitar da wata sanarwa kai tsaye kan ko zai amsa wannan kira ba.

Photos from Muhd Kassim Warure Media's post 26/03/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI

EID-EL-FITR: Alhaji Muhammad Kassim Warure ya kai ziyarar barka da Sallah ga Sheikh Qaribullah Kabara

Shahararren ɗan kasuwa a Jihar Kano, Honourable Alhaji Muhammad Kassim Warure, ya kai ziyarar barka da Sallah tare da neman albarka ga shugaban ɗariƙar Qadiriyya na Afirka, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, a gidan Qadiriyya da ke Kabara a birnin Kano.

A yayin ziyarar, Alhaji Muhammad Kassim Warure, ya bayyana cewa ziyarar ta kasance domin girmamawa da taya murnar Sallah, tare da neman addu’ar Shehin Malamin kan abubuwan da ya sa a gaba domin samun nasara da alkhairi.

A nasa ɓangaren, shugaban ɗariƙar Qadiriyya, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, ya bayyana jin daɗinsa da ziyarar, yana mai yi wa Warure addu’a da fatan alkhairi a rayuwarsa.

Sanarwa:
Suleman Ibrahim Modibbo
Publicity Secretary
(Alhaji Muhammad Kassim Warure)

26/03/2026

Homage visit to Malam Salihu Sagir Takai by Hon. Muhammad Kassim Warure (Hasken Gwale).

Photos from Muhd Kassim Warure Media's post 26/03/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI

EID-EL-FITR: Alhaji Muhammad Kassim Warure ya kai ziyarar barka da Sallah ga Malam Salihu Sagir Takai

Shahararren É—an kasuwa a Jihar Kano, Honourable Alhaji Muhammad Kassim Warure, ya kai ziyarar barka da Sallah ga shugaban shirin Renewed Hope Agenda na Jihar Kano, Salihu Sagir Takai.

Da yake jawabi a yayin ziyarar, Alhaji Muhammad Kassim Warure, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin neman albarka da kuma shawarwari kan harkokin siyasa da ya sa a gaba, yana mai bayyana Salihu Sagir Takai a matsayin uba kuma jigo a jam’iyyar APC.

Warure ya kuma taya shi murnar samun muƙamin jagorantar shirin Renewed Hope Agenda na Bola Ahmed Tinubu a Jihar Kano, yana mai cewa ya dace da wannan muƙami, la’akari da irin gogewa da ƙwarewarsa a harkar shugabanci.

A nasa ɓangaren, Salihu Sagir Takai ya bayyana jin daɗinsa da ziyarar, inda ya yi addu’a tare da fatan alkhairi ga Alhaji Muhammad Kassim Warure.

Ya kuma ƙara da cewa irin mutane kamar Warure ne ake buƙata a siyasa, duba da nutsuwarsa, dattakonsa da kuma yadda ya ke taimakawa al’umma, musamman a ƙaramar hukumar Gwale da Jihar Kano baki ɗaya.

Sanarwa:
Suleman Ibrahim Modibbo
Publicity Secretary
(Alhaji Muhammad Kassim Warure)

12/11/2024
Photos from Muhd Kassim Warure Media's post 12/11/2024

Ongoing Renovation and Construction of four Classrooms at Unguwa Uku Model Pri, Schl, Tarauni L.G, Kano State..


Want your business to be the top-listed Government Service in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Abdullahi Wase Road, Gwale L. G. A
Kano
700101