25/09/2026
BAYANIN HANDOVER
Ni, Musa Ibrahim Galadima, tsohon Shugaban Ƙungiyar Wakili Reporters UGG/MJB, cikin girmamawa da godiya, na mika ragamar shugabancin ƙungiyar ga Hon. Abubakar Adamu, wanda ya kasance Secretary General na ƙungiyar, kuma yanzu shi ne sabon Shugaban Ƙungiyar Wakili Reporters UGG/MJB.
An gudanar da wannan Handover ne domin tabbatar da ci gaba da tafiyar da ayyukan ƙungiyar cikin tsari, haɗin kai, gaskiya da mutunta juna.
Ina miƙa godiyata ga dukkan mambobin ƙungiyar bisa goyon baya, haɗin kai da gudummawar da s**a ba ni a lokacin da nake jagorantar ƙungiyar.
Ina kuma taya Hon. Abubakar Adamu murnar wannan sabon matsayi, tare da yi masa fatan samun nasara da ikon tafiyar da ƙungiyar bisa kyakkyawan shugabanci.
Allah Ya taimake shi, Ya ba shi hikima da hangen nesa wajen jagorantar Wakili Reporters UGG/MJB, domin ci gaba da samun nasara da cimma manufofin ƙungiyar.
Daga:
Musa Ibrahim Galadima
Tsohon Shugaban
Wakili Reporters UGG/MJB