24/05/2026
🕋✨ Mina na iya zama wajen da mutum zai rikice musamman ga masu zuwa Hajji karo na farko. Yin shiri da kula sosai na taimakawa wajen sauƙaƙa ibada cikin aminci da kwanciyar hankali.
Ga wasu muhimman shawarwari domin kada ka ɓata hanya a Mina:
📍 Da zarar ka isa, ka gano tantinka a taswira sannan ka haddace ainihin wajen.
📞 Ka adana lambar jagoran ƙungiyarku a waya kuma ka tabbata tana da sauƙin samu.
👥 Ka kasance tare da ƙungiyarka a koda yaushe. Idan kuka rabu, ka sanar da jami’i ko ma’aikaci nan take.
🪧 Ka kula da allunan hanya, lambobin sashe da wuraren da s**a shahara domin su taimaka maka wajen gano hanyar dawowa.
🗺️ Kafin ka fita daga tantinku, ka tsara hanyar dawowarka domin samun sauƙin komawa.
Ka ajiye wannan jagora domin tafiyar Hajjinka, ko ka tura shi ga ‘yan uwa da abokan arziki masu shirin zuwa Hajji 🤍
🕋 Muna hidimar Alhazai tun shekarar 1982
Aroma Travel Service Pvt Ltd
“Sunan da za ka iya yarda da shi.”
20/05/2026
ALHAMDULILLAH… ✈️🕋
⏰ 5:00am
Yanzu haka muna a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano International Airport domin shirye-shiryen tashi zuwa Ƙasar Saudiyya, inda zamu sauka kai tsaye a Birnin Jeddah domin sauke farali na aikin Hajjin bana 2026.
Ina matuƙar godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da Ya nuna min wannan rana mai albarka. Haka kuma ina miƙa saƙon godiya ta musamman ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa wannan dama da kulawa da ya bai wa al’ummar jihar Kano. Allah Ya saka masa da alkhairi, Ya ƙara masa lafiya da nasara wajen jagoranci.
Ina kuma addu’ar Allah Ya kawo wa duk wanda bai samu damar zuwa bana ba nasa lokaci cikin sauƙi da alkhairi. 🤲
Ina roƙon addu’o’inku na Allah Ya sa tafiya lafiya, Ya karɓi ibadunmu, Ya sa mu dawo gida lafiya cikin rahama da gafara.
A matsayina na ɗan Adam, ina neman yafiyar duk wani kuskure ko ɓata rai da na taɓa yi wa kowa, cikin sani ko rashin sani.
Allah Ya sa Hajjinmu ya zama Hajji Mabrur. Ameen. 🕋🤍
Munir Ibrahim Takai
Ssr Film Institute Kano,
To the Executive Governor of Kano State.
Highlights
18/05/2026
Gadai Ainihin Yadda Wajen Taron Oga Ake,
Amma kunzo kunata Sakawa Mutane Tsohon hoton lokacin da muke tare Daku.
#
18/05/2026
*SANARWAR!!!!! SANARWA!!!!!*
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano na sanar da Alhazan da s**a fito daga ƙananan hukumomin:
- TOFA
- RIMIN GADO
- MADOBI
- KABO
- GARKO
- AJINGI
- WUDIL
- TAKAI
- SUMAILA
- GAYA
- KARAYE
- ROGO
Cewa su fito Sansanin Alhazai na Jihar Kano (Hajj Camp) domin tantance su zuwa ƙasa mai tsarki.
Za su fito ne a yau Litinin, 18 ga Mayu, 2026 da misalin ƙarfe 12:00 na dare.
Ana buƙatar maniyyata su fito cikin uniform ɗinsu tare da ƙananan jakunkunan da aka ba su domin tafiya ƙasa mai tsarki.
Sanarwa daga:
Sulaiman Abdullahi Dederi
P.R.O
17/05/2026
Jajirtaccen Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf , ya sasanta saɓanin da ke shirin ɓarkewa tsakanin Hon. Alhassan Rurum da Sen. S A Kawu Sumaila, OFR Ph.D domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da cigaban siyasar Jihar Kano. 🙏
Munir Ibrahim Takai
Ssr Film Institute Kano
17/05/2026