29/05/2026
DR UMAR GARBA
i belong to everybody and i belong to nobody Yan kumbotso muna bukatar chanji, A wajan Allah muke nema ga sabon jini nan muh'd fairuz
29/05/2026
15/05/2026
Allah ka bamu sa'a.
29/04/2026
Jiya kenan 28_04_2026 a wata ziyara da nakai wa Mai girma Jagora a gidansa dake Abuja domin tattauna wasu batutuwa.
Muna adduar Allah ya cikawa me gidanmu burikansa na alkhairi. Ameen.
Dr. Umar Garba
13/04/2026
A madadin Dr. Umar Garba , tsohon shugaban hukumar kare hakkin masu saya da sayarwa ta Jihar Kano, tare da daukacin magoya bayansa, muna mika sakon ta’aziyya ga Hon. Umar Ibrahim Balla bisa rasuwar mahaifiyarsa a wannan rana ta 13/04/2026.
Hakika wannan babban rashi ne ba kawai ga iyali ahalinta kadai ba, har ma ga abokai da ‘yan uwa baki daya. Muna rokon Allah (SWT) Ya jikanta da rahama, Ya gafarta mata, Ya kuma sanya Aljannatul Firdaus ta zama makomarta.
Muna kuma addu’ar Allah Ya ba iyalanta da daukacin ‘yan uwa hakurin jure wannan rashi.
Allah Ya jikan Hajiya da rahama, Ya kuma sa mu dace da samun rahamarsa a kodayaushe.
Amin.
Sanarwa daga:
SANI ABDULLAHI IBRAHIM
09/04/2026
A wannan ranar ta Alhamis, 09/04/2026, tsohon shugaban Hukumar Saye da Sayarwa ta Jihar Kano, Dr. Umar Garba , tare da dimbin magoya bayansa, sun kai ziyara ta girmamawa da jaje ga tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda shahararren masanin akidar Kwankwasiyya ne.
Ziyarar ta kasance wata dama ta nuna tausayi, goyon baya da kuma karfafa zumunci tsakanin shugabannin siyasa da al’umma. Haka kuma, an yi amfani da wannan ziyara wajen tattauna muhimman al’amuran da s**a shafi ci gaban al’umma da siyasa a jihar Kano.
Muna addu’ar Allah Ya karbi wannan ziyara da alheri, Ya kuma kara dankon zumunci da fahimtar juna a tsakaninmu.
🖋️🖋️🖋️🖋️
SANI ABDULLAHI IBRAHIM
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano
