28/02/2026
Dama sun san kansu ne
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi gargaɗin cewa ‘yan Najeriya na iya nuna mummunar martani a akwatin zaɓe idan matsalolin tattalin arziƙi da tsaro na yanzu s**a ci gaba, yana mai kwatanta lamarin da shan kaye da tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ya yi a zaɓen 2015.
Galadima ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya bayyana a matsayin baƙo a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels mai suna Politics Today, inda ya soki manufofin jam’iyyar mai mulki ta APC, tare da watsi da ikirarin cewa rayuwar jama’a ta inganta.
28/02/2026
kaji tsoron Allah
Babban abin takaici ne ayadda shuwagabanni suke burus da harkar tsaron Arewacin nan kuma a hakan a sami wasu maras tsoron Allah wadan da basu yadda Allah ne yake azzurtawa ba saboda dan abin da zasu samu su ringa kokarin lallai sai sun baiwa iyayen gidan su kariya ( azzaluman shugabanni masu ci ) wanda hakan ne yake kara assasa wadan nan matsalolin domin hakan yana alamta cewa bamu damu da abinda ke faruwa ba matukar za'a bada kudi yanzu idan banda rashin sanin kai ko ince iskanci irin na shugabanni Dawowar Sale pakistan da aka taro shi yake campaign Yana cewa Nigeria ana amsa masa da sai tunibu dan Allah anan ina technology, koda kana son tunubu mun yadda to amma kana cikin yankin da ake kashe musulmai kamai fara kuma kazo ka tara masu dabi'un dabbobi kana yiwa wanda karkashin kulawar sa ake duk abin da ake din kenan hakan kana nuna baka da matsala da hakan a cigaba da yi tunda kai ma yanzu dabi'un ku daya su kuma yaran da ka tara suke maka ihun dama kun jahitar dasu kun hana su ilimi b***e su gane ina kuka dosa sale Pakistan kaji tsoron Allah
27/02/2026
Gwamna Abba ka fi ƙarfin mota
Maigirma gwamna Abba K. Yusuf, duk wanda Allah Ya ba wa shugabanci sai ya haɗa da hakuri da jama’a. Babba juji ne, inji masu iya magana. Shi kuwa William Shakespeare cewa ya yi “Uneasy lies the head that wears a crown". Bima’ana, duk wata matsala ta tattara akan wanda ya hau kujerar shugabanci.
Duk wanda Allah ya zaɓa cikin miliyoyin mutane ya ba wa ragamar shugabanci, to kuwa sai ya haɗa da haƙuri da miliyoyin jama’a. Dole sai ya gani, ya nuna bai gani ba, kuma ya ji, ya nuna bai ji ba.
Akwai ɗaya cikin tsoffin kwamishinanka da ya nemi shawarata kimanin sati biyu da s**a gabata, kan batun motocin da aka siya musu. Shawarar da na ba shi ita ce: in dai za ka iya ajiye kujerar kwamishina, mece ce kuma mota da ba za ka iya ajiyewa ba? Haka dai muka rabu, bai gamsu da shawarar da na ba shi ba na ya mayar da motar salin-alin.
Duk da cewa a fahimtata ka fi kwamishinonin nan gaskiya akan wannan lamari, amma tunda kai babba ne, bai kamata mota ta janyo cece-ku-ce tsakaninka da tsofaffin kwamishinoni ba, musanman dan albarkacin ɗan gidan Kwankwaso.
Duk wata ni’ima da alfarma ta ofis, gwamna ka samu a ƙarƙashin Kwankwaso – tun daga gida da mata da mota da kujerar hajji da uwa-uba kujerar gwamna, duk Allah Ya ba ka ta silar wannan bawan Allah. Akwai abin da ɗauke kai ya fi kawo maslaha akan cewa lallai sai an bi ƙa’ida.
Wannan hoton mushen motar ka ce Toyota Corolla (First Lady), wacce Kwankwaso ya siya maka tare da manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati a 1999, kuma ya sahale muku ku tafi da ita bayan an faɗi zaɓe.
Hausawa na cewa in dai loma ɗaya ta ishi maƙwalamci, to a tsoma a mai ba shi.