24/07/2026
Shirin gyaran ilimi na Gwamnatin Jihar Kano ya samu gagarumar karramawa a matakin ƙasa da ƙasa bayan da shugabannin harkokin ilimi na duniya s**a yaba da ƙudirin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na sauya fasalin ilimi ta hanyar ci gaba da saka jari, aiwatar da sauye-sauyen manufofi da kuma inganta sakamakon koyo.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis.
An bayyana wannan yabo ne yayin Taron Ƙasa da Ƙasa na Majalisar Dokoki kan Juyin Juya Halin Karatu (International Parliamentary Forum on Reading Revolution) da aka gudanar a House of Lords, Westminster, London, a ranar Alhamis, 23 ga Yuli, 2026.
Ƙungiyar Universal Learning Solutions (ULS), wata ƙungiya mai zaman kanta ta ƙasa da ƙasa da ke aiwatar da shirin Jolly Phonics a Najeriya domin bunƙasa ƙwarewar karatu da rubutu a makarantun boko da na haɗaka, ita ce ta tallafa wajen shirya taron.
Da yake jawabi a wajen taron, Babban Daraktan Universal Learning Solutions, Mista Gary Foxcroft, ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jagoranci nagari da hangen nesa da ya nuna wajen sauya tsarin ilimin Jihar Kano ta hanyar ci gaba da samar da isassun kuɗaɗe da kuma ƙirƙirar yanayi mai dacewa domin aiwatar da gyare-gyaren ilimi.
Taron tattaunawar ya gudana ne ƙarƙashin jagoranci da shugabancin **Lord Alton na Liverpool**, fitaccen mamba a Majalisar House of Lords, wanda ya bayyana cewa Najeriya da Birtaniya suna da alaƙa mai ƙarfi ta fuskar muradu da ƙimomi iri ɗaya.
Ya ce matakin da Jihar Kano ta ɗauka na rungumar tsarin koyar da karatu da rubutu na Ingila wani muhimmin tsari ne da zai taimaka matuƙa wajen inganta ilimin yara.
A cikin muhimmin jawabin da ya gabatar, **Rt. Hon. Sir Nick Gibb**, wanda shi ne Ministan Makarantu mafi daɗewa a tarihin Birtaniya, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano ta nuna ƙwarin gwiwa da babban buri wajen sauya fasalin ilimi.
Da yake wakiltar Gwamna Abba Kabir Yusuf, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Gyaran Ilimi, Haladu Mohammed, ya shaida wa Majalisar Dokokin Birtaniya cewa ilimi shi ne babban abin da gwamnatin yanzu ta bai wa fifiko.
Ya ce gwamnatin Kano na ci gaba da ware kaso mafi girma na kasafin kuɗinta na shekara domin bunƙasa ilimi a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin farfaɗo da fannin.
Haladu Mohammed, ya bayyana cewa a halin yanzu akwai kimanin ɗalibai miliyan biyar da ke karatu a makarantu daban-daban na jihar Kano.
A cewarsa, jihar na da sama da makarantu na boko 8,000 da kuma fiye da makarantun Alƙur'ani 14,000 waɗanda ake haɗawa da tsarin ilimin zamani.
Ya kuma bayyana cewa har yanzu Kano na fuskantar ƙalubalen yara sama da miliyan ɗaya da ba sa zuwa makaranta, lamarin da ya sanya gyaran ilimi ya zama babban fifikon gwamnati.
Haladu ya ƙara da cewa jihar na buƙatar ƙarin malamai kusan 84,000 domin biyan buƙatun ilimi da ke ƙaruwa.
Sai dai ya bayyana cewa gwamnatin mai ci ta ɗauki sabbin malamai kusan 20,000 cikin shekaru uku da s**a gabata domin rage gibin ƙarancin malamai.
Ya kuma sanar da mahalarta taron cewa gwamnatin ta ƙaddamar da sabuwar Manufar Bunƙasa Malamai, wadda ta tanadi ɗaukar malamai bisa la'akari da buƙatun kowace al'umma.
Bugu da ƙari, ya ce gwamnati ta tsara Shirin Gaggauta Ilimin Bai Daya (Accelerated Basic Education Programme) domin bai wa yaran da s**a wuce shekarun makaranta amma ba sa zuwa makaranta damar samun ilimi, tare da haɗa ɗaliban makarantun Alƙur'ani cikin tsarin ilimin zamani.
A saƙon da aka karanta a madadinsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na dawo da martabar ilimi a Jihar Kano.
Gwamnan ya ce:
Gwamnatin Kano ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen samar da dukkan abin da ake buƙata har sai an dawo da fannin ilimi zuwa matsayin da ya dace da shi.
Wannan karramawa da Kano ta samu a Majalisar Dokokin Birtaniya na nuna yadda amincewar ƙasa da ƙasa ke ci gaba da ƙaruwa kan gyare-gyaren ilimin jihar, tare da ƙara tabbatar da matsayin Kano a matsayin abin koyi wajen sauya fasalin ilimi a Najeriya da ma sauran ƙasashe.
Taron ya samu halartar ƙwararrun masana ilimi daga Birtaniya da kuma 'yan Najeriya mazauna ƙasashen waje, ciki har da Misis Hindy Mohammed, Dr. Amina Abubakar, Farfesa Paunile Dixon, da abokin bincikenta Dr. Steve Humble na Jami'ar Newcastle.
A nasa jawabin, Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar Kano, Sheikh Ahmad Tijjani Sani Auwal, ya bayyana cewa haɗa makarantun Islamiyya da tsarin ilimin zamani zai taimaka wajen ƙara bunƙasa ƙwarewar karatu da lissafi a tsakanin al'ummomin Kano.
Sheikh Ahmad Tijjani Sani Auwal ya kuma gode wa Majalisar Dokokin Birtaniya bisa ba gwamnatin Kano damar bayyana irin nasarorin da gwamnatin Gida Gida ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samu a fannin ilimi.
SBDT