10/10/2026
A daren yau, Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta sake cimma wani gagarumin nasara a ƙoƙarinta na tabbatar da tsafta da ingantaccen muhalli a Kano, inda aka girka wasu sabbin kwandunan shara na musamman domin hana zubar da shara a kan manyan titunan jihar.
Wannan mataki zai ƙara inganta tsarin kula da shara tare da ƙarfafa tsaftar muhalli a faɗin Jihar Kano.
Yana da matuƙar muhimmanci a fahimci cewa waɗannan kwandunan shara an tanade su ne domin masu wucewa a ƙasa, matafiya da sauran masu amfani da tituna su zubar da ƙananan shara. BA a tanade su domin masu shaguna da ’yan kasuwa su zubar da sharar kasuwancinsu ko ta gidajensu ba.
Muna kira ga masu shaguna, ’yan kasuwa, kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki da su yi koyi da wannan kyakkyawan mataki ta hanyar samar da kwandunan shara a wuraren kasuwancinsu da tabbatar da zubar da shara yadda ya kamata.
Tsaftace Kano nauyinmu ne baki ɗaya. Mu haɗa kai wajen gina Kano mai tsafta, lafiya da kyakkyawan muhalli.
Dr. Muhammad S. Khaleel
Manajan Darakta
REMASAB