01/06/2026
KCF Ta Karrama Ministan Gidaje Da Raya Birane Engr. Muttaqa Rabe Darma Da Lambar Yabo A Katsina
Kungiyar tuntuɓa ta dattawan jihar Katsina Consultative Forum (KCF) ta karrama ministan gidaje da raye birane Injiniya Muttaƙa Rabe Darma.
Ƙarramawar ta biyo bayan irin gudunmawar da kungiyar ta ce ta lura sabon ministan ya bayar wajen cigaban jihar Katsina
Taron karrama injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya gudana a ɗakin taro na Masaukin Baki na Hellside a lokacin lafiyar cin abinci da aka shiryawa Jakadun Nijeriya guda biyu 'yan asalin jihar Katsina inda 'yan uwa da abokan arziki s**a shaida ƙarramawar.
Kazalika injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya bayyana wannan karramawa a matsayin karfafa gwiwa musamman a ayyukan da s**a shafi al'umma kai tsaye.
Sannan ministan ya yi kira ga al'ummar jihar Katsina da su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya wajen cigaban da gina jihar Katsina da kasa baki ɗaya.
01/06/2026
Happy New Week to the Chairman GMTD, Engr. Muttaqha Rabe Darma.
May this new week bring you greater success, wisdom, good health, and outstanding achievements as you continue to provide purposeful leadership and service to humanity.
Wishing you a productive and blessed week ahead.
31/05/2026
Engr. Muttaqa Rabe Darma ya gwangwaje marayu da kayayyakin sawa da kudi domin rayuwarsu ta inganta a Katsina
Ministan gidaje da raya birane na Najeriya Engr. Muttaqa Rabe Darma ya kai tallafin kayan sawa da kudi ga wasu yara marayu masu rauni a gidan marayu da ke bayan babban asibitin jihar Katsina, ranar Lahadi 31, ga watan Mayun 2026.
Mataimaki na musammam ga ministan gidajen PA Gambo Garba shi ne ya jagoranci kaddamar da rabon tufafin sakawa ga marayu maza da mata a gidan kula da marayu na “Katsina Childrens Homes” a Katsina.
A jawabin Hon. Gambo Garba, ya ce Ministan gidaje da raya Birane Engr. Muttaqa Rabe Darma PhD, ya turo su gidan marayun domin su duba abinda s**a fi bukata wanda ya bada umurni a dinka wa marayun kayan sabbin kayan sawa
A cewar, Hon. Gambo Garba bayan samun kididdigar marayun sun dinka wa maza 21 shadda da yadi kala 2, sai mata 9, sun dinka masu atamfa da leshi kala 2, sannan kananan yara domin rayuwarsu ta inganta.
Wasu daga cikin ma'aikatan sun yi godiya ga Engr. Muttaqa Rabe Darma, bisa wannan tallafi da aka ba marayun domin taimakon rayuwarsu
A karshe Engr. Muttaqa Rabe Darma, ya bai wa ma'aikatan gidan marayu gudunmawar kudi kan yadda suke ɗawainiya wajen kula da yaran a gidan marayun.
31/05/2026
Ministan Gidaje da Raya Birane na Tarayya, Engr. Muttaqha-Rabe Darma, PhD, ya kai ziyarar gani da ido a aikin gina gidajen Renewed Hope Estate guda 250 da Gwamnatin Tarayya ke gudanarwa a kusa da Jami’ar Umaru Musa Yar’adua University da ke Jihar Katsina.
A yayin ziyarar, Ministan ya nuna rashin jin daɗinsa kan tafiyar hawainiya da aikin ke yi, inda ya buƙaci masu ruwa da tsaki da kamfanin da ke gudanar da aikin su ƙara himma da ƙwazo domin tabbatar da kammala aikin cikin lokaci da kuma bin ƙa’idojin inganci da aka gindaya.
Ya jaddada kudirin Gwamnatin Tarayya na samar da gidaje masu araha ga al’umma, tare da tabbatar da cewa dukkan ayyukan da ke ƙarƙashin shirin Renewed Hope Housing Programme sun kammala yadda ya kamata domin amfanin jama’a.
31/05/2026
Kirarin Engr. Muttaqha-Rabe Darma
Mai Kudin da baya Tsoron Talauci
A cikin wata daya kacal, yanata kawo togomoshi a Jihar Katsina. Munaso Al'ummar Katsina da Najeriya su fahimci: an aje kwarya a gurbinta.
Shi ba kudi ke matsalarshi ba. Jihar Katsina ita ce karkashin zuciyarsa. Kuma da karfin ikon Allah ba'a fara ba ma
Hakika, Engr. shi Masoyin Jihar ne na Asali
Saboda burinsa shine:
• In ya samo zai saudaukar
• Yanada kyawawan dabi’u
• talakawa ne gabanshi sune manufarshi da fafutikarshi
"Wallahi, Engr. bai taba samun kudi ya cire wasu ba — wai don gobe ya dauka, ko kuma don kar ya yi talauci."
Wallahi, ina ba ku tabbacin cewa:
Al'ummar Jihar Katsina za su yi farin ciki Insha Allah
Wannan rubutu an yi shi ne don ƙara girmama aikin Engr. Muttaqa Rabe Darma da kuma sanar da Al'ummar Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.
30/05/2026
Hon. Minister of Housing and Urban Development, Engr. Muttaqha-Rabe Darma, attended a ceremony organized in honor of Amb. Shehu Ilu Barde. The event brought together distinguished guests, community leaders, and well-wishers to celebrate his contributions and achievements. The occasion highlighted the importance of leadership, service, and commitment to national development.
30/05/2026
Samun Engr. Muttaqa Rabe Darma albarkace ga jihar Katsina - Inji Hon. Gambo Garba
Hon. Gambo Garba, ya ce bai tsammanin Aƙwai wani minista a Najeriya da ya kawo ma al'ummarsa ci gaba cikin ƙankanan lokaci a kasa da sati 2 kamar ministan gidaje da raya birane Engr. Muttaqa Rabe Darma.
A cewar, Gambo Garba Engr. Muttaqa Rabe Darma mutum ne wanda ya ginu akan taimakon al'umma wanda daga hawan shi ministan zuwa kawo yanzu ya kawo tsare-tsare na taimakon al'umma daban-daban a fadin Katsina
Katsina Reporters ta samu cewa, Gombo Garba ya fadi hakan a wajen taron bada jarin kudi ga mutane 100 masu ƙananan sana'oi a matsayin murnar nada PA na ministan gidaje.
Hon. Gambo Garba, shi ne mataimaki na musammam [PA] na sabon ministan gidaje Engr. Muttaqa Rabe Darma.
A ƙarshe, Gambo Garba, ya roƙi al'ummar jihar Katsina da su taya Engr. Muttaqa Rabe Darma da addu'a don sauke nauyin da Allah ya dora masa na jama'a.
By Mustapha S Galadima
30/05/2026
Mai Girma Ministan Gidaje da Raya Birane na Najeriya, Engr. Muttaqha Rabe Darma, ya tura wakilansa zuwa gidan marayu domin duba halin da suke ciki tare da jin irin taimakon da suke buƙata domin inganta rayuwarsu, kamar yadda kowane yaro ke rayuwa tare da iyayensa.
An gudanar da wannan ziyara ne ƙarƙashin jagorancin mai taimaka masa, Alhaji Gambo Garba, inda aka tattauna hanyoyin da za a tallafa wa marayun da kuma samar musu da kyakkyawar makoma.
Muna addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya saka musu da mafificin alkhairi, Ya ƙara musu lafiya, arziki da nasara a dukkan ayyukansu na alheri. Amin.