Sen. Abdu Soja Media Team

Sen. Abdu Soja Media Team

Share

Senator Abdu Soja Media Team

It's Official Page.

Photos from Sen. Abdu Soja Media Team's post 31/05/2026

Sanata Abdu Soja Ya Ƙarfafa Tattalin Arziki a Mazabar sa.

1. Rabon Motocin Bas 46

SANATA YAR’ADUA YA RABA MOTOCIN BAS 46 GA AL’UMMAR KATSINA TA TSAKIYA

A wani bangare na Shirin Tallafawa Al’umma na Naira Biliyan 1.9, Mai Girma Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua ya rabawa al’umma motocin bas guda 46 domin taimakawa matasa, kungiyoyi da masu sana’ar sufuri wajen bunkasa harkokinsu.

Wannan tallafi zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma rage matsalolin sufuri a fadin kananan hukumomi 11 na Mazabar Katsina ta Tsakiya.

2. Rabon Motocin Saloon 35

SANATA YAR’ADUA YA RABA MOTOCIN SALOON 35 GA WASU MATASA.

Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua ya rabawa wadanda s**a ci gajiyar shirin tallafinsa motocin saloon guda 35 domin inganta rayuwarsu da kuma samar musu da hanyoyin samun kudin shiga.

Tallafin na daga cikin shirin bunkasa tattalin arziki da Sanatan ke aiwatarwa domin inganta rayuwar al’ummar mazabarsa.

3. Rabon Motocin Asibiti 5

SANATA YAR’ADUA YA KARA KARFAFA BANGAREN KIWON LAFIYA DA RABA MOTOCIN ASIBITI GUDA 5

Domin inganta ayyukan lafiya da ceto rayuka, Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua ya rabawa cibiyoyin lafiya motocin daukar marasa lafiya (Ambulance) guda biyar.

Ana sa ran motocin za su taimaka wajen jigilar marasa lafiya cikin gaggawa musamman a yankunan karkara.

4. Rabon Motocin Hilux 3

SANATA YAR’ADUA YA RABA MOTOCIN HILUX 3 DOMIN AIKIN AL’UMMA

A kokarinsa na karfafa ayyukan ci gaban al’umma, Sanata Yar’adua ya raba motocin Hilux guda uku domin saukaka gudanar da ayyukansu.

5. Rabon Motocin Jeep 4

SANATA YAR’ADUA YA RABA MOTOCIN JEEP 4 GA WADANDA S**A CANCANTA.

A karkashin shirin Mega Empowerment, an rabawa wasu daga cikin wadanda s**a amfana motocin Jeep guda hudu domin bunkasa rayuwarsu da karfafa harkokin tattalin arziki.

6. Rabon Keken NAPEP 26

SANATA YAR’ADUA YA RABA KEKEN NAPEP 26 GA MATASA

Domin samar da ayyukan yi da rage zaman banza, Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua ya rabawa matasa keken NAPEP guda 26.

Tallafin zai taimaka wajen samar da hanyoyin dogaro da kai ga matasa a fadin mazabar.

7. Rabon Industrial NAPEP 13

SANATA YAR’ADUA YA RABA INDUSTRIAL NAPEP 13 DOMIN TALLAFA WA KANANAN SANA’O’I

Sanatan ya kuma rabawa masu sana’o’i da kungiyoyi Industrial NAPEP guda 13 domin saukaka jigilar kaya da habaka kasuwanci.

8. Rabon Sabbin Babura 150

SANATA YAR’ADUA YA RABA SABBIN BABURA 150 GA MATASA

A wani muhimmin bangare na shirin tallafinsa, Sanata Yar’adua ya rabawa matasa sabbin babura guda 150 domin samar musu da hanyoyin samun abin dogaro.

9. Rabon Babura Tuwarus 260

SANATA YAR’ADUA YA RABA BABURA TUWARUS 260 DOMIN INGANTA RAYUWAR MATASA

Mutane da dama sun amfana da rabon babura guda 260 wanda zai taimaka musu wajen gudanar da sana’o’i da samar da kudaden shiga dama harkokin yau da kullum.

10. Rabon Firiji 400

SANATA YAR’ADUA YA RABA FIRIJI 400 GA MATA DA MATASA

Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua ya rabawa mata da matasa firiji guda 400 domin tallafawa sana’o’insu da bunkasa harkokin kasuwanci.

11. Rabon Injinan Nika Dana Markade 400

SANATA YAR’ADUA YA RABA INJINAN NIKA DANA MARKADE 400 GA MATA DA MAZA.

Domin karfafa tattalin arzikin gida, Sanatan ya rabawa mata da maza injinan nika dana Markade guda 400 domin taimaka musu wajen gudanar da sana’o’insu da samar da karin kudin shiga.

12. Rabon Kekunan Dinki 410

SANATA YAR’ADUA YA RABA KEKUNAN DINKI 410 GA MASU SANA’A

A kokarinsa na bunkasa sana’o’in hannu, Sanata Yar’adua ya rabawa matasa da mata kekunan dinki guda 410 domin karfafa sana’ar dinki da samar da ayyukan yi.

13. Rabon POS Machines 100

SANATA YAR’ADUA YA RABA NA’URORIN POS 100 DOMIN HABAKA KANANAN KASUWANCI

Masu kananan sana’o’i sun amfana da rabon na’urorin POS guda 100 wanda zai taimaka wajen saukaka harkokin kasuwanci da hada-hadar kudi.

14. Rabon Wayoyin Hannu 160

SANATA YAR’ADUA YA RABA WAYOYIN HANNU 160 GA MATASA DA MATA

A karkashin shirin tallafinsa, Sanatan ya rabawa matasa da mata wayoyin hannu guda 160 domin karfafa amfani da fasahar zamani wajen kasuwanci da sadarwa na zamani.

15. Rabon Kekuna 100

SANATA YAR’ADUA YA RABA KEKUNA 100 GA DALIBAI NA MAKARANTU A KARAMAR HUKUMAR DANMUSA.

Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua ya raba kekunan hawa guda 100 domin saukaka zirga-zirga ga dalibai yan makaranta na yankunan karkara a karamar hukumar Danmusa.

16. Tallafin Kuɗi ga Mutane 150

SANATA YAR’ADUA YA BA MUTANE 150 TALLAFIN KUDIN FARA SANA’A

Baya ga kayan aiki da motocin da aka raba, Sanata Yar’adua ya bai wa mutane 150 tallafin kudi domin fara ko fadada sana’o’insu.

Wannan tallafi na daga cikin kokarin Sanatan na tabbatar da cewa al’ummar Katsina ta Tsakiya sun samu damar dogaro da kai da bunkasa tattalin arziki.

Sen. Abdu Soja Media Team.

27/05/2026

Eid al-Adha Message

In the name of Allah, the Most Gracious, the Most Merciful.

I extend my warmest congratulations and best wishes to the entire people of Katsina Central Senatorial District on the occasion of Eid al-Adha.

I felicitate with the people of Katsina senatorial district on this blessed celebration. I pray that Allah accepts our عبادات, and blesses us with peace, prosperity, and continued progress.

Eid al-Adha is a time of sacrifice, compassion, unity, and generosity. I urge us all to continue to uphold the values of peace, togetherness, and mutual love for the development of our communities and our state at large.

May Allah grant us the opportunity to witness many more Eids in good health, abundant blessings, and lasting peace.

27/05/2026

SAƘON BARKA DA BABBAR SALLAH.

Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Ƙai.

Ina miƙa saƙon taya murna da fatan alheri ga ɗaukacin al’ummar Mazabar Sanata ta Katsina ta Tsakiya bisa zagayowar Babbar Sallah.

Ina taya al’ummar ƙananan hukumomi goma sha ɗaya na mazabar mu — Katsina, Batagarawa, Rimi, Charanchi, Jibia, Kaita, Batsari, Safana, Dan Musa, Kurfi, da Dutsinma — murnar wannan lokaci mai albarka, tare da addu’ar Allah Ya karɓi ibadunmu, Ya sa albarka da zaman lafiya da ci gaba a tsakaninmu.

Babbar Sallah lokaci ne na sadaukarwa, tausayi, haɗin kai da taimakon juna tare da zumunci, Ina kira gare mu da mu ci gaba da rungumar zaman lafiya, haɗin kai da ƙaunar juna domin cigaban al’ummarmu da jiharmu baki ɗaya.

Allah Ya maimaita mana wannan Sallah cikin ƙoshin lafiya, yalwar arziki da zaman lafiya mai dorewa.

Barka da Sallah!

Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua.
(Mutawallen Katsina).

25/05/2026
Photos from Sen. Abdu Soja Media Team's post 25/05/2026

Sanata Abdu Soja ya aike da wakilan sa don jajanta ma Hon Bishir Mamman Dutsinma tsohon Dan Majalissar Dokoki wanda ya wakilci karamar hukumar ta Dutsinma bisa iftila’in gocewa da tsakewar kashi da yasamu.

Ziyarar karkashin jagorancin Alhaji Umar Farooq Ak sun mika sakon jajen Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua ga Hon Bishir Mamman, Hon Bishir Mamman ya bayyana godiyar sa ga Sanata da wakilan nasa.

Sen. Abdu Soja Media Team.

Photos from Senator Abdulaziz Musa Yaradua's post 25/05/2026
24/05/2026

Labari Cikin Bidiyo.

Kalli Yanda Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua ya halarcin zaben fidda gwani na dan takarar Shugaban Kasa karkashin Jamiyyar APC a Mazabar sa ta Kangiwa dake cikin karamar hukumar Katsina.

22/05/2026

Sakon godiya tare da ban gajiya Daga Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua (Mutawallen Katsina) Sanata mai wakiltar shiyar Katsina ta tsakiya kuma Dan takarar Sanata karkashin Jam’iyyar APC a shiyar Katsjna ta tsakiya.

Sen. Abdu Soja Media Team.

21/05/2026

Ya zama wajibi al'umma su gode ma Tinubu saboda ya gyara tattalin arzikin Nijeriya da tsaro - Inji Sanata Abdul-aziz Yar'adua

Haka kuma Audu Soja ya ce cire tallafin mai ya samar da kudaden shiga ga jahohin Najeriya.

Sen. Audu Soja ya fadi hakan a wata fira da ya yi da kafar sadarwa ta DCL Hausa

Want your business to be the top-listed Government Service in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Address


Katsina