Littattafan Hausa Novels

Littattafan Hausa Novels

Share

Nabude wannan page dinne domin kawo maku littattafai masu dadi. Dasa nishadi, nine naku (SULAIMAN SA

19/03/2021

((((((SALON SO))))))
((((((PART 25)))))))
:

Yana saukowa babban falon ya ji fitinan nan
kamshi jawahir mai har gitsa masa kwalkwalwa ya
yi hamdala ga ubangiji yayi godiya ga Allah da
jawahir ta dawo hannunsa
Bai ganta a babban falon ba don haka ya yi sallama
a nata falon ya tura kofar ya shiga. "Subhanallahi! Tsarki ya tabbata ga wanda ya
hallici wannan kyakyyawar budurwar yarinya sai
ka ce balarabiya. Anya ba aljanu ne suke
yaudararsa suna neman bude masa ido ba.?
"Me ya sa kika tafi wani wajen ba da izinin mijinki
ba har tsawon shekara daya? Kina ganin kinyi dai dai kenan? Ko kin manta aure k**e yi? Ya za ki da
dumbin zunubin tashin hankalin da kika sa mijinki
a ciki.?"
Ta marairaice fuska kamar za ta yi kuka don Allah
yaya kayi hakuri ba zan sake ba. Ya ce, "Shikenan
ba wani abu sai dai ki kiyaye gaba. Kin ga yanzu ba mu kadai ne a gidan ba kina tare da abokiyar zama
don haka ki kiyaye kin san ba na son hayaniya
bare abin da zai daga min hankali. Shiru ta yi ba ta
ce komai ba don ta san idan ta yi magana hawaye
ne zai zubo don wani dunkulallen abu da ya tokare
mata makogaro, ni na san ba komai ba ne sai kishi. Ya ce, "Ba ni break din na ci, "Ta mike tsam ta kai
masa gabansa ta durkusa tana hada masa shayin
ya yi kauri da madara, bonbita, neskofi, da
sauransu. Ta bude masa fulas din soyayyen dankali
ne da wainar kwai, sai gasasshiyar kaza da ta gasa.
Ya ce, "Je ki falo na ki dauko biredi. "Ta dan yi dum ya ce, "Ba ki ji ba ne? Ta ce, "Yaya matarka fa tana
saman?
Yace, "Ba komai je ki, ki dauko min ai bacci take yi.
Haka ta tafi kamar wadda kwai ya fashewa a ciki
shi dai yana tsananin kaunar jawahir yarinya me
tsananin hankali da biyayya ga saukin kai ga k*ma uwa uba ta hada komai da yake tsananin SO a jikin
mace.
Jawahir dai har ta hau sama ta sauko ba ta ga
matarsa ba. Ta shigo falon ta da siririyar sallamarta
ya amsa mata ta zo gabansa ta durkusa ta miko
masa, ya ce, "To zauna mu sha ta girgiza kai, ya hada kai tare da cewar ba na son gardama zauna
mu sha.
Ta zauna s**a fara birek Haidar danna birek dinsa
yake yi yana ci sosai don yaushe rabon da ya yi
break ma a gidansa tun jawahir tana nan.
Ita kuwa a yangace ta ke ci kamar mai cin magani ya kalle ta ya ce, "Ke ba za ki bude baki ki ci ba ne?
Wato kin fa dawo za ki rinka kin cin abinci ki k*ma
ramewa ko? Can da yake suna tursasa ki ki ci ai ga
shi nan kin yi kiba to ni ma na daina kyale ki dole
na matsa miki ki ci ki koshi. Haka ya takura ta ta ci
da yawa. Daga nan ya fita ya tafi office cikinsa da koshi.
Jawahir kuwa ta rufe kofar falonta ta yi zamanta a
dakinta. Dan haka ba ta san wainar da suke toyawa
ba. Da ta ji yunwa ragowar birek dinsu na safe ta
dauka ta ci ragowar kazar da Yogourt roba biyu ta
ji ta koshi kuwa. Shi kuwa Haidar a office duk ya kasa samun sukuni
ganin yanda jawahir ta koma. Karfe shida ya tashi
daga office ya yi gida. Ya yi sallama falon shiru ba
kowa bare a amsa masa. Ya haye samansa ya tube
ya yi wanka ya dauro alwala ya yi sallar magariba
ya sako kananan kaya ya sauko kasa ya shiga dakin Kausar.
Tana tare da 'yan aikinta suna aikin bautarsu na
matsa mata kafa wannan abu yana konawa Haidar
rai.
S**a yi gaggawar fita daga dakin. Ya zauna tare da
cewar, "Ina abincina.? Ta ce, "Na ga ba ka cin abincin masu aiki shi ya sa
ban ajiye maka ba, ya ce, "Okey kin kyauta. "Ya
mike ya fice kawai ya shiga dakin jawahir shiru sai
dai ya ji motsin ruwa a bandaki wanka take kenan,
don haka ya nemi gefen gadonta ya kishingida
yana shakar daddadan kamshin da dakin ya ke yi. Jawahir da ba ta san da mutum a dakin ba ta gama
wankanta ta dauko tawul iya gwiwa ta fito gashin
kanta duk ya bazu ya manmanne mata a fuska ta
bude kofar tolet din ta fito. Tana 'yar wakarta ta
nufi gaban mudubi. Subhanallahi! Ai tuni hankalin
Haidar ya so gushewa don ganin kyakkyawar kirar jawahir, jiki mulmul da shi ga shi jajir santsi yake yi
da sheki, santala santalan cinyoyinta kamar na
Baturiya.
Ta zauna gaban mudubi ta fito da mayukanta da
hadin turarukanta ta fara mulke jikinta. Sam ba ta
kula da wani a dakin ba tana shirin yaye tawhul din don shafe jikinta sai ta hango kamar mutum ta
mudubin tuni ta razana ta yu kara cikin
dimautacciyar murya da takaicin rashin kwancewar
tawul din ta ya ce, "A'a jawar meye haka?
Ta ce, "To Yaya ai tsoro na ji ban san ka shigo ba, ya
ce, "Okey sorry, sorry je ki ki gama shirinki. To k*ma sai ta kasa shirin a gabansa sai daya dakin
ta shiga ta karasa shirinta ta fito cikin doguwar riga.
Tsarki ya tabbata ga Allah, wannan yarinya da
kyau take ga iya diresin kamar aljana. Abun da
Haidar yake fada kenan a zuciyarsa. Har ta zo
gabansa ta durkusa ta ce, "Sannu da zuwa yaya." Ya ce, "Yauwa jawahir kin ci abinci? Ta girgiza kai
ya ce, "To me kika ci.?
Ta ce, "Yogourt da ragowar naman daxu. Ya ce,
"Shi ne zai rike miki ciki? Me ya sa k**e son sakaci
da cikinki ne?
Me ya sa baki girka kin ci ba.?" Ta ce, "Ai gani na yi ba ni kadai ce a gidan ba.
To in ban da abinki jawahir ke da gidanki sai an
girka an ba ki? Ke da na san ki da kyankyami, za ki
rinka cin abincin me aiki ne?" Ta girgiza kanta, ya
ce,
To kin gani ki rinka girkinki kina ci kin ji ko.
Yanzu me za ki ci, ko za mu fita muje mu sayo wani
abin ne ko k*ma mu je gidan abinci.
Ta girgiza kai, "A'a zan girka wani abu yanxu
Ya dube ta ya ce, "Dare be yi miki ba. Ta ce, "A'a ba
komai. Tun da ta soma magana yake jin wani abu, zil-zil yana tsarga masa don jin dadin muryarta da
shaukin begenta. Ya mike ya fita jikinsa a sanyaye
kamar wanda kwai ya fashewa a ciki ya fito ya hau
samansa sai ya tarar da Kausar a kwance a kan
gadonsa tana nishi. Ya isa kusa da ita da saurinsa
ya ce, "Lafiya?" Menene ya faru? Ba yanzu na barki a dakinki ba. Ta ce, "Wallahi fama nake yi da ciwon
mara tun safe daurewa kawai na ke yi ka daure ka
kaini asibiti yanzu."
Haidar ya ce, "Yanzu ya dace mu fita asibiti mu bar
jawahir ita kadai a gidan? Kausar ta ce, "Haba
Haidar me yake damunka ne me zai same ta, ba ga masu aiki nan a gidan ba, ko ka fi so ni na kwana
ina murkususu?"
Ya ce, "To shikena tashi muje. Lokacin da s**a fito
don tafiya sannan jawahir ta fito falon za ta shiga
kicin wannan shi ne karo na farko da jawahir ta ga
Kausar ita ma Kausar ta ganta. Ba su yiwa juna magana ba sai Haidar da ya ce zamu fita yanzu
zamu dawo.
Jawahir ta shiga kicin kamar ba ta ji me yake cewa
ba, s**a fice jawahir ta zauna a babban falo ta
kunna kallo, salkamar da taji ce ta sata saurin
juyowa. "Lalala Bilki yau ke ce a gari?" Gaskiya ba ki da alkawari, ni na za ta ma kin manta da ni."
Bilki ta ce, "Haba jawahir ya zan yi na manta da ke,
kin san tun ranar da muka zo nan gidan Haidar ya
kore mu nake jin tsoron kada nazo na jawo miki
wata fitinar. To sai da na ji labarin aurensa na so na
zo sai na ji tsoron kada ya cire min kafa daya shi ya sa na hakura na fasa zuwa.
Jawahir ta ce, "Yanzu ya aka yi kika zo?
"Uhm ke dai bari, tare muke da direba munje gidan
kawar Hajiyarmu kusa da ku ne na ga ba zan iya
wuce gidanki ba.
Jawahir tayi murmushi, "Amma gaskiya na gode na k*ma ji dadin zuwanki, don akwai labari da labarai
ma sai dai ga shi dare ne da za ki daure da kin zo
min da rana mun wuni muna hira.
Bilki tayi ajiyar zuciya ta ce, "Kina ganin in na zo
babu wata matsala ko Haidar yana nan."
Jawahir ta ce, "Ba komai wallahi ba zai ce miki komai ba.
To shi kenan jawahir na fita kin ga dare ya yi sai na
zo din
"Okey Bilki na gode don Allah ina sa ido kada fa ki
ki xuwa."
"Insha Allahu zan zo" Tayi sallama ta tafi. Jawahir ta soya indomie da kwai ta gasa masa kifi
ta hada masa lemon kwakwa da madara ta zuba a
jug ta cilla masa kankara ciki ta jere komai a kan
tebir din falon ta shiga sashenta ta ci na ta ta watsa
ruwa ta wanke bakinta ta je ta yi kwanciyarta. Sai
goma na dare su Haidar s**a dawo. Kausar ta wuce dakinta Haidar kuwa ya nufi tebur din da
abinci yake don yunwar da yake ji tun break din
safe da ya yi a dakin jawahir.
Ya bude komai ya ci ya yi kat, ya rinka shan lemon
kwakwar nan yana nishadi a kasan zuciyarsa
kuwa sai shiwa jawahir albarka yake. Da ya gama ya murda kofar dakinta yau ma a rufe gam, ya
koma dakinsa yau ma ya kwanta yana murkususu
da ya rufe idonsa kyakkyawar surar jawahir yake
gani. Ga wata muguwar sha'awarta da tayi masa
mugun kamu haka ya rinka juyi yana murkususu.
Sai da asuba ya tashi ya yi alwala ya yi Raka'atainil Fajri ya yi ta karatun Alkur'ani ya yi addu'arsa ya
shafa. Ya dade yana lazimi sannan ya sauko falon
kasa ya zauna ko zai ga jawahir ta fito ya samu ya
ganta ko zuciyarsa ta lafa da tsananin radadin
kaunarta.
Ya yi sa'a kuwa ta bude kofarta ta fito tana sanye da abaya da karamin farin hijab, da ya sha adon
bakin les, tana rike da carbi a hannunta ta yi kyau
kamar ita ta yi kanta.
Duk motsin da tayi sai komai na jikinta ya motsa.
Yanda jikinta yake girgiza shi yake dada motsawa
da Haidar sha'awarta. Jawahir ta yi mamakin ganinshi a falon, don haka
ta karasa gabansa tayi saurin xubewa ta gaisheshi.
Ta mike ta nufi kicin idonsa na kanta.
Ya ce, "Jawahir" Ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya
ce, "Don Allah idan break za ki hada ki hada da
mu."(HMMM GASKIYA JAWAHIR AKWAI HAKURI DON NA TABBATA A IRIN KISHI NA MATA BA KOWACCE XATA IYA GIRKI TA BAWA KISHIYAR DA ITA BA XATA YI BA).

17/03/2021

(((((((SALON SO))))))
(((PART 21 TO 24)))):
:

Bangaren Kausar kuwa kullum cikin yowa Haidar
waya take safe, rana, yamma da dare ma ba ta bar
shi ya huta ba kan maganar aurensu tun yana boye
mata yana cewa ta jira shi har dai ya fito ya gaya
mata gaskiyar batun matarsa. Amma ya ba ta
hakuri da ta jira iyayensu su dan samu nutsuwa sai ya tada maganar su zo.
Amma da ta kai ta kawo yau da Kausar ta tayar da
hankalinta sosai don gani take yi kamar Haidar din
sake subuce mata zai yi a karo na biyu, ganin
yanda ta samu kanta ne ya sa Haidar ya je yake
tuntubar mahaifinsa da zancen. Abbansa ya ce, Yanxu Haidar ba za ka hakura da
auren nan ba, kana kallon maganar nan ce ta tayar
muku da rigima ga shi ba a san inda 'yar uwartaka
take ba ko?
Haidar ya ce, Abba ka tausaya min mana, yau
shekarar jawahir daya kenan da barin gidan nan. Abba kana kallon kullum ina hanyar gidan nan
don cin abinci ni ba na iya cin abincin waje bare na
rinka zuwa Otal ina ci. Abba ba ka tausaya min na
samu na yi auren nan ko ni ma na samu nutsuwa a
gidan?
Abba ya ce, "Yanxu kana ganin idan ka yi aure surutun mutane 'yan uwa da abokanan arziki ba za
su dinga ganin ba ka damu da batan matarka ba?
Ka ga abin zai zama abin surutu ko?
Haidar ya ce "Wallahi Abba jawahir tana hannun
inna don ita ta boye ta.
Ya ce, "Ka tabbata? Daga bakin wa ka ji? Wallahi Abba migadin gidan Inna na ritsa na ce ko
ya gayan gaskiya ko na debo masa 'yan sanda shi
ne yake gaya min tana gidan Inna to idan na je wa
da Inna maganar sai ta koro ni, ni dai ina ganin
gwara na yi auren in ta ga na yi auren za ta dawo
da ita. Abba ya ce, "To shi kenan Allah ya zaba abin da ya
fi alheri, zan je wajen Alhaji ibrahim din duk abin da
muka tattauna sai ka ji. Ya ce, "To Abba na gode.
Ya mike ya tafi.
Abban Haidar ya samu Dadyn jawahir yake gaya
masa yan da s**a yi da Haidar din, Alhaji Ibrahim ya ce, ai ni tun da na ga hankalin Inna bai tashi ba
na san cewa jawahir tana hannunta. To na sha
tuntubar Aisha a kan maganar, to idan a ka bar
maganar ai anyi zalinci k*ma an shiga hakkin
Haidar, shekara guda mace ta gudu ta bar ka k*ma
a hana ka yin aure, ai da zalunci, ni dai kawai ina ganin in Allah ya kai mu jibi mu je gidansu yarinyar
a gama maganar komai Haidar ya samu mata kawai
Lokacin da s**a je Abuja gidan kaninsa Alhaji
Aminu s**a sauka tukunna sai da s**a huta s**a
samu nutsuwa sannan s**a dinguma har Alhaji
Aminu zuwa gidansu Kausar. Sai bayan tafiyarsu sannan jawahir ta dawo daga
makaranta.
Antinta take bata labarin zuwansu Dadynta,
Jawahir gabanta ya fadi, "Lafiya kuwa Aunty.? "Eh
to, wallahi ban sani ba don sun tafi tare da Ankul
dinki k*ma be gaya min inda za su je ba ko dalilin zuwansu ba.
Jawahir ta ce, "To Allah ya sa dai ba ganowa s**a
yi ina nan ba. Amin da 'yata, don ba na so a raba ni
da ke. S**a yi dariya.
Gidan su Kausar an yi wa su Alhaji kyakkyawar
karba inda iyayenta s**a nuna karamci da dattako. A lokacin mahaifinta ya ce ya yanke ranar aure sati
biyu masu xuwa kawai nan fa a ka yi ta murna ana
sa musu albarka. To su Alhaji su daga nan s**a
hawo jirgi s**a juyo gida shi k*ma Ankul din ya
koma gida.
Suna zaune da matarsa a falon suna tatraunawa jikin maryam duk ya yi sanyi da jin abin da ya
kawosu, Alhajin Abuja. Jawahir ta shigo falon tare
da yin sallama ta tafi kusa da Ankul dinta ta zauna
dab da kafarsa a kan kafet ta ce, "Ankul barka da
dawowa.
"Yauwa 'yata sannu "Ankul me ya kawo su Dady? Ko sun san ina nan ne?
Ya girgiza kai, "Dady bai san kina nan ba kawai
abin da ya kawo su ne, shine na yi musu rakiya.
Ankul Dady bai tambayeni ba?
"Ai bai san kina nan ba ne shiyasa.
"Ankul ko dai maganar auren Haidar ce ta tashi s**a zo s**a gaya maka?"
"In ban da abinki idan auren Haidar ne ai sai su yo
min waya ba sai sun zo ba ko?
"Eh to, haka ne Amkul'" ya ce, "Kwaso littattafanki
mu gani, "Ta mike ta nufi dalinta.
***** ****** *****
Lokacin da s**a isa gida s**a shaidawa Haidar
halin da ake ciki, a satin s**a hada hada kayan lefe
da komai da komai mata s**a kai, duk wannan
halin da ake ciki hankalin Haidar yana kan jawahir
don haka ya je ya shirgo mata kayan fadar kishiya akwati uku hadaddun kaya na gani na fada, don
tsadaddu ne a ciki ya ai ka wa Inna ya ce a gaya
mata tun da ta rike masa mata matarsa ta hana shi
to ga kayan fadar kishiya ne don ba a gaya musu
da baki ba. Inna ta karbi kayan ta samu waje ta
adans su. Biki ya zo bangarensu Kausar sun sharyawa bikin
don kalolin fatin da za a yi da komai da komai
Kausar ce ta bude bakinta ta yi ta hidimarta ba ta
jiran ango don ta san halinsa auren ba dada shi ya
yi da kasa ba, ta yi hidima da bidirinta. Fati daya
kawai Haidar ya je shi ma, sai da ta dame shi da magiya sannan ya daure ya je.
Amarya ta tare a gidan angonta Haidar. Babban
falon gidansa na amfanin kowa da kowa ne, a
falon akwai kofa da take kallon gabas ita ce in an
bude an shiga sashen jawahir da katon falo da
dakuna uku a ciki, sai toilet, kicin da suke a ciki. To idan an dawo falon akwai wata kofar da take
kallon yamma wato tana kallon kofar bangaren
jawahir to ita ma in ka shiga katon falo ne da kicin
da tolet shi Amarya Kausar ta shiga, to a tsakiyar
babban falon bene ne wanda za ka hau ka je
turakar megidan, shi ma falon falo ne, da ya kushi dakuna biyu na bacci da tolet da kicin, sai wata
kofa da za ka bi a saman dai, shi k*ma makeken fili
ne da aka kayatar da shi aka yi masa rumfa don
hutawa, to nan saman shi ne na megida Haidar.
Zama ya yi dadi tsakanin Ango da Amarya sai dai
sabanin halayya da ta zo bamban ta ango da amarya, don ita Kausar ta samo masu yi mata aiki
har mutum uku ta cika masa gida da mutane ke
nan, shi da yake dan hutu ba ya son hayaniya, to
amma duk dawowar da zai yi zai tarar da Kausar
uwar lalaci a mike a doguwar kujera ko kan kafet
masu aikinta suna yi mata tausa, wani karin abin haushi wai ba ta iya girki da kanta sai dai me aiki ta
yi musu wannan dalili shi yake hana shi cin abincin
gidan, an gudu ba a tsira ba kenan, don kullum sai
ya biya ta gidansu ya ci abinci
Karin abin da yake bawa Haidar Haushi da Kausar
wai gadon da s**a kwanta sai dai ta kirawo me aiki ta gyara, wai ina abubuwan da jawahir take
sanya musu a gidan da dakunansa suke kamshi
ne, duk yanzu wannan kamshin mai dadi babu. Shi
wai shi yaya zai yi ne ya dawo da jawahir dinsa ne,
ko don lafiyayyen girkin da take yi masa mai dadi
ga ladabi da biyayya, duk yanda ya bata mata rai ba za ta fasa yi masa girki ba ko ta ki gaishe shi, ga
shi ya yi auren wayayyiya wadda ta yi karatu a
waje amma babu biyan bukata.
Don zamansa da tatsitsiyarsa ya fi sau dubu dari,
duk hanyar da ya bi don Inna ta dawo masa da
jawahir ya bi amma magana daya take gaya masa ita ma ba ta san inda take ba.
Lokacin da jawahir ta ji labarin auren Haidar ta yi
kuka sosai ta tashi hankalinta har sai da Inna ta zo
Abuja don rarrashinta. Don lokacin Ankul dinta
yana legos. Jawahir kuka take kamar rainta zai fita
Inna kuwa sai sai rarrashinta ta ke yi tana bata
hakuri jawahir ta ce, ni ba wani abu ne ya sa ni kuka ba irin yanda ya wulakanta ni ya yi aure kin
ga ya sake nunawa duniya cewar bai damu da ni
ba kenan. 'Inna ta tausayawa jawahir don ta
fuskance ta kishi ne yake damunta.
Inna ta ce, "Ki yi hakuri idan kina so ma yau sai na
mayar da ke gidanki. "Da sauri jawahir ta d**o kai tare da saurin katse Inna, "Haba-"Haba Allah ya
sawake ai sai ya ga na damu da shi ne ya sami
hanyar da zai k*ma wulakanta ni.
Inna ta ce, in dai wannan k**e ji kwantar da
hankalinki domin kuwa yanzu Haidar ta damu
dake wanda ba kya zato, auren nan da ya yi ya yi shi ne don na yi fushi na dawo masa da ke ne, ta ba
ta labarin yanda hankalin Haidar ya tashi na
rashinta da yanda a kayi auren har kayan fadar
kishiyar da ya kai mata da irin korar karen da take
yi wa Haidar din, ko ba komai in kalaman Inna ya
sanyayawa jawahir zuciyarta har ta ji tana sha awar ta koma gidan Haidar ko dan ta ga wanne irin zama
suke yi da Amaryar ta sa.
Jawahir ta ce, "Shi kenan Inna ba komai Allah ya
kara rufa asiri.
Kwanan Inna biyu a Abuja ta juyo zuwa gida,
Maryam ta ce da jawahir kada ki damu diyata, ni na san shirin dana yi wa jikinki kowanne namiji in dai
ya dandana ki to ba ba zai iya kusanta ki da wata
mace ba, ni na fada miki haka k*ma ki hakura ki
koma gidan Haidar ko don ki ba ni labari gaba,
idan ya dandani zumarki. Jawahir ta ji kunya ta
mike da gudu ta bar wajen. Bayan Inna ta koma gida washegari ta nufi gidan
danta Alhaji Ibrahim mahaifin jawahir, su momy da
Abba Nasir zuwa su Auwal da Sani sun yi murna da
ganin Inna gida ya rude a na ga Inna ga Inna. Inna
ta zauna cikin jikokinta ana wasa ana dariya Momy
kuwa tana ta hidimar kawo mata ababan ci da na sha. Momy ta zauna s**a gaisa Inna ta ce,
"Maigidan kuwa yana nan.? Momy ta ce, "Eh yana
nan bari na yo miki magana da shi."
Momy ta samu Dady rigingine a kan gado yana
kallon sili da alamu tunani yake yi, Ta yi sallama tare
da cewa, "Barka da hutawa. Ya amsa da yauwa: Inna ce ta zo take son magana da kai. "Ya mike
zumbur ya ce, "To gani nan fitowa.
Ya zo ya durkusa har kasa ya gaida Inna, ya ce
"Inna da kanki kika taho maimakon ki aiko na zo.?
Ta ce, "Kamawa ta yi daman na zo a kan maganar
yaran nan ne, ya ce, "Wanne yara?" "Ta ce, "Wanda ka hada auren dole yanzu k*ma
kuka je kuka yi masa auren da yake so, ita kun
hana ta wanda take so ta mutu kenan ko.?
Ya ce, "Inna Allah ya ba ki hakuri wallahi ba haka
ba ne."
Dady ya ce, "Don Allah don Annabi Inna ki yi hakuri kada ki yi haka ba mu san abin da auren
nan ya kunsa ba, kada mu yi wa Allah shisshigi a
lamarinsa.
Yanxu ki yi hakuri ki dawo da jawahir nan gidan
gobe sai na sa a mayar da ita gidanta.
Inna ta katse shi, "Kana nufin a mayar da yarinyar ya ci gaba da wulakanta ta ko?
"Wallahi Inna ni na san ba zai wulakantata ba, in
kika yi la'akari da yanda ya gigice da batan jawahir
din. Inna ai kun hora shi ya horu ba zai sake ba.
Inna 'ya 'yan nan duk namu ne wa za mu ki a
cikinsu.? Duk wanda za ta aura ai ba kamar Haidar din ba ko Innata?
Ta ce, "To shi kenan ai kokarinka ni ma na fi son a
karfafa zumunci. "Yauwa Innata yanxu ina jawahir
dina?
Tana can gidan kawunta. Dady ya rike baki "Wanne
kawun nata? "Tana da wani kawunne bayan Auta Aminu?" Alhaji ya ce, "Ikon Allah yanxu duk
binkicen nan da muka yi ta yi tana Abuja.?
Sallamar Haidar da Abbansa ne s**a shigo nan fa
Abban ya nufi Innar ya durkusa gaban Inna yake
gaishe ta, "Haidar kuwa gaban Dady ya je ya gaishe
shi, shi ya ki kallon Inna. Dady ya ce, "To ni na amsa gaisuwarka ba ka gaida
uwata ba.?
Haidar dai ya yi shiru bai ce komai ba bai k*ma kalli
Inna ba. Abba ya ce, "Ai yanzu ma shi ya je ya taso
ni dole har da kukansa shi fa sai an nemo masa
matarsa jawahir. Tun sallar la'asar ya tashi daga office ya je ya sani a gaba ga shi har bayan issha ya
ki tafiya gidansa shine na ce ya zo mu je wajenka
ko za a sami wani dan labari."
Inna ta ce, "Daman abin da ni ma ya kawo ni kenan
na zo a karbo min takardar sakin jikata ita ma ta je
ta auri wanda take so." Haidar ya yi saurin tasowa ya rike kafar Inna don
Allah don Annabi Inna ina jawahir take.?
Ta ce, "Ina
ruwanka da inda take ba kayi aurenka ba, to ka ba
ta takardarta ita ma ta auri wanda take so."
Haidar ya ce, "Don Allah don Annabi Inna ki yi hakuri ki yi min rai ki dawo min da matata wallahi
zan kula da ita ba za a k*ma samun kuskure ba.
"Inna ta ce, "A'a, ka je dai ka rike matarka ita ma sai
ta samu wani.
Haidar ya ce, "Ki rufamin asiri "Inna wallahi ko
cewa kika yi sai na saki Kausar za ki dawo min da jawahir sai na sake ta, don ni jawahir ta fiye min
kowace mace.
"Inna ta ce, "Ni da kake fushi da ni ba ka kula ni. Ya
yi saurin cewa, "To yi hakuri mu shirya don Allah
Inna jawahir tana ina.?
Inna ta ce, "Jawahir tana Abuja gidan kawunku tun washegarin ranar da ka koro ta daga gidanka na
tura ta can. "Tuni Haidar ya mike ya nufi bakin
kofar waje.
Abbansa ya ce, "Haidar ina za ka ne? Ya ce, "Abba
Abuja zan tafi yanzu."
Dady ya ce, "Ba ka da hankali ne ka dubi lokaci fa yanxu karfe tara ka baro matarka a gida ba ka
gudun hakkinta, ka yi hakuri ka koma gidan na yi
wa kawun naku waya gobe za su taho a jirgi insha
Allahu a gobe za a dawo maka da matarka."
Ya rissuna ya karayi musu godiya sannan ya tafi
gidansa cike da nishadi. Daga nan su ma s**a gama tattaunawa a tsakaninsu Inna direbanta ya
maidata gida. Abba ma ya nufi nasa gidan.
Washegari sha biyu na rana a Kano ta yi wa Ankul
da Aunty da jawahir da ma tun goma na safe
kannan Momy s**a tafi gidan Haidar don wankewa
jawahir kayanta tare da kade mata kura s**a share mata sashinta s**a gyara komai.
Dady da Momy sun yi mamakin ganin yanda
jawahir ta girma haka ta kara kyau da haske kamar
ba ita ba. Yaya Abba dai da Nasir sai da s**a yaba
kyan nata.
Da yake Inna ma ta zo nan dai aka hadu da Inna da Ankul da Dady da Momi da Anti Maryam a ka yi ta yi
wa jawahir fada da nasiha yanda za ta zauna da
mijinta da kishiyarta lafiya, ki ci gaba da yi wa
mijinki ladabi da biyayya kada ki yarda wata rigima
ta k*ma hada ku da mijinki sai mun saba miki.
Gaba daya k*ma s**a yi ta sama ta albarka. Anti Maryam ta ja ta daki ta dada yi mata bayanin yanda
za ta yi amfani da magangunnan da ta hada mata.
Da magariba s**a raka ta gidan mijinta kamar
sabuwar Amarya. An dai sake yi mata fada da
nasiha daga nan kowa ya fashe ya barta.
Ta shige sashenta ta kuwa garkame kofa sai karfe goma na dare Haidar ya shigo gidan. Dakin Kausar
ya shiga ya same ta a mimmike a gado ya zauna a
gefenta ya tambaye ta jawahir kuwa ta dawo?
Ta ya mutse fuska tare da tabe baki kai da ka je ka
dawo da ita ba ka san ta dawo ko ba ta dawo ba
bare ni da ban san ta ba, ko na taba ganin ta ne? Be k*ma ce mata komai ba ya yi tolet don inda
sabo ya saba da rashin ladabi na Kausar. Da ya
gama shirnsa ya nufi dakin jawahir sai ya ji shi a
kulle sai ya haye samansa ya yi dai-dai a gadon
bacci.
Har ya fara bacci ya ji shigowar Kausar ta bi shi gadon s**a kwanta. Da safe jawahir ta riga su tashi
don haka ta hada birek dinta iya wanda za ta ci ta
gyara babban falon nan da dakunanta kamar
yadda ta saba ta turare su kamshi ya wadaci ko ina
ta shiga ta tsala wankanta da kwalliyarta 'yar
ubansu. Shadda ganila ta saka wadda ta sha dinkin surfani
duk bulu da yalow da yake kwambineshin ce, ta
sha a don gwal fuskar nan tata sai sheki take tana
shainin. Ta zama cikakkiyar mace sosai kirjinta
kamar ya fashe don cika. Jikinta kuwa wani fitunan
nan kamshi ne yake tashi kamar an yi barin turare a jikinta. Ta fito falonta ta zauna, ba babban falo ba.
Ta dauki break dinta za ta fara ci kenan ta jiyo taku
an yo sashenta.
Haidar har ya tashi ya yi wanka ya gama shirnsa
cikin kayatacciyar shiga ta alfarma kamai yanda ya
saba, amma gimbiya Kausar ana gado a kwance ana ta sharar bacci.

14/03/2021

(((((((SALON SO)))))))
(((PART 19 TO 20))))
HAIDAR ya kasa samun nutsuwa dole ya nufi gidan abokinsa Faruk don yanke shawarar da za ta fisheshisu. Yana zaune a falo Faruk ya hada kai da guiwa yana ta tunani tare da karanta wasikar jaki. Faruk ya shigo falon tare da yin sallama. Bai jira an amsa sallamar ba don ya san ba zai samu ba ya karaso ya dafa kafadar Haidar ya ce, Me yake faruwa ne da kai aminina? Wace matsala ce k*ma take kokarin danno maka kai ne? Kai da za ka yi auren ke ce raini. Ya ce, "Kyale ni Faruk abin duniya duk ya dame ni, ko ka san jawahir ta gudu ban san inda ta nufa ba. Faruk ya dafe kirji ta gudu fa ka ce? Me ya hada ku, ko na ce me ka yi mata? "Uhm kai dai a yi sha'ani, wai daga na yi maganar aure zan yi sai yarinya ta gudu. Faruk ya ce, "Ai madallah ka ga irin abin da nake jiye maka ko, to ai ga irin ta nan yanxu sai ka je ka bunciko ta a duk inda take. Haidar ya ce, "Wallahi ni dai ina zaton tana gidan Inna don mota ta da ta dauko ta taho da ita, na ganta a gidan Innan. Sai dai amma Innan ta kafe ta ce jawahir din ba ta gidanta. Faruk ya ce, Ka ga taso mu kaje kawai mu shammace ta ba tare da munyi sallama ba mu shiga kawai in tana ciki za mu gan ta. S**a mike s**a yi gidan Inna Haka s**a danna kai falon Inna babu sallam abun mamaki ba jawahir sai Inna da ta yi zumbur za ta tashi ta ce ni har kun tsorata ni lafiya kuka shigo min haka babu sallama? Faruk ya durkusa yana gaishe ta Haidar kuwa zubewa ya yi a kasa yana yi wa Inna magiya inna don Allah don Annabi Inna ki taimaka ki fito min da jawahir. Inna ta ce, Haidar me kake fada ne? Ni na san inda jawahir take ne? Faruk ya ce, "To ai ni abin da ya fi ba ni mamaki ya a ka yi motar ta zo nan gidan, "Inna ta ce, "Ni dai ina zaune aka aiko min da mukullin motar na ajiye na zata ma ko tare suke da Haidar din motar ta lalace musu s**a ajiye ta, su je su dawo. Ta mike ta shiga dakinta ta fito ta ce ga mukullin motarka nan kada ku sake zuwar min idan ba jikata kuka gano min ba. Haidar cikin marairaita kamar zai yi kuka ya ce, "To yanzu Inna ya za a yi da neman jawahir din.? Cikin fada ta ce, To ya za a yi kuwa? Da ka rike ta hannu bibbiyu ai da haka ba ta faru ba ko? Yanxu da ka yi sakaci da ita ta bata ai ko wa sai ya huta. A dauki yarinyar nan cikin girma da mutunci 'yar uwarka ta jini a baka amma ka rinka wulakanta ta. Ya yi saurin cewa, "Wallahi Inna ba wulakantata nake ba wai don kawai na ce, zan kara aure shi ne ta yi tafiyarta. Inna ta ce, "Uhm ai ka ga yanzu ta bar maka filin gidanka ka fi sakewa kai da Amaryar taka sai ka je kai ta yo auren. Faruk ya ce, "Inna hakuri za a yi in dai an san inda take din a fada mana. Ta ce, "To ban sani ba ku tashi ku ba ni waje. **** ****** ****** Maganar jawahir kuwa tana gidan Ankul dinta ta dage da karatu don makaranta biyu zan ce take yi. Tana zuwa jami'a yayin da k*ma Ankul dinta ya daukar mata lakcara guda yake dada tunasar da ita da nusar da ita halayyar dan Adam, yanda ake iya zama da su sannan yana koya mata dabaru na iya kasuwanci da yanda za ka sarrafa kudi duk kankantarsu don juya su. Ta bangaren jawahir kam ma iya cewa Alhamdullihi, don komai a ka gaya mata ya zauna a kwalkwalwarta kenan da yake yarinya ce me kaifin basira da kokari. Jawahir ta gama nazarin abun da aka yi musu lakca a yau ta mike a gajiye ta shiga toilet ta yi wanka ta gama shirinta ta fito falo ta samu Auntynta a zaune. Maryam ta kalle ta tayi murmushi, "Tubar kallah 'yar gidan Ankul ba dai kyau ba, zo ki zauna na dora miki inda muka tsaya don so nake yi ki mallake Haidar tsab yanda ya raina ki yake kiranki da tatsitsiya ko kwaila to yanzu ki zame masa dan hakin da ka raina. Yanzu abin da zan fara miki da shi shine zan koya miki kissoshi kala-kala don haka dauko littafi da biro ki rubuta komai don gudun mantawa. (Saboda haka idan kuna so nima na fada muku to kowa ya/ ta dauko biron shi/ta domin nima saida na rubuta sannan na iya kawo muku badon haka ba........hmmm. Gani nan ina zagayawa fa. Hhhhh su o'o akwai akwai tsoro ji harda rawar jiki kar na ganta ba paper). Jawahir ta mike ta dawo da littafi da biro, "To yanzu za mu fara da kissar tsafta don ita ce kan gaba a kan komai. Ki kasance mai tsaftar gidanki ko da yaushe cikinsa da wajensa. Kicin dinki ya zamo a gyare a share, a goge ki turara masa turarukan wuta me dadin kamshi. Toilet dinki ya zamo kullum cikin gyara idan kika wanke kika goge komau kika cire yana ki masa nasa turaren wutar na musamman ya kasance cikin kamshi wanda mutum ya yi bahaya wannan kamshin zai kashe masa jin warin bahayan nasa, idan ba ki da lokacin yin wanki da kanki to a ajiye almajiri idan sun kai kala biyu zuwa uku ki ba shi ya wanke ya goge miki, idan kin tashi sai ki turare kayan naki da turaren kaya sannan ki jera a kwaba. Sai k*ma kwabar ki sa mata turaren kaya don gudun warin ruma da dai sauransu. Ki kasance mai kwasar shimin mijinki, gajeren wandonsa, hankijinsa da dai wani karamin abu da yake amfani da shi ki wanke, ki goge su ki turare su da turaren kaya ki adana masa su. Idan kin shiga wanka ki rinka amfani da daddadan sabulu me kyau da dadin kamshi. Ki rinka cuda hammatarki, kasan nonuwanki, matse-matsin cinyarki, ki rinka wanke gabanki sosai da sabulu me kamshi, duk wani lungu da sako na jikinki ki wanke shi ki gyare shi fes in da ko ina mai gida ya sa kansa zai ji kamshi. Ki kasance ko yaushe cikin gamsasshiyar kwalliya, ki daure da asuba idan kun yi sallah me gidanki zai ja ki ku koma gado ku kwanta, to ki yi kokarin hana kanki bacci. Har sai shi ya yi sai ki janye jikinki a hankali ki tashi ki nufi kicin don hada muku karin k*mallo. Kada ki yi masa break kala daya saboda saurin ginsa ki yi masa kalolin break kowanne ki zuba a fulas gudun kada ya huce. Daga nan ki jere su a tebir ki gyara wajan ki da turare ko ina da daddadan kamshi me sanyaya zuciya, sai ki je ki yi wanka ki bata lokaci wajen yin kwalliya wannan fa kwalliyar safe ce ta barka da tashi me gida. Za ki saka les ko atamfa ko shadda ko boyal duk dai wanda ya samu, za ki feshe jikinki da kalolin turaruka masu kyau da dadin kamshi wanda har za a kasa tantance wane irin kamshi k**e yi, to sai ki nufi dakin maigida. Ba a tashin miji da hayaniya ko surutu ko ki yi ta jijjiga shi kina kiran wane! ka tashi lokaci ya yi, in kika yi irin haka za ki bata ran maigidanki. Abin da kawai za ki yi shine da kin shiga dakin mijinki kin ga yana bacci ga lokacin tafiya Office ko kasuwa ya kusa, to sai ki zauna a gefen gadon ki sa hannuwanki kina shafar fuskarsa kisa bakinki kina hura kunnunsa a hankali kina shafa fuskarsa tare da dan jan karan hancinsa. Ko ki fara shafar kasan mararsa kadan-kadan. To za ki ga ya tashi a nitse ba tare da magagi ko tsaki ba, da ya mike ya shiga toilet ko kafin ya fito sai ki yi saurin gyara gadon ki debo masa kayan da zai sa hade da best da gajeran wando da dan hankici duk k*ma ki feshe su da turaruka masu dadin kamshi ki debomasa takalmansa ki goge su fes, da ya fito daga toilet ki yi gaggawar daukan tawul ki rinka tsane masa ruwan jikinsa sannan ki debo mayukan da yake amfani dasu ki rinka shafa masa a hankali kina yi kina ba shi labari na ban dariya a hirar nishadi. Ki taimaka masa wajen sa kayan nasa, ki sa karamin k*m ki taje masa sumar kansa, ki dada dauko turaruka ki k*ma feshe shi da su, ki sa masa gilas idan yana da ra'ayi. Ki riko hannunsa ku taho zuwa kan tebir kuna tafe a hankali kina yi masa rausaya tare da yawan shigewa jikinsa har ku iso tebir din. Ki rinka zuba masa komai kina turo masa gabansa kada ki damu da sai kin ci a lokacin, ki rinka hada masa abinci me yawa a gabansa ki rinka tura masa kina yi masa shagwabar bai ci da yawa ba, ko ki ce ke ba ki yarda ba sai ya cinye da sauran abubuwan da za su ja hankalinsa ya saki jikinsa sosai ya ci abinci ya koshi. Idan ya mike don ya tafi office ki roko masa jakarsa kina yi masa 'yar shagwabar Honey da ka tashi daga office ka yo gida kada ka tsaya wani wajen ka ji. Honey idan ka isa office ka tsaida hankalinka ka yi aikinka a nitse kada ka yi tunanin komai bare ya sa min kai a damuwa. Za ki ga ya rungumoki tare da shi miki albarka duk k*ma inda yake hankalinsa yana kanki Allah Allah zai yi ya dawo gida don ya tarar da ke. To da ya tafi office ke k*ma a wannan lokacin za ki samu ki yi baccinki kafin lokacin girkin rana ki kula me mijinki ya fi so, me ya fi sha awar ci don ki kiyaye wajen girka masa su, shinkafa da miya, ko tuwon shinkafa da miyar taushe, ko danyar kubewa, ko miyar agushi, ko miyar wake da ganye, ko tuwon dawa, ko na masara, tuwon semovita ko ki daka masa sakwara, ko ki dafa kuskus ko taliya, zaki hada masa da soyayyen naman kaji ko gasasshen naman kasuwa ko farfesun kayan ciki, ko farfesun kan rago ko na jelar sa ko farfesun naman karamar dabba, ( A nan ana magana ne idan mijinki mai hali ne, idan kuwa ba mai hali ba ne sai ki yi masa abin da kika tabbatar yana jin dadinsa dai-dai rufin asiri) To idan kika duba abin da ya fi so a cikin yi masa kika gama komai kafin ya dawo, ki dada gyara gidanki ki turare shi da nau'in kamshi kala kala, ki shiga aiki sake fesa wanka sai ki yi kwalliya ki hade da siket ko riga da wando ko doguwar riga ko dinkakken shadda, ko atamfa, boyal, yadi, material, da dai sauransu, to ya kasance karamin dinki ne dai-dai jikinki ki saka wanda da zarar maigida ya dawo za ki tafi cikin salon murna ki ringume shi kina me yi masa barka da zuwa. Ki fara raka shi dakinsa ki cire masa kayan jikinsa ki hada masa ruwan wanka da turaren wanka a ciki da ya shige tolet sai ki kwashe kayan da ya cire ki rataye masa a anga. Ki fito masa da kanana na shan iska. Da ya gama shirnsa ya fito sai ki zo a nitse cikin dabara ki rinka loda masa abinci yana ci kina fara loda masa wani yanda zai ci ba tare da ya gane ya ci da yawa ba. Kina zuba masa sanyayyen abin sha yana ci yana sha, har sai ya koshi ya yi kat sai ki jawo shi ku baje kan kafet ko kujera kuna wasanni da hirarraki masu dadi ko kallo ku, ki rinka karanta masa labarai masu dadi, amma ki kasance ko yaushe kina manne a jikinsa ki rinka yi masa shagwaba kina mai da kanki karamar yarinya a gabansa kina zama doluwa marar wayo ki rinka sa yin dan sokoncin zai rinka sa mijinki dariya, to yawaita masa irin wannan abubuwan shi zai kara muku shakuwa da fahimtar junanku, za ku kasance cikin bege da son junaku ko da yaushe. Idan kin tabbatar kin wa mijinki lodi da abincin rana to yunwa ba za ta gallabe shi da dare ba, don ba a so da daddare a ci abu me nauyi an fi so a ci irinsu hadin salak, sharfar taliya me romo gasasshen nama, ko hanta ko zaka, farfesun kayan ciki ko na naman romon kai, ko na jelar sa ko naman karamar dabva, kai da dai duk abin da Allah ya h**e muku marar nauyi. To kinga wadannan duk inya ci va za su yi masa bauyi a ciki ba bare su hana shi su kuni su takura shi wajen aiwatar sa sunnah Jan hankalinsa ta suffofin kwanciya kala-kala. Duk abin da kika kula ya fi so to ki lakanci abun duk sanda kuke tare ki rinka kirkiro wasu abubuwan ma da bai san da su ba. Ki saki jikinki da shi ki cire kunya ki rinka sarrafa shi kina dan kukan kissa tare da kiran sunansa a hankali kina hadawa da kalaman soyayya don tafiyar da imaninsa. Ki kasance cikin yawan shan kunun aya, shan zuma, shan rake, lemon zaki, kankana, gwanda, abarba, nono, dabino, cukwi, tufa, inibi, kin ga wadannan ki kasance cikin yawaita cin su ko da yaushe don suna karawa mace ni'ima da amfani sosai a jikinta. Ki nemi garin bagaruwa gwangwani daya, garin kurna gwangwani uku, garin habbatus sauda rabin gwangwani, garin dakakken dabino ki rinka samun busasshiyar aya ki daka sai ki hada su waje guda ki samu lafiyayyen nonon shanu marar tsaki kina diban wadannan kayayyakin da kika hada kina damawa da nonon kina sha, to wannan shi ne sirrin yanda kika ga nonuwanka sun cuccuko sun yi manya suna tsaye ba su da alamar rankwafawa. Jawahir ta ce, "Au Aunty kina nufin garin nan da k**e ba ni damamme da madarar shanu yana da nasaba da cikuwar nonuwana?" Aunty ta ce, "Kwarai kuwa shi ya sa kika ga ina yawan gasa mana naman karamar dabba ruwa ruwa da k*ma romon kai da farfesun wannan sirrika ne na mata. Duk abubuwan da na lissafo a baya su suke bamu ni'ima a jikinmu mu mata suna sa ihu kyan fata, yawan, amfani da man zaitun da habbatus sauda suna sa fata ta yi mul-mul da santsi kamar ta jariri." Jawahir ta ce, "To Aunty ni da ba a gidan miji nake ba amma k**e ta dirka min magunguna da tsumi ina sha. Kuma kullum sai kin sa ni na yi turare na tsugunno da na jiki, meye fa'idar hakan.? Ta dafa kafadarta daya ta ce, "Diyata ke nan, ai duk wannan shiri nake yi miki nake tsumaki don duk sanda Haidar ya kusance ki to haihaita haihaita sunyi sallama da kowacce irin mace don ba me iya gamsar da shi sai ke, na gaya miki Haidar sai ya dawo tafin hannunki, sai yanda kika juya shi. Jawahir ta fada cinyarta tana kyalkyala dariya, "Na gode Aunty sai ya san wadda yake cewa kwaila ko tatsitsiya."


Kuyiman Afuwa akan rashin yimaku posting Jiya👏👏👏👏

Want your business to be the top-listed Government Service in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Katsina