Mata zalla Woman Development Initiative
the organization was created in 2014 under the leadership of HAJIYA SARATU SAA MUSAWA
wannan page an bude shi ne domin tallar ayukan alkharin gwamnatin A.P.C Wanda kungiyar mata zallah na jihar katsina karkashin jagorancin hajiya SARATU SAA MUSAWA suke daukar nayi
Proudly Nigeria 🇳🇬
Taqabbal Allahu minna wa minkum
“May Allah accept (good deeds) from us and from you.”
27/05/2026
Yaumul Eid Mubarak 🌙
Allah ya karɓi addu’o’inmu a wannan rana mai albarka,
ya gafarta mana zunubainmu, ya rubuta mu cikin masu ‘yanci daga wuta. Amin.
ML DIKKO MAI KATSINA
Musawa/matazu Assalamu alaikum 🙏
01/05/2026
Ya Allah Ka kawar da dukkan damuwa daga rayuwar waɗanda suke cikin ƙunci da bakin ciki. Ka ba zukatansu natsuwa, Ka cika rayuwarsu da farin ciki, Ka yi musu rahama da alherinka Amin, 🤲 ❤️
Barkanmu da juma'a yan'uwa
27/04/2026
CONSENSUS: TAKOBI MAI KAIFI BIYU A SIYASAR YAU
Daga
HJIYA SARATU SA’A MSW
(DG MATA ZALLA)
Mece Ce Consensus?
Shi ne tsarin da ‘yan siyasa ke zaune su amince da ɗan takara ɗaya ba tare da an je zaɓen fidda gwani ba. Manufar: A hana rabuwar kai da faɗa.
Amma tambaya a nan ita ce: Shin magani ne ko kuwa cuta ce a ɓoye?
AMFANIN CONSENSUS - IDAN AN YI SHI DA GASKIYA
1. Yana Hana Faɗa da Rarrabuwar Kai
Zaɓen fidda gwani yakan haifar da ƙiyayya. Ɗan’uwa ya zama abokin gaba. Consensus na gaske na iya haɗa kan ‘yan jam’iyya su fuskanci babban zaɓe a dunkule.
2. Yana Adana Kuɗi da Lokaci
Zaɓe yana cin kuɗi sosai. Kuɗin da za a kashe ana yaƙi da juna, a ajiye shi a yi amfani da shi a yaƙi da jam’iyyar hamayya.
3. Yana Kawo Mutum Mai Ƙarfi
Idan shugabanni s**a zauna s**a zaɓo wanda ya fi cancanta da gaske, ba wai wanda ya fi kuɗi ba, to jam’iyya za ta samu ɗan takara mai ƙarfi da ya haɗa kan kowa.
ILLAR CONSENSUS - IDAN AN YI SHI DA SON ZUCIYA
1. Yana Kashe Dimokuradiyya
Dimokuradiyya ma’anarta zaɓi ce. Idan mutane 5 s**a zauna a ɗaki su ce “wannan ne”, to sun hana dubban ‘ya’yan jam’iyya ‘yancin zaɓe. Wannan cin amana ne.
2. Yana Haifar da ‘Yan Tawaye
Mutum ya shirya, ya sayar da kadara, ya yi kamfe, sai a ce “an yi consensus”. Gobe zai fita ya nemi wata jam’iyya. Shi ke nan aka raba jam’iyya biyu.
3. Yana Kawo Shugabanni Marasa Inganci
Sau da yawa ba a yin Consensus don a zaɓo nagari ba. Ana yi ne don a zaɓo wanda shugaba yake so. Sakamako? A samu shugabanni marasa kishin al’umma.
4. Yana Sanya Rashin Amincewa
Idan talaka ya ga an hana shi zaɓe, zai ce “to me zai sa in fito ranar zaɓe?”. Wannan yana kashe ƙwarin guiwar ‘yan ƙasa.
Babban Lura:
Babu laifi a yi Consensus a jam’iyya, sai dai niyyar masu yin shi ce matsalar.
Idan niyya gina jam’iyya ce, zai yi kyau.
Idan niyya murƙushe wasu ce, to zai zama sanadin rugujewar jam’iyya.
Don haka, mu ‘yan siyasa:
Kafin ku ce “Consensus”, ku tambayi kanku:
"Shin muna haɗa kan al’umma ne, ko kuwa muna raba su ne da sunan haɗa kai?"
✍Abubakar Lawal Abbah
(Youngsadik_abba)
16/04/2026
Rayuwa ba ta tsaya ga abin da kake da shi ba — tana tafiya ne da yadda kake amfani da abin da Allah Ya h**e maka. Wani yana da yawa amma zuciyarsa babu kwanciyar hankali. Wani kuma yana da kaɗan, amma zuciyarsa cike take da natsuwa da godiya.
Kada ka auna nasara da yawan dukiya kaɗai, domin mafi girman nasara ita ce nutsuwar zuciya da kyakkyawar mu’amala da mutane.
Ka tuna: Lokaci yana wucewa, dama tana ƙarewa, amma halinka da ayyukanka su ne abin da zai zama shaida a gare ka har abada.
13/04/2026
Rayuwar duniya kamar madubi ce; yadda ka ɗauke ta, haka za ta nuna maka.
Ka bi ta a hankali, domin yau kai ne, amma gobe ba kai ba ne. Mai hankali shi ne wanda ba ya gaggawa, yana tafiya a nutsuwa, yana shirya gobe tun yau.
Kai matashi, kar ka yaudaru da ƙarfin jikinka, Kar ka yi alfahari da yau, domin ba ka san halin gobe ba.
Lokaci ba aboki ba ne; idan ka ɓata shi, zai hukunta ka. Ka gina kanka tun yau, domin gobe ba ta jiran sakaci.
Allah Ubangiji Ya sa mu dace.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the business
Telephone
Address
Katsina
008
