Faiserl Sanusi Alieyou

Faiserl Sanusi Alieyou

Share

News and current affairs || Hausa || Nigeria || Arewa

04/04/2026

Allah yakawo sauki

03/04/2026

Wasu Dabbobin sunfi wasu mutanen ayanxu

03/04/2026

Wai wannan abun a Garin Plateau yake faruwa??? Ina hukumomin suke Rai ya zama kamar ba komai ba

03/04/2026

The most gentleman you witnessed so far since the inception of this war in 28 Feb,2026.

03/04/2026

self Killing

03/04/2026

Hmmmm

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayyana matakin saka kyamarorin tsaro masu amfani da fasahar AI a wasu sassan jihar yayin da yake jawabi a lokacin ziyarar jaje da ya kai ranar Alhamis.

Ƙarin bayani - https://bbc.in/4tLiwxB

02/04/2026

Masha Allah. ALLAH YA KARA KIYAYE KOWA DA KOWA.

02/04/2026

Sunada gskia. Kam

YANZU-YANZU: ‘Lokaci Ya Yi da Za Ka Yi Magana Don Kawo Mafita’ — Al’ummar Jos Sun Yi Kira ga Sheikh Sani Yahaya Jingir

Wasu daga cikin al’ummar garin Jos sun yi kira ga fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Yahaya Jingir, da ya fito fili ya yi magana kan halin da ake ciki, domin taimakawa wajen kawo sauƙi da daidaito a yankin.

Al’ummar sun bayyana cewa akwai buƙatar malamin ya yi kira ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, domin ɗaukar matakan gaggawa da za su rage tashin hankali tare da dawo da zaman lafiya a yankin Jos da kewaye.

A cewarsu, kalaman Sheikh Jingir na da matuƙar tasiri ga al’umma, musamman ganin yadda ya saba jan hankalin jama’a kan muhimman batutuwa na ƙasa. Sun ƙara da cewa irin rawar da ya taka a baya wajen kira ga ƴan Najeriya su zaɓi Shugaba Tinubu ya nuna irin ƙarfin tasirinsa a idon jama’a.

Masu wannan kira sun jaddada cewa lokaci ya yi da manyan malamai da shugabanni za su ƙara taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’umma, musamman a irin wannan lokaci mai muhimmanci.

Photos from Jaridar Tsuntsuwa's post 02/04/2026

Kai Nigeria

31/03/2026
31/03/2026

Allah yasa haka

Gawuna ya faɗi hakan ne a yayin da yake karɓar katin zama dan jam'iyyar ADC a mazabar sa a yau Talata.

31/03/2026

Hmmm

Tinubu Ya Yi Allah-Wadai Da Kashe-kashen Jos Da Kaduna

• Dole A Kamo Wadanda S**a Kashe Mutane a Angwan Rukuba — Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fito ya yi Allah-wadai da kakkausar murya game da hare-haren rashin imani da wasu ‘yan bindiga s**a kai a gundumar Angwan Rukuba da ke Jos, Jihar Filato, da kuma kauyen Kahir da ke Karamar Hukumar Kagarko a Jihar Kaduna.

Shugaban ya bayyana wadannan hare-hare, wadanda s**a hada da kisan jama’a a Jos da kuma garkuwa da baki ’yan bikin aure a Kaduna, a matsayin babban kalubale ga hadin kan Najeriya. Ya kuma tabbatar wa ‘yan kasa cewa ba za a zura ido wadanda s**a aikata wannan danyen aikin su sha da dadi ba.

A cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa kan fannin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bayyana maharan a matsayin azzalamai kuma matsorata.

> "Duk wanda zai fake da duhun dare ya kashe mutanen da ba su da kariya kamar yadda aka yi a Jos da kauyen Kahir, to matsoraci ne marar tausayi. Manufar wadannan maharan ita ce su haifar da ramuwar gayya domin jini ya ci gaba da kwarara," in ji Shugaban.

Shugaba Tinubu ya ba wa jami’an tsaro umarnin su kara kaimi wajen kamo wadanda s**a aikata laifin da kuma wadanda ke yada labaran karya da nufin ruruta wutar rikici. Haka kuma, ya ja kunnen wasu bangarorin kafafen yada labarai da ke kokarin danganta hare-haren da batun addini.

Babban matakin da Shugaban ya dauka sun hada da:
* Kiran Jami'an Tsaro: Ya bukaci jami'an tsaro su rika amfani da bayanan sirri don dakile hare-hare kafin su auku.
* Ceton Wadanda Aka Sace: Ya ba da umarnin gaggauta ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a kauyen Kahir.
* Kayayyakin Aiki: Ya bayyana cewa gwamnati na kan hanyar sayo manyan makaman zamani don bin sawun miyagun mutane a duk inda suke.

Shugaban ya jinjina wa Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna bisa kokarinsu na shawo kan lamarin da kuma tallafawa ayyukan ceto.

Daga karshe, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da s**a rasa rayukansu, sannan ya yi addu’ar samun sauki ga wadanda s**a jikkata, yana mai kira ga al’umma da su ba wa jami’an tsaro hadin kai don tabbatar da zaman lafiya.

Want your business to be the top-listed Government Service in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address


Katsina