30/03/2026
Zaben Gwaji: Wace Jam'iyya Ce, Zaka Zaba?
1. ADC
2. APC
An Samar da wannan Jaridarne domin baku ingatattu Kuma sahihan labaru na gida dana kasashen ketare. Fede Gaskiya shine taken mu
Domin gudanar da aikin cikin girmama, tare da hada kan al'umar mu.
30/03/2026
Zaben Gwaji: Wace Jam'iyya Ce, Zaka Zaba?
1. ADC
2. APC
30/03/2026
Da ɗumi-ɗumi: Tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi ya sauka a jihar kano domin tarbar Sen Rabi'u Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar ADC.
30/03/2026
YANZU-YANZU: Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoninsa Baki Daya
30/03/2026
Cibiyar Yusuf Bala Usman na Gabatar da Sakamakon Bincike kan Mulkin Ƙasa da Tsaro
Cibiyar Yusuf Bala Usman na ci gaba da gabatar da sakamakon binciken da ta gudanar kan harkokin mulkin ƙasa, muhalli da matsalar tsaro a wasu jihohin Arewacin Najeriya.
Binciken ya shafi jihohin Bauchi, Jigawa, Katsina da Kaduna, inda aka mayar da hankali kan gano ƙalubale da kuma nemo hanyoyin magance su.
Ana gudanar da taron ne a yau Litinin, 30 ga Maris, 2026, a Otal ɗin Alhujrat da ke Katsina.
30/03/2026
Yadda Turawa Masu Yawon Bude Ido S**a Zo Kallon Hawan Mai Martaba Sarkin Gombe
30/03/2026
INDA RANKA: An yanke mata hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari bayan ta ƙi auren wanda ya tallafa mata a karatunta.
Wata matashiyar budurwa ‘yar kasar Uganda mai suna Fortunate Kyarikunda, an ba da rahoton cewa an yanke mata hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bayan ta ƙi auren wani ɗan kasuwa da ya tallafa mata a karatunta.
Bisa ga rahoton, su biyun sun fara soyayya ne a shekarar 2015.
Daga baya kuma a shekarar 2018, sun amince za su yi aure, inda sai mutumin ya ɗauki cikakken nauyin kuɗaɗen karatunta da kuma rayuwarta.
Sai dai a shekarar 2026, matar ta ƙi neman auren nasa. Sai ɗan kasuwan ya kai ƙarar ta a kotu.
Bayan kotun Rukungiri ta yi nazari kan shari’ar da kuma nazarin shaidun da aka gabatar, sai ta same ta da laifi kuma ta yanke mata hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari, saboda mutumin ya tallafa mata har tsawon shekaru sama da goma har sai da ta kammala karatunta.
Me kuke tunani Idan haka ta fara Faruwa a Nigeria?INDA RANKA: An yanke mata hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari bayan ta ƙi auren wanda ya tallafa mata a karatunta.
Wata matashiyar budurwa ‘yar kasar Uganda mai suna Fortunate Kyarikunda, an ba da rahoton cewa an yanke mata hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bayan ta ƙi auren wani ɗan kasuwa da ya tallafa mata a karatunta.
Bisa ga rahoton, su biyun sun fara soyayya ne a shekarar 2015.
Daga baya kuma a shekarar 2018, sun amince za su yi aure, inda sai mutumin ya ɗauki cikakken nauyin kuɗaɗen karatunta da kuma rayuwarta.
Sai dai a shekarar 2026, matar ta ƙi neman auren nasa. Sai ɗan kasuwan ya kai ƙarar ta a kotu.
Bayan kotun Rukungiri ta yi nazari kan shari’ar da kuma nazarin shaidun da aka gabatar, sai ta same ta da laifi kuma ta yanke mata hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari, saboda mutumin ya tallafa mata har tsawon shekaru sama da goma har sai da ta kammala karatunta.
Me kuke tunani Idan haka ta fara Faruwa a Nigeria?
30/03/2026
Allahu Akbar Malam Mustapha Elrufai Kenan Yake Kuka A Wajen Jana'izar Kakarsa
30/03/2026
YANZU-YANZU: Yusuf Nasiru Gawuna, Tsohon Ɗan Takarar Gomna A Jihar Kano Ya Sanar Da Ficewarsa Daga Jam’iyyar APC Zuwa ADC A Hukumance
Daga Muhammad Kwairi Waziri
30/03/2026
HON. ALIYU NASIR KANKARA, CLN, MNLA
A wannan zamani da ake ƙara buƙatar shugabanci mai ma’ana a faɗin Najeriya, musamman a matakin ƙasa, fitowar matasa shugabanni irin su Aliyu Nasir Kankara na nuna sabon salo na shugabanci wanda zai haɗa kowa da kowa, kawo ƙirƙira da kuma mayar da hankali ga cigaban al’umma. Ƙudurinsa na tsayawa takarar wakilcin Karamar Hukumar Kankara a Majalisar Wakilai ta Jiha ya zo a kan lokaci, kuma ya ginu ne bisa hangen nesa na sauyi, haɗin kai da cigaba mai ɗorewa.
Aliyu Nasir Kankara ya fito a matsayin mutum mai nauyin hangen nesa, wanda tafiyarsa ta rayuwa ta nuna jajircewa, ladabi da kuma sadaukar da kai wajen hidimar jama’a. Duk da kasancewarsa matashi, yana da sabbin dabaru na rayuwa, wanda hakan ke ba shi damar haɗa kan manya da kuma matasa a Kankara da Jihar Katsina baki ɗaya.
A fagen aikinsa, ya taka rawa muhimmiya wajen shirye shiryen cigaban al’umma, ya rike muƙamai na shugabanci daban-daban, tare da ci gaba da fafutukar inganta rayuwar jama’a. Ta wannan hanya, ya samu ƙwarewa a fannoni da dama wanda ya haɗa da irin su; iya mu'amala tare da zama da jama’a, tattara goyon bayan al’umma, tsara dabaru, ƙarfafawa da kuma magance matsaloli waɗanda suke da matuƙar muhimmanci ga wakilci nagari a matakin majalisa.
A siyasance, Aliyu Nasir Kankara yana da cikakkiyar fahimta kan matsalolin da yankinsa na Kankara ke fuskanta, ciki har da rashin tsaro, rashin aikin yi, ƙarancin ababen more rayuwa da kuma matsalolin ilimi. Maimakon yin alƙawura marasa tushe, a shirye yake don samar da hanyoyin warware matsaloli cikin sauƙi, tare da jaddada haɗin gwuiwa da masu ruwa da tsaki, tsara manufofi masu amfani da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana.
Aliyu Nasir Kankara yana da ƙuduri na musamman wajen ƙarfafa matasa maza da mata ta hanyar koyar da sana’o’i, tallafawa harkokin kasuwanci, noma, wasanni da samar da damarmaki. Yana hangen Kankara wadda ke cike da albarkatu inda matasa za su zama masu ƙirƙirar ayyukan yi, ba masu neman aiki kawai ba, tare da samun horo da kayan aiki da za su taimaka musu su yi gogayya a tattalin arziki na zamani. Manufofinsa sun haɗa da inganta ilimi, noma, ƙwarewar fasahar zamani da kuma koyon sana’o’i, domin tabbatar da cewa matasa ba'a bar su a baya a wannan zamani na fasaha ba.
Baya ga batun matasa, shirinsa ya haɗa da ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa, inganta ababen more rayuwa a karkara, bunƙasa noma da kuma fafutukar samar da manufofi da za su inganta rayuwar talakawa. Kusancinsa da jama’a ya ba shi damar fahimtar ainihin buƙatun su, wanda hakan zai sa wakilcinsa ya zama mai tasiri da amfani.
A ƙarshe, Aliyu Nasir Kankara ba ɗan takara kawai ba ne, yana wakiltar sabon salo na shugabanci mai cike da hangen nesa, ƙwarewa da kuma ƙudurin yi wa jama’a hidima. Tsayawarsa takara wata dama ce ga Karamar Hukumar Kankara na rungumar shugabanci na matasa mai cike da ƙirƙira, kusanci da jama’a da kuma tabbatar da cigaba mai ɗorewa. Idan aka ba shi dama, yana da ƙwarewar da za ta kawo sauyi mai ma’ana ga Kankara da Jihar Katsina baki ɗaya.
Mustapha Muhammad Gimba,
Ɗan ƙasa mai kishin Karamar Hukumar Kankara, Jihar Katsina.
30/01/2026
Kwankwasiyya ta yi watsi da kiran da gwamnatin Kano ta yi wa mataimakin gwamna da ya ajiye mukaminsa
Kungiyar Kwankwasiyya ta yi Allah-wadai da kiran da gwamnatin jihar Kano ta yi na neman Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya yi murabus, tana mai bayyana matakin a matsayin tsokana da rashin godiya.
A wata sanarwa da kakakinta, Hon. Habibu Saleh Mailemo, ya fitar, kungiyar ta ce kiran bai dace ba kuma yana barazana ga zaman lafiya da jituwa a harkokin siyasa a jihar.
Ta zargi wasu jami’an gwamnati da yunkurin wulakanta magoya bayan jagoranta, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da ke cikin gwamnati.
Kwankwasiyya ta jaddada cewa Mataimakin Gwamnan an zabe shi ne tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf a tikitin hadin gwiwa, don haka huruminsa ya fito ne daga kundin tsarin mulki da kuri’un jama’a, ba daga ra’ayin wani mutum ba.
Kungiyar ta ce gwamnatin Kano samfurin gwagwarmayar Kwankwasiyya ce, tare da gargadin cewa ba za ta yi shiru ba idan aka ci gaba da wulakanta mambobinta.
30/01/2026
Jarumar kannywood Mishi Suleiman Ta Kammala Karatun Degree Ɗinta Allah Yayi Albarka Ameen.
30/01/2026
Gwamnatin Jihar Katsina Ta Karyata Jita-jitar Kashe Kuɗin Jiha Kan Shirin Gina Gidaje
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa shirin gina gidaje a garin Radda da kuma karamar hukumar Kankia ba zai ci ko kobo daga baitul-malin jiha ba, duk da jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Shugaban Ma’aikatan Jihar katsina, Alhaji Falalu Bawale, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis, inda ya ce abin da aka sanya hannu a kai yarjejeniyar fahimta (MoU) ce, ba kwangilar gini ba.
Ya ce aikin na da kimar kuɗi Naira biliyan 155, inda kuma za a gina gidaje 3,750, tare da haɗa shirin da harkokin noma da kiwon kifi,wanda kamfanin Spare USA Cooperation zasu dauki nauyin yin shirin.
A cewarsa, masu zuba jari ne ke ɗaukar nauyin aikin gaba ɗaya, yayin da rawar gwamnatin jihar ta taƙaita ne kawai wajen bada fili, ba tare da fitar da ko sisi ba.
Alhaji Falalu Bawale ya ƙara da cewa za a zaɓo mahalarta shirin daga ƙananan hukumomi 34 na jihar, za a horas da su kan dabarun noma na zamani,za kuma a rika biyansu albashi, sannan daga bisani a mallaka musu gidajen da s**a zauna muddin sun cika sharudda.
Shi ma Babban Manajan Hukumar Gidaje ta Jiha, Dakta Aliyu Rabi’u Kurfi, ya ce aikin ya samu cikakken goyon bayan Gwamnatin Tarayya, yana mai jaddada cewa ba da fili da garanti ba ya nufin kashe kuɗin gwamnati.
A nasa bangaren, wakilin masu zuba jari, ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, rage zaman banza da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar Katsina.
Gwamnatin jihar ta ce an shirya taron ne domin kawar da ruɗani da tabbatar wa al’umma cewa ba za a kashe kuɗin jiha a aikin ba.