30/05/2026
Mulkin Gwamnatin Radda: na Shekaru Uku ya kawo Sauyi da Cigaba a Jihar Katsina
Yayin da Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, ke cika shekaru uku a mulki a ranar 29 ga Mayu, 2026, gwamnatinsa ta samu yabo saboda kokarinta wajen inganta tsaro, ilimi, lafiya, noma, ababen more rayuwa da walwalar al’umma.
A bangaren tsaro, gwamnatin ta dauki matakai masu karfi wajen yaki da ‘yan bindiga tare da hada kai da hukumomin tsaro da al’ummomi,tare da daukar jamian tsaro na C watch, lamarin da ya kara samar da zaman lafiya da damar noma da kasuwanci a kalla kaso hamsin chikin adalchi
A fannin ilimi, gwamnatin ta ware kusan kashi 25% na kasafin kudin jihar, ta dauki malamai sama da 8,000 aiki, ta horas da sama da 20,000, tare da gyara da sake gina makarantu fiye da 500.
Bangaren lafiya ya samu gagarumin ci gaba ta hanyar farfado da cibiyoyin kiwon lafiya sama da 270, mayar da wasu cibiyoyi zuwa manyan asibitoci, da daukar ma’aikatan lafiya kusan 2,000 aiki na din,din din,
A bangaren noma, gwamnatin ta tallafa wa manoma da shirye-shiryen bunkasa samar da abinci da aikin gona na zamani,kala kala daga tarakata zuwa galma me amfani da man fetur wanda ya taimaka wajen rage wahalhalun noma a jihar.
kuma, an aiwatar da ayyukan tituna a bangaren shiyyoyi ukku na jihar
Daura zone
Funua zone
Katsina zone
Inda akayi ma manyan biranen shiyyoyin aikin sabunta tituna da fadada su tare da wasu kananan hukumomin daga chikin shiyyar, tare da gyaran gine-ginen gwamnati da bunkasa hanyoyin karkara.
Gwamnatin ta kuma ba muhalli muhimmanci ta hanyar shirye-shiryen dasa bishiyoyi da wayar da kan jama'a game da kare muhalli.
Matasa da mata sun amfana da shirye-shiryen koyon sana’o’i, tallafin kasuwanci da samar da ayyukan yi, yayin da sarakunan gargajiya s**a samu karin kulawa da inganta walwalarsu.
Bayan shekaru uku, gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda ta kafa tubali mai karfi na ci gaba da sauyi a Katsina, tare da ci gaba da mayar da hankali kan tsaro, ci gaban tattalin arziki, ilimi da walwalar al’umma mal Dr. Dikko Umaru Radda bai tsaya haka ba ku biyo mu kashi na biya a shekara ukkun Radda
✍️APC MEDIA LEADS Katsina ta dauki nauyin wannan
27/05/2026
May this blessed Eid bring peace, happiness, and countless blessings to you and your family. May Allah accept our prayers, sacrifices, and good deeds, and fill our hearts with love, unity, and gratitude.
Wishing you joyful celebrations and beautiful moments with your loved ones.
Eid Mubarak!
24/05/2026
Zaben fidda gwani na jamiyyar APC matakin shugaban kasa
President Tinubu: 10.9m
Stanley Osifo: 16,503
21/05/2026
Gwamnan jihar katsina mal Dr. Dikko Umaru Radda ya zama Halastacchen Dan takarar jam,iyyar Apc yanzu haka fatan Allah ya bada nasara chikin sauki.
20/05/2026
Gwamna Radda Yayi Kira Ga ’Yan Takarar APC Da Su Fita Neman Al’umma Gida-Gida Gabanin Zaɓen 2027
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, yayi kira ga dukkan ’yan takarar jam’iyyar APC masu neman mukamai a kujeru daban-daban da su fara Fita Neman Al’umma Gida-Gida Gabanin Zaɓen 2027
Gwamnan yayi wannan kiran ne yayin da yake karɓar wata babbar tawaga daga iyalan fitaccen ɗan kasuwa kuma mai ayyukan alheri, Alh Dahiru Barau Mangal, ƙarƙashin jagorancin dan takarar majalisa mai wakiltar mazabar Katsina, Barrista Abba Dahiru Mangal, a ziyarar godiya da s**a kai masa.
Gwamna Radda ya buƙaci ’yan takarar da su kusanci al’umma tare da neman addu’o’i da goyon baya daga masu ruwa da tsaki, shugabannin al’umma da malaman addini a faɗin jihar.
Haka kuma, ya yabawa ’yan takarar da s**a janye wa Barrista Abba Mangal a takarar kujerar Majalisar Wakilai, inda ya bayyana hakan a matsayin alamar haɗin kai da balagar siyasa a cikin jam’iyyar APC.
A nasa jawabin, Barrista Abba Mangal ya yabawa salon shugabanci na Gwamna Radda, yana mai cewa nagartaccen shugabancinsa ne ya tabbatar da gudanar da zaɓukan fidda gwani cikin nasara da lumana a faɗin jihar.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa idan aka zaɓe shi zuwa Majalisar Tarayya, zai bayar da wakilci nagari tare da kare muradun al’ummarsa yadda ya kamata.
MS Ingawa
SSA, Media & strategy
18/05/2026
EFCC ta kwato naira miliyan 837 ta damkawa Gwamnatin jahar Katsina su.
18/05/2026
Jamiyyar apc a jihar katsina ta tabbatar da Senator Abdulaziz Musa Yaradua a matsayin dan takarar ta a yankin Katsina zone wanda zaiyyi mata takarar sanata a zaben 2027 mai zuwa
Geamnan jihar katsina shine babban bako a taron kuma shine Wanda ya kaddamar dashi a filin Wasa na chikin garin katsina
18/05/2026
Jamiyyar apc a jihar katsina ta tabbatar da Senator Muntari dan dutse a matsayin dan takarar ta a yankin Funtua wanda zaiyyi mata takarar sanata a zaben 2027 mai zuwa
Geamnan jihar katsina shine babban bako a taron kuma shine Wanda ya kaddamar dashi a garin Funtua ,