03/02/2026
Available @08065760115
لا إله إلا الله محمد رسول الله صلى الله عليه وآله وصحبه وسلم
03/02/2026
Available @08065760115
28/01/2026
You're All Invited
18/08/2025
Sakon ALLAH zuwa ga shugabanni.
A karshen aya ta 40 cikin suratun Nuur Allah yace: ".....Allah yana taimakon mai taimakonshi (taimakon addininshi).
A aya ta 41 sai ya bayyana su wanene yake magana akansu, inda yace: "Sune wadanda idan muka tabbatar dasu a bayan kasa (muka basu mulki) sai su tsayar da sallah, su bayar da zakkah, suyi umarni da kyakkyawa su kuma yi hani da mummuna. Ga Allah ne shi kadai al'amari yake komawa.
Don haka duk shugaban dake son taimakon Allah to ya yi kokari wajen taimakon addinin Allah.
17/01/2025
Assalamu Alaikum.
Barkammu da Safiyar Juma'a Mai albarka.
Ga Sabuwar Ɗauka na shadda mao kyau da Inganci.
Kawai ku Tuntuɓemu a 08065760115.
AbūMuhsin Ɗāhiru Dissi
31/12/2024
TARBIYYAR YARA:
Yadda zaka baiwa yaranka tarbiyya ta hanyar hanasu kangara, wargi da shaye-shaye.
YĀ DAN UWA MAI ALBAKA: Don baiwa yaranka ingantacciyar tarbiyya da zata nesanta su daga rikicewar zamani na abinda ya shafi kangara, sace-sace, shaye-shaye da sauransu to ga magani.
Allah swt yana faɗawa Manzonsa wanda kirane da ya shafi Annabi (s.a.w) damu al'ummar shi cikin Alkur'ani yana cewa:
اتْلُ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِنَ الْكِتَابِ وَأَقِمِ الصَّلَاةَ ۖ إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَىٰ عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنْكَرِ ۗ وَلَذِكْرُ اللَّهِ أَكْبَرُ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا تَصْنَعُونَ.
Ma'ana Allah yace da Annabi (Alaihis salatu Wasallam) "Ka karanta abinda ake wahayinshi zuwa gare ka ma littafi (Alƙurani), ka kuma tsaida sallah, lallai sallah tana hana alfasha da ayyuka abin ƙyama, kuma ambaton Allah shi ne mafi girma. (Al'Alkabut 45).
Da wannan ne Malaman tarbiyya s**a ce, matuƙar aka koyawa yaro sallah tun yada yaro ƙarami (7years) kamar yadda yazo a hadisi, kuma sannan aka koyawa mashi littafin Allah (alƙur'ani) sannan yana zuwa inda ake ambaton Allah wurin wa'azuzzuka aka kuma sanar dashi ingantattun zikirora da s**a inganta daga Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) to Lallai ba zaka sameshi ya taso yana aikata wani abu da yaci karo da tarbiyya ba.
Allah muke roƙo da ya shiryar damu da zurriarmu zuwa ga abinda ya yarda dashi.
✍️ Ɗan uwanku AbūMuhsin Ɗāhiru Dissi
30/06/1446AH.
31/12/2024CE.
10/12/2024
SALLAR ISTIKHARA
●Istikhara shine neman zabin Allah a kan wani al'amari na ka, ya zaba maka abin da yake shine ya fi alkhairi a gareka ta hanyar yin sallah da addu'ar da Sunnah ta koyar na Istikhara.
●Sunnah ne yin Istikhara, kuma a na yin ta ne ga abun da yake halal, kamar kasuwanci, sayan wani abu, neman aure, neman aiki da sauransu
●Idan mutum ya yi nufin yin wani abu, zai fara neman shawaran kwararru kuma amintattu masana a game da al'amarin.
●Mutum zai yi sallah raka'a biyu na nafila, sannan ya karanta Addu'ar.
Addu'ar Istikhara shine:
💧اللهم إِنِّي أَسْتَخِيرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْألُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيم، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلا أَقْدِر، وَتَعْلَمُ وَلا أَعْلَم، وَأَنْتَ عَلاّمُ الغُيوبِ، اللّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ- (وَيُسَمِّي حَاجَتَهُ) - خَيْرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي- أو قال: عَاجِلِهِ وَأَجِلِهِ- فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا اْلأَمْرَ شَرٌ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ عني وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِي الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ.
💧Allahumma inni astakhiiruka bi ilmika, wa astaqdiruka biqudratika, wa as'aluka min fadlikal azeem, fa innaka taqdiru wala aqdir, wa ta'lamu wala a'lamu, wa anta allamul ghuyuub, Allahumma inkunta ta'lamu anna hazal amra (sai ya ambaci bukatar na shi), Khairun liy fii deeniy wama'ãshiy wa ãqibati amriy faqdurhu liy wa yassirhu liy, thumma bãrik liy feehi, wa in kunta ta'lamu anna hazal amra sharrun liy fii deeniy wama'ãshiy wa ãqibati amriy fasrifhu anniy wasrifniy anhu, waqdur liyal khaira haithu kaana, thumma ardiniy bihi.
FASSARAN ADDU'AR: Ya Allah Ina neman zabinka domin iliminka, kuma ina neman Ka ba ni iko domin Ikonka, kuma ina rokonKa daga falalarKa Mai girma, domin Kai ne mai iko, ni ba ni da iko, kuma Kai ne Masani, ni kuwa ban sani ba, kuma Kai ne masanin abubuwan gaibu. Ya Allah! Idan Ka san cewa wannan al'amarin (Sai ya ambaci bukatan na shi) alkhairi ne a gare ni a cikin addinina, da rayuwana, da kuma karshen al'amarina, (A wata riwayar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa) Ka kaddarta mini shi, kuma Ka saukake mini shi, sannan Ka albarkace ni a cikin sa. Idan kuma Ka san wannan al'amarin sharri ne a gare ni a cikin addinina, da rayuwana, da karshen al'amarina, (A wata riwayar; da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa) Ka kawar da shi daga gare ni, kuma Ka kawar da ni daga gare shi, kuma Ka kaddarta mini alkhairi a duk in da ya ke, sa'annan Ka sanya mini yarda da shi".
________________
●Shaykhul Islami Ibnu Taimiya(RA) ya ce: Mas'ala game da addu'ar Istikhara, shin a na yinta ne a cikin sallar ko bayan sallama a ke yinta? Ya ce: Ya halatta a yi addu'an a cikin sallar Istikhara ko a waninsa, kafin sallama ko bayan sallama, Amma addu'an kafin yin sallama shi ya fi falala, domin Manzon Allah(SAW) mafi yawa addu'oinsa kafin sallama ne, kuma mai sallah kafin sallama bai riga ya idar ba yana cikin sallah, to wannan shi ya fi kyau. Wallahu aalam
(الفتاوى الكبرى: ج2/ ص265)
●Wasu malamai kuma suna ganin yin addu'an bayan sallama shi ya fi, almuhim duk wanda ka yi yayi in sha Allah.
●A na yinta ne a lokutan da ba a hana yin nafila ba, Shaykh Ibnu Uthaimeen(RA) ya ce: "Sallar Istikhara idan na wani al'amarine na gaggawa da ba za a iya jinkirtashi zuwa lokacin hanin nafila ya fita ba to za a sallace ta haka nan, amma idan sababin yinta din zai yiwu a jinkirta (ma'ana al'amarin ba na gaggawa bane) to wajibi ne a jinkirta(har zuwa lokacin da ba a hana yin nafila ba).
(مجموع فتاوى ابن عثيمين 14/275).
●Wani ba ya yi ma wani Istikhara, kuma ba gani a ke yi a mafarki ba!
Duk wanda yayi shawara da amintattu kuma masana, sa'annan ya nemi zabin mahaliccinsa, kuma ya yi azama a cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin Allah madaukakin sarki Ya ce;
(وَشَاوِرْهُمْ فِي اْلأَمْرِ فَإِذَا عَزَمْتَ فَتَوَكَّلْ عَلَى اللهِ)
"Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka kuduri aniya, to ka dogara ga Allah".
30/06/2024
HALIN DA MUKE CIKI A YANZU BABU MAKAWA LAIFINMU NE KUMA SAI MUN GYARA ZA MUGA SAUYI.
Lallai Allah yana faɗa a cikin littafinsa mai girma (Alkur'ani) da cewa.
"Duk abinda ya shafe ku na musiba, to cikin abinda hannayenku ne s**a janyo ne, kuma Allah yana yin afuwa ga da yawa daga ciki" (Shurah 30).
Ya kuma faɗa a wata ayar.
" .... Lallai Allah baya canjawa mutane halin da suke har sai sun canza abinda ke cikin zukatansu...(Ra'ad 11).
Haka nanma Imam Ibn Majah ya fitar da hadisi a cikin sunan nashi a hadisi na 4019 wanda salsalar hadisin ta tuƙe zuwa ga sahabi Abdullahi Ɗan Umar (Radhiyallahu Anhu) ya ce wata rana Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam) ya fuskance mu, sai yace: Ya ku taron mahajirai, abubuwa guda biyar idan aka jarrabeku da su, Ina roƙon Allah tsari da kada ku riskesu.
1. Alfasha ba zata yaɗuba cikin al'umma har su rinƙa bayyanata face annoba ta yaɗu a cikinsu, da cututtukan da al'ummomin da s**a wuce basu sansu ba.
2. Mutane ba zasu tauye mauni ba face sai an jarrabesu da fari (ƙarancin ruwan sama) da tsadar rayuwa da zaluncin shuwagabanni.
3. Mutane ba zasu hana zakkar duniyoyinsu ba face Allah ya hana masu ruwan sama, ba don dabbobi ba da ko ruwan saman ba za a yi ba.
4. Mutane ba zasu canja alƙawarin Allah da alƙawarin Manzon Allah ba face sai Allah ya ɗora maƙiyansu akansu waɗanda ba suba,sashensu ya rinƙa karɓar abinda ke hannun sashe.
5. Shuwagabanninsu ba zasu bar hukunci da littafin Allah ba suna zaɓar abinda Allah ya saukar subar wani sashe fashe Allah ya sanya faɗace-faɗace a tsakaninsu.
Don haka ya ƊAN UWA MAI ALBARKA, cikin waɗannan laifuffukan da Annabi (Alaihis Salatu wassalām) ya lissafo wannene ni da kai bama aikatawa? Don haka sai na gyara, sai kaima ka gyara sai muga gyara da sauyi daga wajen Allah.
ALLAH muke roƙo da ya bamu ikon ganin kusakuranmi ya bamu ikon gyarawa. Allah ka bamu lafiya da zama lafiya ya kawo mana sauƙi cikin halin da muke ciki na matsalar tsaro da ƙuncin rayuwa.
✍️ AbūMuhsin Ɗāhiru Diss
15/06/2024
Yau take ranar Arfah mafi alkhairin wuni a wajen Allah. Wunin da yake baƙantawa shaidan rai yake kuma kunyata shi.
Ya Ɗan uwa mai albarka daure ka ƙawata wannan wuni naka da yawaita faɗin kalmar.
لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير.
Daure ka yawaita addu'a, domin addu'ar irin wannan rana karɓaɓɓiya ce.
Allah muke roƙo albarkacin wannan rana da ya karɓi ayyukanmu da addu'o'inmu ya biya mana buƙatunmu ya yaye mana damuwoyinmu.