Building Your Future Ambassadors

Building Your Future Ambassadors

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Building Your Future Ambassadors, Political organisation, Katsina.

04/06/2026

🎉 Facebook recognized me as a consistent post creator this week!

04/06/2026

A visit to Alhaji Abdulƙadir Mamman Nasir - the Chief of Staff to the Governor of Katsina State Dr. Dikko Umaru Radda

Photos from Building Your Future Ambassadors's post 04/06/2026

BYFA Ta yi Na Musamman da Shugaban Fadar Gwamnati domin Gabatar da Wani Muhimmin Tsarin da zai Taimaka wa Nasarar Gwamna RaÉ—É—a a 2027

Darakta Janar na Building Your Future Ambassadors (BYFA), wadda a baya ake kira Dikko Vision Movement (DVM), Dr. Isah Rabe Kambarawa ya gudanar da wata muhimmiyar ganawa ta musamman da Shugaban Ma'aikata na Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdulƙadir Mamman Nasir, a Fadar Gwamnatin Jihar Katsina.

Ganawar ta mayar da hankali ne kan hanyoyin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin BYFA da gwamnatin jihar wajen tallata manufofi da nasarorin gwamnatin Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda, CON, tare da tabbatar da dorewar manufofin ci gaba da ke ƙarƙashin Tsarin "Gina Makomarka".

A yayin tattaunawar, Darakta Janar na BYFA ya gabatar da wani muhimmin tsari da ƙungiyar ta tanada wanda aka tsara domin ƙarfafa wayar da kan al'umma game da ayyukan gwamnati da kuma samar da ƙarin goyon bayan jama'a ga gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Ya bayyana cewa BYFA ta ƙudiri aniyar ci gaba da kasancewa a gaba wajen wayar da kan al'umma kan manufofi, shirye-shirye da nasarorin gwamnatin jihar, tare da ƙarfafa matasa, mata da sauran al'ummomi su ci gaba da mara wa gwamnati baya domin tabbatar da ɗorewar ayyukan ci gaba da ake aiwatarwa a faɗin jihar.

Da yake jawabi a yayin ganawar, Shugaban Ma'aikata na Fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdulƙadir Mamman Nasir, ya yaba da hangen nesa da jajircewar shugabannin BYFA wajen samar da sabbin hanyoyi na tallafawa manufofin gwamnati da kuma ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnati da jama'a.

Ya bayyana shirin da ƙungiyar ta gabatar a matsayin wani muhimmin mataki da zai taimaka wajen ƙara wayar da kan al'umma game da nasarorin gwamnatin jihar, yana mai cewa ya yi daidai da manufofi da shirye-shiryen gwamnati na bunƙasa walwala da ci gaban al'ummar Katsina.

Shugaban Ma'aikatan ya kuma tabbatar da shirye-shiryen Fadar Gwamnati na yin aiki kafaÉ—a-da-kafaÉ—a da BYFA domin tabbatar da nasarar duk wani tsari da zai amfani al'umma tare da taimakawa wajen ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatin Malam Dikko Umaru RaÉ—É—a, PhD, CON.

Darakta Janar na BYFA ya samu rakiyar Daraktan Mulki na ƙungiyar, Hon. Sadiq Abdullahi Gwarjo, yayin wannan muhimmiyar ziyara.

Har ila yau, zaman ya samu halartar wasu manyan jami'an gwamnati da s**a haɗa da Sakatarorin Dindindin na Fadar Gwamnati da kuma Ma'aikatar Lamuran Mata, lamarin da ya ƙara nuna muhimmancin tattaunawar da aka gudanar.

Ganawar ta gudana cikin yanayi na fahimtar juna, haɗin kai da kyakkyawan fata kan makomar jihar, inda ɓangarorin biyu s**a jaddada aniyarsu ta ci gaba da aiki tare domin tallafawa manufofin ci gaba da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.

Sanarwa:
Daraktan YaÉ—a Labarai da Sadarwa
Building Your Future Ambassadors (BYFA)
Alhamis, 4 ga Yuni, 2026
18 ga Zul-Hijjah, 1447AH

Hannatu Musa Musawa
Alh. Ibrahim Kabir Masari
Aminu Bello Masari
Katsina State Government
Katsina State Television KTTV
Katsina State Radio Service -KTRS
Renewed Hope Katsina State
City Boy Movement Katsina State
GMTD

01/06/2026

The Architect of Renewed Hope Agenda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Dr. Dikko Umaru Radda
Seyi Tinubu
Renewed Hope Katsina State
City Boy Movement Katsina State

01/06/2026

Jagoran Tsarin Manufar Cigaba na Gina Makomarka
Dr. Dikko Umaru Radda

01/06/2026

Mujallar Gina Makomarka (MGM)
Fitowa ta 40

Dr. Dikko Umaru Radda

Photos from Building Your Future Ambassadors's post 01/06/2026

Mujallar Gina Makomarka [MGM]:
Fitowa - Arba'in [40]
Adadin Shafuka - 44

Wannan Mujalla na ƙunshe da muhimman batutuwa da kuma aikace-aikacen Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Dr. Dikko Umaru Radda, CON, da aka aiwatar a makon da ya gabata, daga Litinin, 25 zuwa Lahadi, 31 ga Mayu, 2026.
Duka wannan na a matsayin sakamakon yanda ake aiwatar da Tsarin Manufar Cigaba na Gina Makomarka (Building Your Future Strategic Policy - BYFSP) wanda shi ne ruhin Gwamnatin Jihar Katsina ta Mai girma Malam Dikko Umaru RaÉ—É—a, PhD, CON.

Sanarwa:
Daraktan YaÉ—a Labarai da Sadarwa
Building Your Future Ambassadors [BYFA]
Litinin, 1 ga Yuni, 2026
15 ga Dhul-Hijjah, 1447

Katsina State Government
Katsina State Television KTTV
Katsina State Radio Service -KTRS
Renewed Hope Katsina State
City Boy Movement Katsina State
GMTD

30/05/2026

Congratulations Your Excellency Dr. Dikko Umaru Radda

30/05/2026

Muna mika saƙon taya murna da jinjina ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda CON, a yayin da gwamnatinsa ta cika shekaru uku kan karagar mulki a yau, Juma’a 29 ga Mayu, 2026.

A cikin waɗannan shekaru uku, gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa ta nuna ƙwazo, hangen nesa da jajircewa wajen aiwatar da Tsarin Manufar Cigaba na Gina Makomarka (Building Your Future Strategic Policy), wanda ya zama ginshiƙin ci gaba da sauyin alheri a Jihar Katsina.

Mun shaida gagarumin ci gaba a muhimman ɓangarorin takwas na tsarin, wato:
✓ Gyaran Tsarin Gudanar da Ayyukan Gwamnati
✓ Ilimi da Bunƙasa Ƙwarewa
✓ Kula da Jin Daɗin Al’umma
✓ Ƙananan da Matsakaitan Sana’o’i (MSMEs) da Tattalin Arzikin Cikin Gida
✓ Kiwon Lafiya
✓ Noma da Bunƙasa Masana’antu
✓ Tsaro
✓ Kuɗaɗen Shiga na Cikin Gida (IGR)

Muna yi wa Mai Girma Gwamna fatan kammala wannan wa’adi lafiya, cikin nasara da ɗaukaka a shekarar da ta rage.

Haka kuma, muna yi masa fatan samun gagarumar nasara a zaɓen Gwamnan Jihar Katsina na shekarar 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar APC, domin ci gaba da aikin gina makomarka da bunƙasa rayuwar al’ummar jihar, In Allah Ya yarda.

Allah Ya ƙara ba ka ƙarfi, lafiya, hikima da basirar jagoranci domin ci gaba da hidimtawa al’ummar Jihar Katsina.

Sanarwa:
Daraktan YaÉ—a Labarai da Sadarwa
Building Your Future Ambassadors (BYFA)

Juma’a, 29 ga Mayu, 2026
12 ga Dhul-Hijjah, 1447

Katsina State Government
Hannatu Musa Musawa
Alh. Ibrahim Kabir Masari
Aminu Bello Masari
Renewed Hope Katsina State
City Boy Movement Katsina State





Want your business to be the top-listed Government Service in Katsina?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address


Katsina
820