Building Your Future Ambassadors' Initiative

Directions

Building Your Future Ambassadors' Initiative Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Building Your Future Ambassadors' Initiative, Political organisation, Katsina.

11/10/2026

Rana ta Uku (3) na Rangadin Jiha na BYFAI a Shiyyar Katsina

Isowar tawagar BYFAI ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar kuma Ko'odinetan Jiha na Bikin Sana'oi, Dr. Isah Rabe Kambarawa, CPM, CPD, CHRM, a Fadar Magajin Malam Hakimin Ɗanmusa, Alhaji Darda'u Mu'azu, domin ganawa da masu sana'o'in hannu, a cigaba da shirye-shiryen Bikin Sana'oin Hannu na Jihar Katsina (1.0).

Labari cikin Hotuna:Ziyarar tawagar rangadin Bikin Sana'oi na Jiha ƙarƙashin Building Your Future Ambassadors' Initiativ...
10/10/2026

Labari cikin Hotuna:

Ziyarar tawagar rangadin Bikin Sana'oi na Jiha ƙarƙashin Building Your Future Ambassadors' Initiative (BYFAI) a masana'antar ƙere-ƙere na kayayyakin ƙasar laka mai suna Better Life da ke a Ajiwa.

BUILDING YOUR FUTURE AMBASSADORS' INITIATIVE (BYFAI)SANARWAR MANEMA LABARAITAWAGAR RANGADIN BIKIN SANA’O’IN HANNU TA ISA...
10/10/2026

BUILDING YOUR FUTURE AMBASSADORS' INITIATIVE (BYFAI)

SANARWAR MANEMA LABARAI

TAWAGAR RANGADIN BIKIN SANA’O’IN HANNU TA ISA ƁATAGARAWA, MAHAIFAR KO'ODINETAN SHIYYAR KATSINA

Tawagar Rangadin Bikin Sana’o’in Hannu ta Jihar Katsina ta isa Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa, mahaifar Ko'odinetan Bikin Sana’o’in Hannu na Shiyyar Katsina, Ambasada Mubarak Sale Bakiyawa, a rana ta biyu ta rangadin shiyyar, domin ganawa da masu sana’o’in hannu da kuma cigaba da wayar da kansu kan shirye-shiryen Bikin Sana’o’in Hannu na Jihar Katsina.

Ziyarar ta kasance wani muhimmin mataki na cigaba da rangadin Shiyyar Katsina, tare da kai wannan shiri zuwa mahaifar Ko'odinetan shiyyar domin tattaunawa da masu sana’o’in hannu da ƙarfafa musu gwiwa su kasance cikin masu cin gajiyar damar da bikin zai samar.

Tawagar ta samu tarba daga Ko'odinetan Bikin na Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa, Ambasada Ibrahim Ali, tare da Ko'odinetocin mazaɓu 10 na ƙaramar hukumar.

Da yake gabatar da jawabin maraba da baƙi, Ambasada Ibrahim Ali ya bayyana farin cikinsa da zuwan tawagar, tare da miƙa godiya ga Kwamitin Rangadin Jiha bisa ziyartar ƙaramar hukumar da kuma ƙoƙarin da yake yi na wayar da kan masu sana’o’in hannu kan muhimmancin bikin.

A yayin taron, ’yan Kwamitin Rangadin Jiha, Ambasada Yusha’u Salisu Zakariya da Ambasada Binta Isah, sun gabatar da muhimman jawabai kan muhimmancin sana’o’in hannu ga mata, matasa da al’umma baki ɗaya.

Sun bayyana cewa sana’o’in hannu na da muhimmiyar rawa wajen samar da dogaro da kai, ƙarfafa tattalin arzikin iyalai, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa ƙwarewar matasa. Sun kuma ƙarfafa gwiwar mata da matasa da su rungumi sana’o’in hannu, su inganta ƙwarewarsu, tare da amfani da damammakin da ke akwai wajen bunƙasa sana’o’insu da inganta rayuwarsu.

Daga bisani, Shugaban Tawagar Rangadin Jiha kuma Shugaban Kwamitin Bikin, Dakta Isah Rabe Kambarawa, ya gabatar da cikakken bayani kan Bikin Sana’o’in Hannu na Jihar Katsina, musamman dangane da tsare-tsaren gudanar da bikin da kuma manufar Katsina Crafts & Creative Economy Development Project (2026–2030).

Dakta Kambarawa ya bayyana cewa Katsina Crafts & Creative Economy Development Project (2026–2030) ya ƙunshi shirye-shirye guda 12 da aka tsara domin bunƙasa sana’o’in hannu da tattalin arziƙin ƙirƙira a Jihar Katsina, inda Katsina Crafts Festival, wato Bikin Sana’o’in Hannu na Jihar Katsina, ya kasance shiri na farko cikin waɗannan shirye-shirye.

Ya ƙara da cewa wannan shiri ya yi daidai da Ginshiƙai na 2 da na 4 na Tsarin Manufar Cigaba na Gina Makomarka (Building Your Future Strategic Policy – BYFSP), wanda ya kasance ruhin tsare-tsaren cigaban Katsina State Government ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda, CON.

Shugaban tawagar ya jaddada muhimmancin haɗa masu sana’o’in hannu, musamman mata da matasa, cikin shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziƙin ƙirƙira. Ya bayyana cewa irin waɗannan shirye-shirye na da damar ƙarfafa ƙwarewar masu sana’o’i, inganta kayayyakin da suke samarwa da kuma faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa, Honourable Yahaya Lawal Kawo, wanda Shugaban Majalisar Kansiloli, Alhaji Abubakar Muntari Ajiwa, ya wakilta, ya miƙa godiyarsa ga tawagar bisa ziyarar da ta kawo ƙaramar hukumar.

Ya kuma bayyana goyon bayan Gwamnatin Ƙaramar Hukumar Ɓatagarawa ga shirye-shiryen Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa wajen aiwatar da shirye-shiryen cigaban al’umma.

Shi ma Ko'odinetan Bikin Sana’o’in Hannu na Shiyyar Katsina, Ambasada Mubarak Sale Bakiyawa, ya yi godiya ga Tawagar Rangadin Jiha bisa ci gaba da rangadin shiyyar da kuma kai ziyara Ɓatagarawa, mahaifarsa. Ya bayyana fatansa na ganin an kammala rangadin cikin nasara da lafiya, tare da samun cikakken haɗin kai daga shugabannin ƙananan hukumomi, Koodinetocin mazaɓu da masu sana’o’in hannu domin tabbatar da nasarar bikin.

A yayin taron, an bai wa ɗalibai, malamai da sauran mahalarta damar gabatar da tambayoyi da bayyana ra’ayoyinsu kan bikin da kuma irin damar da shirin zai samar. Shugaban tawagar ya ba da ƙarin bayani kan batutuwan da aka gabatar, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai wajen cimma manufofin shirin.

Ziyarar Ɓatagarawa ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Kwamitin Rangadin Jiha, shugabannin ƙaramar hukuma, Ko'odinetocin mazaɓu da masu sana’o’in hannu, tare da cigaba da wayar da kan al’umma game da manufar Bikin Sana’o’in Hannu na Jihar Katsina da muhimmancinsa wajen bunƙasa tattalin arziƙin ƙirƙira.

Sanarwa:
Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa
Building Your Future Ambassadors' Initiative (BYFAI)
10 ga Oktoba, 2026
28 ga Rabi'ut-Thaniy, 1448

10/10/2026

Ziyarar tawagar Jiha ta BYFAI a masana'antar ƙere-ƙere ta Better Life a Ajiwa.

10/10/2026

A kan hanyarmu ta zuwa masana'antar ƙere-ƙere ta Better Life a Ajiwa a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Ɓatagarawa jim kaɗan bayan ganawa da masu sana'oin hannu na Ɓatagarawar, tawagar rangadin Bikin Sana'oi na Jihar Katsina ta Building Your Future Ambassadors' Initiative (BYFAI) ta haɗu da ayarin Mai girma Durɓin Katsina Hakimin Gundumar Mani, inda ta tsaya domin gaisuwar ban girma.
Allah Ya ƙara wa Durɓi lafiya da kwanuka masu albarka.

10/10/2026

Ziyarar Bangirma:

Isowar Tawagar Rangadi ta BYFAI ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Dr. Isah Rabe Kambarawa a Fadar Mai Martaba Malamawan Katsina Hakimin Gundumar Ɓatagarawa, Alhaji Muhammad Dikko Ɗalhatu, wanda ya samu wakilcin Alhaji Musa Ɗalhatu.

10/10/2026

Rana ta Biyu (2) na Rangadin Jiha na BYFAI a Shiyyar Katsina

Isowar tawagar BYFAI ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar kuma Ko'odinetan Jiha na Bikin Sana'oi, Dr. Isah Rabe Kambarawa, CPM, CPD, CHRM, a ƙaramar hukumar Ɓatagarawa domin ganawa da masu sana'o'in hannu, a cigaba da shirye-shiryen Bikin Sana'oin Hannu na Jihar Katsina (1.0).

10/10/2026

Ziyarar jajantawa zuwa ga Maigarin Ɗangamau, Alhaji Aminu Boko, sakamakon jarabawar harin 'yan bindiga da ya faru a garin.
Da fatan Allah Ya ƙara mana zaman lafiya.

Labari cikin Hotuna:Ziyarar ban girma zuwa ga Sarkin Shanun Katsina, Hakimin Gundumar Charanchi, Alhaji Abashe Abdulƙadi...
10/10/2026

Labari cikin Hotuna:
Ziyarar ban girma zuwa ga Sarkin Shanun Katsina, Hakimin Gundumar Charanchi, Alhaji Abashe Abdulƙadir, a wani ɓangare na shirye-shiryen gudanar da Bikin Sana'oi na Hannu na Jihar Katsina wanda Katsina State Government ta ɗauki nauyi ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dr. Dikko Umaru Radda, CON.

BUILDING YOUR FUTURE AMBASSADORS' INITIATIVE (BYFAI)SANARWAR MANEMA LABARAITAWAGAR RANGADIN BIKIN SANA’O’IN HANNU TA ISA...
10/10/2026

BUILDING YOUR FUTURE AMBASSADORS' INITIATIVE (BYFAI)

SANARWAR MANEMA LABARAI

TAWAGAR RANGADIN BIKIN SANA’O’IN HANNU TA ISA CHARANCHI, MAHAIFAR GWAMNA RAƊƊA

Tawagar Rangadin Bikin Sana’o’in Hannu ta Jihar Katsina ta isa Ƙaramar Hukumar Charanchi, mahaifar Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, PhD, CON, a rana ta biyu ta rangadin Shiyyar Katsina, domin ganawa da masu sana’o’in hannu da kuma cigaba da wayar da kansu kan shirye-shiryen Bikin Sana’o’in Hannu na Jihar Katsina.

Tawagar ta samu tarba daga Ko'odinetan Bikin na Ƙaramar Hukumar Charanchi, Ambasada Bishir Abdu, tare da Ko'odinetocin mazaɓu 10 na ƙaramar hukumar.

Da yake gabatar da jawabin maraba da baƙi, Ambasada Bishir Abdu ya nuna farin cikinsa da zuwan tawagar, tare da miƙa godiya ga Kwamitin Rangadin Jiha bisa ziyartar ƙaramar hukumar da kuma ƙoƙarin da yake yi na wayar da kan masu sana’o’in hannu game da muhimmancin bikin.

A yayin taron, ’yan Kwamitin Rangadin Jiha, Ambasada Yusha’u Salisu Zakariya da Ambasada Fatima Bala, sun gabatar da muhimman jawabai kan muhimmancin sana’o’in hannu ga mata, matasa da al’umma baki ɗaya.

Sun bayyana cewa sana’o’in hannu na daga cikin muhimman hanyoyin samar da dogaro da kai, bunƙasa tattalin arziƙin iyalai, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa ƙwarewar matasa. Sun kuma ƙarfafa gwiwar mata da matasa da su rungumi sana’o’in hannu, su inganta ƙwarewarsu, tare da amfani da damammakin da ke akwai wajen bunƙasa sana’o’insu da inganta rayuwarsu.

Daga bisani, Shugaban Tawagar Rangadin Jiha kuma Shugaban Kwamitin Bikin, Dakta Isah Rabe Kambarawa, ya gabatar da cikakken bayani kan Bikin Sana’o’in Hannu na Jihar Katsina, musamman dangane da tsare-tsaren gudanar da bikin da kuma manufar Katsina Crafts & Creative Economy Development Project (2026–2030).

Dakta Kambarawa ya bayyana cewa Katsina Crafts & Creative Economy Development Project (2026–2030) ya ƙunshi shirye-shirye guda 12 da aka tsara domin bunƙasa sana’o’in hannu da tattalin arziƙin ƙirƙira a Jihar Katsina, inda Katsina Crafts Festival, wato Bikin Sana’o’in Hannu na Jihar Katsina, ya kasance shiri na farko cikin waɗannan shirye-shirye.

Ya ƙara da cewa wannan shiri ya yi daidai da Ginshiƙai na 2 da na 4 na Tsarin Manufar Cigaba na Gina Makomarka (Building Your Future Strategic Policy – BYFSP), wanda ya kasance ginshiƙin tsare-tsaren cigaban Katsina State Government ƙarƙashin jagorancin Malam Dr. Dikko Umaru Radda, CON.

Shugaban tawagar ya jaddada muhimmancin haɗa masu sana’o’in hannu, musamman mata da matasa, cikin shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziƙin ƙirƙira, yana mai bayyana cewa irin waɗannan shirye-shirye na iya samar da damammakin haɓaka ƙwarewa, tallata kayayyakin sana’o’i da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga.

A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Charanchi, Honourable Sani Ibrahim Koɗa wanda Sakataren Ƙaramar Hukumar, Alhaji Aminu Isyaku, ya wakilta, ya miƙa godiyarsa ga tawagar bisa ziyarar da ta kawo ƙaramar hukumar.

Ya kuma bayyana goyon bayan Gwamnatin Ƙaramar Hukumar Charanchi ga shirye-shiryen Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, PhD, CON, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa wajen aiwatar da shirye-shiryen da aka tsara domin cigaban al’umma.

Shi ma Koodinetan Bikin Sana’o’in Hannu na Shiyyar Katsina, Ambasada Mubarak Sale Bakiyawa, ya gode wa Tawagar Rangadin Jiha bisa ci gaba da rangadin a shiyyar, tare da kai ziyara Ƙaramar Hukumar Charanchi a wannan rana ta biyu.

Ya bayyana fatansa na ganin an kammala rangadin cikin nasara da lafiya, tare da samun cikakken haɗin kai daga shugabannin ƙananan hukumomi, Koodinetocin mazaɓu da masu sana’o’in hannu domin tabbatar da nasarar bikin.

A yayin taron, an bai wa mahalarta damar gabatar da tambayoyi, ra’ayoyi da shawarwari dangane da bikin da kuma damar da zai samar wa masu sana’o’in hannu. Shugaban tawagar ya ba da ƙarin bayani kan batutuwan da aka gabatar, tare da jaddada muhimmancin haɗin kai wajen cimma manufofin shirin.

Ziyarar Charanchi ta kasance wani muhimmin mataki na ci gaba da rangadin Shiyyar Katsina, wanda ke da manufar kusantar masu sana’o’in hannu a matakin ƙananan hukumomi da mazaɓu, domin wayar da kansu da ƙarfafa shigarsu cikin shirye-shiryen Bikin Sana’o’in Hannu na Jihar Katsina.

Sanarwa:
Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa
Building Your Future Ambassadors' Initiative (BYFAI)
10 ga Oktoba, 2026
28 ga Rabi'ut-Thaniy, 1448

Address

Katsina
820

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Building Your Future Ambassadors' Initiative posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share