02/10/2026
ALHAJI BABALLE JAJI (MARAFAN YAMMA NA POTISKUM) NA ISAR DA FATAN ALHERI DA ADDU’AR ZAMAN LAFIYA GA AL’UMMA:
Alhaji Baballe Jaji, (Marafan Yamma na Potiskum), na isar da sakon fatan alheri ga al’umma, tare da yin addu’ar samun zaman lafiya, hadin kai, da tausayi a tsakanin jama’a.
Baballe Jaji, ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da kasancewa masu hakuri, mutunta juna da taimakon juna, domin zaman lafiya shi ne ginshikin ci gaba da wadata.
ALLAH Ya tabbatar da zaman lafiya a Potiskum, da Yobe da Najeriya baki Daya.