SABON SALON Soyayya MAZA DA MATA - arewa Online

SABON SALON Soyayya MAZA DA MATA - arewa Online

Share

Computer Storage

09/05/2023

Wani Dattijo yace wa daya daga cikin jikokin sa:-
Ya kai dana, Lalle shiga Aljanna kyauta ne, Amma wuta sai an biya kudi ake shiga.
Sai yaron yace:-
Ya haka yake kasancewa ya kaka na😳!?
Sai kakan yace:-
Duk wanda zai yi c**a (karta) sai ya biya kudi,
Kuma duk wanda zai sha giya sai ya biya kudi,
Duk wanda zai busa taba sigari ko wiwi ko shi-sha sai ya biya kudi,
Kuma duk wanda yake son ya ji waka sai ya biya kudi,
Kuma duk wanda yake son ya yi tafiya dan 6arna da alfa'sha sai ya biya kudi.
Amma Aljanna yakai dana kyauta ne, ba a kashe kudi dan shigan ta,
Duk mai yin sallah zai yi sallah ba tare da ya biya kudi ba,
Kuma duk wanda zai yi azumi ba sai ya biya sisi ba,
Kuma duk wanda zai yi Istigfari zaiyi ba sai ya biya sisi ba,
Haka Kuma duk wanda zai rintsa ganin sa daga haram ba sai ya biya sisi ba.
To ya kai dana, shin kana son ka kashe kudin ka dan ka shiga wuta ko kana son Aljanna kyauta?

Kai me karatu wannan sakon ya iso gareka kyauta, kai ma ka tura wa wani ya samu kyauta dan ka samu ladan haka.
ALLAH sa mu dace.

09/05/2023

Kamar yadda Allah ya halicce mu da hagun da dama, haka aka sanya mana gamuwa da farin ciki ko damuwa a zukatanmu.

Haƙiƙa akwai ƙunci, damuwa, matsi da matsaloli da ɗan adam ke fuskanta a rayuwarsa, amma mu sani duk yana faruwa sak**akon nisantar hanyoyin warware matsalolin cikin aiyukanmu da furucinmu.

Idan kana son samun sauƙin damuwa, da samun rayuwa cikin walwala da farin ciki, da samun zaman lafiya to ka kiyaye waɗannan:

1. Mayar da komi ga Allah da tawakkali cikin duk abinda ya same ka mai daɗi ko maras daɗi.

2. Yawan tilawar ƙur’ani da bibiyarsa a zuciyarka safiya da maraice.

3. Cire hassada da ƙyashi a zuciyarka, duk abinda wani ya samu ba rabonka ba ne, kuma Allah ne ke ɗaukaka kowa, ka kyautata zato ga Allah ka jira naka rabon.

4. Nisantar dogon buri, da kwaɗayin komi, da tsananin neman tara duniya ta kota halin ƙaƙa.

5. Yawan salati ga Annabi (ﷺ), kuma ka haɗa da bin sunnar Annabi (ﷺ) cikin aiyukanka da maganganunka.

6. Yawan addu’a da neman falalar Allah cikin dukkan buƙatunka.

7. Zama da mutanen kirki, da koyi da magabata na ƙwarai, da yawan halartan tarukan bada ilimi, da wuraren wa’azi.

8. Nisantar miyagun aiyuka, musamman aikata zunubi da ganganci.

9. Riƙe sirrinka da sirrin waninka cikin dukkan al’amuran rayuwarka musamman kiyaye yawan fallasa manufofinka, ko watsa zancen wani ga jama’a.

10. Tsayawa kan halal cikin cin abincinka, da tara dukiyarka da hanyoyin sarrafa duk abinda ka mallaka.

11. Tausayi, da nuna jin ƙai ga masu rauni, miskinai, marayu da marasa gata. Wato ciyar da dukiyarka ga mabuƙata.

12. Sada zumunta, yawan alheri ga na kusa da kai, da na nesa, kuma ka rayu cikin sassauci da saurin afuwa da yafe laifi ga makusanta da duk waɗanda Allah ya haɗa ka zama da su.

Haƙiƙa in ka riƙe waɗannan za ka sami cikakkiyar natsuwa, hutawar zuciya da samun rayuwa mai daɗi a duniya da lahira.
________________________
Allah sa mu dace. Amin

11/01/2023

SAURARA KAJI.
-
"Akwai mutane da yawa a kafafen sada zumunta waɗanda ko da da barkwanci s**a yi posting, to za kaga ka sami wata fa'ida a cikin rubutun su, za ka tarar akwai koyarwa ta addinin musulunci a cikinsa wanda musulmi zai amfana a ciki, to haƙiƙa muna goyon bayan a dinga bibiyar ire-irensu"
-
"Akwai waɗanda kuwa duk wani motsinsu a social media, to ba karantarwa bace, kawai suna yi ne don son burgewa da agani kuma a yaba musu, to haƙiƙa ba ma goyon bayan ka dinga bibiyarsu, domin haƙiƙa babu wani alfanu a tattare dasu"
-
"Ka daure a wannan duniyar ta zahiri ko ta social media ka kasance wanda al'umma za su dinga amfana da ilminka wajen gyatta tsakaninsu da mahaliccinsu, kada ka zamto wanda kawai burinsa ya dinga ba wa mutane dariya a kafar sadarwa, haƙiƙa wannan taɓewa ce a gareka"
-
Allah ta'ala yasa mu dace baki ɗaya.
- 𝐈𝐬𝐦𝐚'𝐢𝐥𝐚 𝐌𝐮𝐬𝐚~✍🏽

28/11/2022

Motsin da yafi kowanne
sauki
gareka shine MOTSA
HARSHENKA.

Amma kuma yafi
kowanne hatsari da cutarwa a
gare ka
idan baka kiyayeshi shi
ba!

Ya Rabb ka Tseratar
Damu Daga Sharrin Harshanmu!

DUNIYA
MAKARANTA!

28/11/2022

DUNIYA
MAKARANTA
"Da ace bankuna suna cire
mana kudi idan mukaci
naman wani su jefa a
Account dinsa, da mun k**a kanmu. Amma da
yake ladarmu ake cirewa
bamu ji sam, ko a
jikinmu".
Abunda yafi komai
takaici a alkiyama shine ga ladarka, baka iya
bawa iyayenka da
'ya'yanka da masoyanka
amma kana kallo za'a
dauka a bawa makiyanka
don kaci namansu ko ka zaluncesu.
Allah ya shirye mu,
Allah yasa mu gane.

28/11/2022

*ABUBUWA GUDA
UKU SUNE SIRRIN
SAMUN AMINCI A
RAYUWAN DUNIA
DA LAHIRA*
1- Cin Halas da nisantar Haramun.
2- Yawaita Tuba da
Istigfari.
3- Riko da Sunnah da
nisantar Bidi'ah.

28/11/2022

Na san cewa MUTUWA
na jira na, don haka sai
nake ta tanadin GUZURI
na KWARAI don shirin
GAMUWA da
UBANGIJINA. Š Imam Hasanul
Basariy (Rahimahullah)
Ina mai roka mana Allah
ya yafe mana
kurakurenmu baki daya..

28/11/2022

TUFAFI su ne
SUTURARKA ta
ZAHIRI,
TSORON ALLAH shi
ne SUTURARKA ta
BADINI. Yi kokari ka gyara ciki
da wajenka...
DUNIYA MAKARANTA

28/11/2022

Idan kana Jiran Godiya
da Sakayya Daga
Mutane Babu Shakka
Zaka Sha Mamaki!
Yi kokari kayi komai
Dan Allah!
DUNIYA MAKARANTA

28/11/2022

Idan kana tafiya babu takalmi zaka gamu da wanda yake tafiya ba kafafu;kalli wanda ka fishi a kullum sai ka godewa ubangiji
DUNIYA MAKARANTA

28/11/2022

DUNIYA MAKARANTA

1- A lokacin da ka koshi
ne wani yake jin yunwa.
2-Lokacinda kake da
lafiya sannan wani yake
ciwo. Idan ka samu aminci wani yana cikin
tsoro. Haka duniya take;
yau gare ka, gobe ga dan
uwanka.
3- Ba da hakuri ba yana
tabbatar da yin laifi bane, amma yana nuna
rashin girman kai da
neman a zauna lafiya.
4- Duk mutane idan s**a
mutu suna komawa ga
Allah ne. Amma masu imani tun a nan duniya
suke komawa gare shi.
5- Idan rana ta fito
mutane s**an manta
fitilun da suke haskaka
titunan gari da daddare. Kada ka yi mamaki idan
ka yi alheri a yau zuwa
gobe an manta. Wannan
dabi'a ce ta dan Adam.
6- Idan ka samu alheri
fada ma wanda kake so. Idan ka gamu da bala'i
fada ma wanda ke son
ka.
7- Turawa ba su fi mu
basira da hankali ba.
Banbancin mu da su guda daya ne: Su s**an
karfafi mai rauni a cikin
su har sai ya yi kwari, su
taimaki mai basira har ya
ida kwarewa. Mu kuma
muna raunana mai karfi ne a cikinmu, mu dakile
mai basira har sai ya
dallashe.
8- Sadakar dabino kwaya
daya da za ka yi ta don
safta fi kyautar gonar abinci da za ka yi domin
a yabe ka.
9- Zaka ciyar da Dan
kare na kwanaki uku
kawai yayi shekara uku
bai mantaka ba. Amma dan Adam sai kayi
shekara uku kana ciyar
da shi amma cikin
kwanaki uku ya manta da
kai.
10- Alkawari da Zumunta shine kayi wa
goshi kayi wa keya.
Ma'ana ka rike alkawari
a lokacin da kuke tare da
mutum haka ma idan ya
bada baya ka rike mar k**ar yana gabanka
koma fiye da hakan.
Allah Sarki Rayuwa
kenan! Allah yadatar
damu duniya da lahira
yadatar damu da cikawa da Imani. Ameen. KAYI
KOKARI KA GINA
RAYUWARKA AKAN
ABU UKU:
1- Son Allah da
Manzonsa. 2- Gaskiya da Rikon
Amana.
3- Hakuri da Jarrabawa
a Rayuwa....
Barkanmu da warhaka

28/11/2022

RAYUWA tana koya
maka SO...
YAU da GOBE na koya
maka wa KAKE SO....
MATSALOLIN
RAYUWA na koya maka WA KE SON
KA...
Allah ka hadamu da
masoya Na gari!
DUNIYA
MAKARANT!!!

Want your business to be the top-listed Government Service in Yola?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Yola