Binani Ambassadors Online

Binani Ambassadors Online

Share

This is an official Page for "Binani Ambassadors"

13/04/2026

Namu ye namu Binani

02/04/2026

BINANI 2027💥
Sabuwar Tafiya
Sabuwar Gwamnati

02/04/2026

2027 ta Sen. Aishatu Dahiru Ahmed Binani ce

22/07/2025

Idon ka yi da kyau za ka ga da kyau!

22/07/2025

2027 na nan tafe

22/07/2025

A Goodbye Letter to APC

Photos from Binani Ambassadors Online's post 04/02/2025

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alh Atiku Abubakar ya ziyarci Her Excellency Sen. Aishatu Dahiru Binani, a gidanta dake Abuja

18/10/2023
18/10/2023

MAI HALI BAYA FASA HALIN SA, KOWNAI TSUNTSU KUKAN GIDAN SU YAKE

BINANI IKON ALLAH

Abinda muke so wadanda basa Adamawa su fahimta, wannan alheri da take rabawa al'ummar fa, ba ta kan kowani kujera na siyasa ku ba wani mukami a gwamnati ta rike bah.

Tana rabawa yayan talakawa neh su ma su Amfana dashi.
Yeah, Eh itace ta raba taki (Fertilizer) kwanakin baya ga manoman rani, wanda Ni da nake magana am part of the beneficiaries, wannan takin ma da ta raba kada mu manta bata kan kowani mukami.

Kyauta, tausayi, taimako, kulawa da tallafawa al'umma halin ta neh, ko da mukami ko babu.

Bata da na biyu a Adamawa wajen taimako da tausayi masu kananan karfi.

Allah ya cika Miki burin ki Hajiya
Saura kiris da yardar Allah, Kujerar Gwamnan Adamawa naki neh da yardar Allah.

*Binani is coming*

✍️ Ɗan Mama
18th October, 2023.

05/08/2023

KOTU ZAMA NA SHA BIYU (12).

A yau Asabar 5/8/23 kotun sauraron kararrakin za'be ta yi zama na Goma Sha Biyu. Zaman wanda ya guda kamar yadda aka saba an yi ta ne domin baiwa Jamiyar PDP damar gabatar da shaidun ta a yunkurin ta na kare kanta a gaban kotun.

Da farko dai Lawyan Jam'iyar PDP ya shaidawa kotun cewa suna bukatan kotun da tayi amafani da takardun da Hukumar za'be ta gabatar a matsayin takardun su wanda Lawyan Sanata Binani bai goyi baya ba, yana Mai cewa wajibi ne Jam'iyar PDP ta gabatar da nata takardun ba wai ta 'boye a bayan Hukumar za'be ba.

Daga nan sai Lauyan PDP ya sanar da kotun cewa yana da shaidu guda 22 da zai gabatar a cikin kwanaki ukun da kotun ta ba su.

Lauyan PDP ba da sunan Aliyu Idi Hong a matsayin shaidan su na farko.

Amma yayin da Aliyu Idi Hong ya ke yunkurin fitowa gaban kotun sai Lauyan Sanata Binani ya mike ya shaidawa kotun cewa Aliyu Idi Hong *star witness* ne wanda kotun zata baiwa Lauyoyin Binani mintuna 25 domin yi mishi tambayoyi.

Amma a nasu 'bangaren Lawyoyin Fintiri da na Jamiyar PDP sun nuna rashin yardan su da hakan. Sun shaidawa kotun cewa Idi Hong karamin shaida ne (ordinary witness) a dalilin haka tambayoyin da za'a mishi kar ya wuce Mintuna 10. Sun Kara da cewa d'aya daga cikin shaidun Sanata Binani wanda ya kawo report da yakai shafi 171 bai bayyana a matsayin star witness ba.

An yi zazzafan muhawara akan ko Idi Hong zai fuskanci Lauyoyin Sanata Binani na mintuna 25 ko na mintuna 10.

Daga karshe bayan Alkalan sun tafi hutu na wasu mintuna sun dawo kuma sun zartar da cewa:

Mun saurari muhawarar dukkan bangarori akan wannan takaddama. A dalilin haka muna shaidawa dukkan bangarori cewa kotun ita take da wuka da nama. Lauyoyin Jamiyar PDP dake cewa kotun batada hurumin bada matsayanta akan Idi Hong ba dai dai bane.

Akan batun cewa d'aya daga cikin shaidun Mai kara bai bayyana a gaban kotun a matsayin babban shaida ba kuwa muna tunatar da ku cewa kotun ta baiwa dukkan bangarori mintuna ashirin da biyar domin yiwa wancan shaidan tambayoyi. A cikin Lauyoyi guda uku da s**a mishi tambayoyi Lauyan Hukumar za'be ne kawai ya ci lokacin shi amma Lauyoyin PDP da na Fintiri basu ma Kai mintuna goma ba. Wannan ba laifin kotun bane. Abune wanda kuka ga daman yi. Kotu batada hurumin tirsasa Lauya sai yayi amfani da lokutan shi duka.

Kotun na sanar da bangaren Wanda ake Kara cewa Lauyoyin Binani zasu yiwa Idi Hong tambayoyi na tsawon mintuna 25 a matsayin star witness. Wannan shi ne matsayan kotun.

A wannan mataki ne Lauyan PDP ya mike Yana cewa "ina sanar da wannan kotu cewa bayan mun dubi shara'an da idon basira, ni da sauran abokan aiki na Lauyoyi, mun zartar cewa mun janye gabatar da Idi Hong da sauran shaidun mu guda 21 a gaban wannan kotun. Muna godewa kotun da damar da ta bamu".

Alkalan kotun sun amince da rokon Jamiyar PDP na janye shaidu Kuma ta d'age karan zuwa 12/9/23 domin zama na adoption wato zaman kusa da na karshe.

Adamu Ibraheem Jimeta,
Jimeta, Nigeria

04/08/2023

KOTU ZAMA NA SHA DAYA (11).

A yau Jumma'a 4/8/23 Kotun Sauraron Kararrakin za'ben Gomna a Jahar Adamawa tayi zama kamar yadda ta alkawarta. Zaman wanda ake sa ran hukumar za'be zata gabatar da shaidun ta a gaban kotun ya gudana cikin tsanaki.

Yayin da alkalai da Lauyoyin dukkan bangarori s**a sami isa harabar kotun sai Lauyan Hukumar Za'be Barrister Nurain Jimoh ya mike, ya gabatar da kanshi ya ci gaba da cewa "Mai Shara'a muna mika godiyan a Madadin hukumar za'be da irin d'aga kafa da aka mana har zuwa yau. Barrister Jimoh ya cigaba da cewa "ina sanar da wannan kotun akwai takardu da muka kawo a gaban wannan kotun domin a dauke takardun a saka a cikin abubuwan da muke bukatar wannan kotu tayi la'akari da su".

Alkalai sun nemi jin ta bakin Lauyoyi ko akwai mai ja akan wannan amma Lauyoyin Fintiri da na Jamiyar PDP sun goyi baya. Amma a nashi bangaren Lauyan Sanata Binani ya shaidawa kotun rashin amincewar shi da takardun yana mai cewa hujjojin hakan na nan tafe a rubuce kamar yadda tsarin kotun ya tanadar.

A wannan ga'bar ne Lauyan Hukumar za'ben ya sake mikewa yana mai shaidawa kotun cewa "bayan dubi ga wannan Kara da idon basira kuma da tuntu'ba da mukayi muna sanar da kotun cewa mun janye alkawarin da mukayi na gabatar da shaidu a yau, hasalima muna sanar da wannan kotun cewa a yau Jumma'a hokumar za'be ta kawo karshen kare kanta da take yi.

Daga nan Lauyan Fintiri wato DD Dodo SAN ya mike, ya nemi kotun cewa ta basu dama su bud'e nasu kare kan wanda kotun ta amince.

Lauyoyin Fintiri sun fara da sanar da kotu cewa su ba zasu kawo ko wani irin takarda ba suna neman alfarmar kotun da zasu yi amfani da takardun da Lauyan Hukumar za'be ya gabatar a gaban kotun.

A wannan mataki Lauyan Fintiri s**a fara gabatar da shaidu.

Shaida na farko shine Hon. Sahabo Aliyu Gurin wanda ya bayyana a gaban kotun ya shaidawa kotun cewa: Shi dan asalin Fufore ne kuma ya zo ya sanar da kotun cewa anyi za'be a Fufore cikin kwanciyar hankali da tsanaki batare da tashin hankali ba. Hon. Sahabo Aliyu Gurin ya kara da cewa Fintiri shi ya ci za'ben kuma yana kira ga Kotun da su tabbatar da Fintiri a matsayin wanda ya ci za'ben.

Daga nan sai Lauyan Senator Binani ya mike ya yiwa Hon. Sahabo Gurin tambayoyi inda yake ce masa a cikin "statement" naka kace anyi tashin hankali a wurin tattara za'be amma Kuma yau kana shaidawa kotun anyi za'be cikin Lumana, wanne kake son kotun ta yarda dashi? Sai yace e an yi tashin tashina. Yayinda Lawyan ya tambaye shi a matsayin shi na shaida daga Fufore ko akwatuna nawa Fufore ke da shi sai Hon. Sahabo ya ce bai San yawan akwatunan ba amma ya san cewa dukkan anyi za'be cikin lumana. Daga nan Lauyan Binani ya ci gaba da mishi tambayoyi har lokacin da aka d'iba mishi ya cika.

Daga nan Kuma sai Lauyan Fintiri ya mike yayin da Alkalan kotun s**a nemi ya gabatar da shaidan su na biyu. DD Dodo SAN ya shaidawa kotun cewa "ina amafani da wannan dama in sanar da kotun wannan shine shaidan mu daya tilo kuma muna sanar da kotun cewa mun rufe kare kan mu da muka bud'e yau. Batun kwana ukun da aka d'iba mana mun jingine a baiwa Jamiyar PDP dama ta gabatar da nata".

Daga nan sai Lauyan Jam'iyar PDP ya mike ya nemi kotun ta bashi zuwa gobe Asabar domin kawo shaidu.

Kotun ta d'age zaman ta zuwa gobe Asabar 5/8/23 da misalin karfe 10 na sa fe domin baiwa Jamiyar PDP daman gabatar da shaidun ta.

Adamu Ibraheem Jimeta ,
Jimeta, Nigeria.

Want your business to be the top-listed Government Service in Yirol?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Gimba Road State Low Cost Jimeta
Yirol