Hisbah Sabon Gari, Zaria

Call Directions Contact the organization

Hisbah Sabon Gari, Zaria Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hisbah Sabon Gari, Zaria, Government Organization, SABON GARI LG GAMBO SAWABA SECRETARIAT, Sabon Gari.

SAƘON TAYA MURNA DA FATAN ALKHAIRI ✅✌️Hukumar Hisbah ta ƙaramar Hukumar sabon Gari ƙarƙashin jagorancin Commander Malam ...
02/11/2026

SAƘON TAYA MURNA DA FATAN ALKHAIRI ✅✌️

Hukumar Hisbah ta ƙaramar Hukumar sabon Gari ƙarƙashin jagorancin Commander Malam Abubakar Auwal Adam tana taya murna ga Mai girma Shugaban karamar Hukumar sabon Gari kuma Shugaban Chairmomin Jihar Kaduna Ash-Sheikh Jamilu Abubakar Albani na cika shekaru biyu cif akan karagar mulki.

Muna addu'a yanda aka fara lafiya ALLAH ya sa a gama Lafiya.🤲

KARRAMAWA BA TA ZUWA A BANZA! Muna miƙa saƙon taya murna ga Kwamandan Hisbah Sabon Gari, Zaria  , MLM Auwal Abubakar Ada...
13/10/2026

KARRAMAWA BA TA ZUWA A BANZA!

Muna miƙa saƙon taya murna ga Kwamandan Hisbah Sabon Gari, Zaria , MLM Auwal Abubakar Adam bisa wannan karramawa da ya samu.

Wannan karramawa abin farin ciki ne, kuma tana ƙara tunatar da mu muhimmancin jajircewa, sadaukarwa da aiki tukuru wajen hidimar al’umma.

Muna roƙon Allah Ya sanya wannan karramawa ta zama alheri a gare shi, Ya ƙara masa basira, hikima da ikon sauke nauyin da ke kansa. Allah Ya ɗaukaka shi a duniya da lahira, Ya kuma ƙara ɗaukaka Hukumar Hisbah baki ɗaya.

Jagoranci amana ne, hidima sadaukarwa ce, karramawa kuma abin godiya ce ga Allah!
Muna alfahari da kai, Kwamanda!
Allah Ya ƙara ɗaukaka ka, Ya sa wannan ya zama farkon samun manyan nasarori masu albarka. Amin.

13~oct~2026
Faisal Abubakar Albagawiy

06/10/2026

INNĀ LILLĀHI WA INNĀ ILAYHI RĀJI’ŪN!

Cike da matuƙar jimamin , muke sanar da rasuwar Mallam Nafiu Baba-Ahmed, fitaccen mutum, ɗan ƙasa mai daraja, jagoran al’umma, kuma mai kishin hidimar Musulunci da bil’adama.

Kafin rasuwarsa, Mallam Nafiu Baba-Ahmed ya kasance Sakatare-Janar na Supreme Council for Sharia in Nigeria (SCSN), inda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ci gaba da tabbatar da kyawawan ɗabi’un Musulunci, adalci, zaman lafiya da fahimtar juna, tare da kula da walwala da muradun al’ummar Musulmi.

Rasuwarsa babban rashi ne ga iyalansa, al’ummar Musulmi, ƙasa baki ɗaya, da dukkan waɗanda s**a yi hulɗa ko aiki tare da shi.

Muna roƙon Allah SWT Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, Ya kuma bai wa iyalansa, abokan aikinsa da daukacin al’ummar Musulmi haƙuri da ƙarfin zuciyar jure wannan babban rashi.

Za a gudanar da Sallar Jana’izarsa bayan Sallar Azahar, da misalin ƙarfe 1:00 na rana, a Abuja yau, In Shaa Allah.

Allah Ya jikansa da rahama, Ya haskaka kabarinsa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ce makomarsa.

Allah Ya ba iyalansa da al’ummar Musulmi baki ɗaya haƙurin wannan babban rashi.

Āmīn Ya Rabbal Ālamīn.Idan kana so, zan iya kuma ƙara masa taken “CIGIYYA” da salon Shafin Ƙasar Zazzau A Jiya Da Yau, domin ya kasance a shirye kai tsaye don Facebook.

A yau 1st October, 2026 Allah Ya ƙaddara mai girma ASP Ibrahim Aliyu (Mai zube) O/C Police Outpost Kwangila da kammala a...
01/10/2026

A yau 1st October, 2026 Allah Ya ƙaddara mai girma ASP Ibrahim Aliyu (Mai zube) O/C Police Outpost Kwangila da kammala aikin sa na Dan Sanda Bayan kwashe shekaru 35 masu albarka yana aikin.
An gudanar da walima wanda yan uwa da abokan arziki s**a shirya domin ta yashi murnar aje aiki lafiya. A yayin gabatar da walimar, Mai zube ya samu yabo daga dubbanin mahalarta taron inda aka adunga zuba masa albarka, kuma aka dunga bashi kyaututtuka domin nuna yadda ya zauna da mutane cikin girmamawa da iya aiki.

A Gaskiyar magana shine, tunda aka bude Kwangila Police Outpost ba a taba samun O/C kamar sa ba. Sai dai muna sa ran wanda ya gajeshi malam Bashir zai biye masa cikin yardar Allah.

Muna rokon Allah Ya sanya Albarka a wannan aje aiki, Ya karawa rayuwa Albarka Ya kuma kawo babban rabo.

01/10/2026
Mun kai ziyarar gani da ido asibitin Sa'idu dange dake railway a ƙaramar Hukumar sabon Gari domin ganin irin yanda ayyuk...
01/10/2026

Mun kai ziyarar gani da ido asibitin Sa'idu dange dake railway a ƙaramar Hukumar sabon Gari domin ganin irin yanda ayyuka ke gudana na bada magunguna da ayyukan tiyata da sauran cututtuka kyauta Wanda mai girma ɗan majalisar mu na tarayya Hon Sadiq Ango Abdullahi ya ɗauki nauyi kuma kyauta ga al'ummar sa da Allah ya ɗora nauyin su akan sa a majalisar tarayyan Nigeria.

Ayyukan suna gudana cikin tsari da nasara.

Allah ya ƙara masa Jagora ya kuma cigaba da haɗa shi da mashawarta na ƙwarai Amin.

1/10/2026.

22/09/2026

GOOD MORNING ALL🍣🍛

13/09/2026

ALLAH KASA MU WANYE LAFIYA.

Address

SABON GARI LG GAMBO SAWABA SECRETARIAT
Sabon Gari
810103

Telephone

+2348113524351

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hisbah Sabon Gari, Zaria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Organization

Send a message to Hisbah Sabon Gari, Zaria:

Shortcuts

Share

Nearby government services